MALEEK 35_36

545 41 1
                                    


35_36

Not edited

Kallon shi take da wani irin expression a fuskan ta, drivern ta ne ya matso yace hajiya kiyi hakuri mutaimaka mashi musaka shi a mota, daukarshi inzaka iya bazan iya tabashiba gaskiya da najasa a jikinsa,

Da kyar Driver ya daga shi yasaka a mota kamar wata gawa yashige yaja suka wuce gida, suna isa suka daukeshi suka wuce da shi daki suka ajiye shi bedroom

Maleeka tanashiga dakinta ta zuba uban tagumi tana tunanin yazaayi  a nemo meenal don tunda meenal tabar garinnan almost 2months kenan Amman maleek is not himself yakasa hakuri, gashi ita yanzu abin yafara bata mamaki.

Tin daga lokacin maleek bashine ya farfadoba sai wajejen 8nasafe,  bude idonsa yayi yaga dakin yana juya masa, kansa ne yaji ya masa wani mugun nauyi, amai ne yataho masa dakyar ya Mike bai karasa toilet ba dukushewa yayi yafara kwararo amai kamar ze amaiyar da yan cikinshi, sai wani kakari yake kamar Wanda ze mutu, kwaciya kawai yayi a gun bayan yagama don ko danyatsan shi bai iya dagawa nishi yake kadan kadan  kamar ze mutu.

Maleeka datajiyo kakarinsa da saurinta tashigo dakin kwance taganshi duk yayi dama da amai, salati tasaki ta nufe sa da sauri tana jijjigashi Jim ko motsi baya yi yasa takara rudewa ga wani mugun zafi da jikinsa yayi kamar wuta, daga shi tafara kokarin yi Amma inna ta kasa don maleek din ba karami bane, wayar ta takira tashiga neman nomban muhassin, hello muhassin plss kazo yanzu it's urgent, kit takashe wayar bata ma jira jin mai zaice ba.

Muhassin tayagama shirinsa kenan kiran maleeka yashigo, jin muryarta a rude yasa ya zuri makulli yashige mota, gudu yafara kwasawa kamar ze tashi sama, wani uban tsaki yasaki ya daki steering ganin Ana zuwa kanshi traffic ta nuna alamar su tsaya, babu yanda ya iya dole yatsaya traffic na na bada Hannun ya fizgi motar da gudu Amma babu shiri yaci wani uban Burki Wanda har saida yayi Kara, sanadiyyar ganin wani accident da yafaru wata babbar mota ce ta take karamar mota tayi rugugu  dasauri muhassin yafito hankalinshi a tashe ganin a fiddo mace an baje ta a babban titi kamar Matatta duk ta kakkarye ko ina jikinta jini ne, masu daukar hoto saiyi suke duk antaru akanta, muhassin matsawa yayi Don San ganin wacece akwance,

Idonsane yayi arangama da sholy yashe a kantiti duk jini jikinta hankalin muhassin a muguntashi yake kallon ta babu ko kiftawa, tunawa dayayi yanada uzuri yasa ya wuce yashige mota,

Nan da nan saiga motar asibiti tazo ta kwashe sun wuce asibiti.

Muhassin na Isa direct dakin maleek yashiga ganin maleek a yashe akasa yasa yanufe cikin sabon tashin hankali yana salati, shiryashi yayi ba bata lokaci aka saka shi a mota, maleeka ma fitowa Sanye da mayafi tashiga motar mai aikinsuce tabiyota da mus'ab daketa barzar kuka ze bita an ma ko ta kanshi bata bi.

A sukwane muhassin yashigo fargakiyar Asibitin  ko parking din kirki beyiba saiga ma akaitan asibiti rikeda stretcher Dora shi akayi da gudu suka nufi emergency zasu shiga kenan muhassin yahango sholy kwance kan stretcher saye da oxygen a hanci anshige da ita likitoci sunyi kanta.

Wasu likitocin turawa sukayi kan maleek sunkai su biyar kowa da abinda yakeyi Don kokarin ganin numfashinsa yadawo.

Bayan kamar awa biyu saiga likitocin Sunfito sai sharce zufa suke, dagudu su maleeka suka karaso tana likita how is he, calm down Mrs zaku iya shiga kuganshi but yana bukatar Hutu and you yanuna muhassin yace meet me in my office, okey muhassin yace suka fara shiga dakin Don ganin jikinsa.

Maleeka ce ta karaso da sauri tana kallon maleek cikin tausayi kwance yake kamar gawa sanya cikin blue din kaya da wani farin abu a kanshi, hancinshi toshe da oxygen ga da wasu naurori kota Ina dafashi tayi zuciyarsa ce kadai ke bugawa ahankali, kwalla dake zubo mata ta share tace plss my brother katashi wannan gadon baidace da kai ba plss, kuka kawai takeyi jin likitan yace yana bukatar Hutu yasa tafita takoma waje tana kuka,

Direct office din likita muhassin yawuce knocking yayi, daga ciki aka bashi umarnin shigowa, kallonsa Dr sultan yayi yace have a seat, zama muhassin yayi yamika masa Hannu sukayi musabaha, anatse Dr yace garin yaya kuka bari ya shiga wannan condition din, his life is at risk, becouse damuwa tamasa yawa yana fama da depression, zuciyarsa na gab da bugawa.

Hankali tashe muhassin yace doctor me abinyi yanzu plss we don't want to loose him plss doctor,

To for now de munyi iya bakin kokarin mu don ganin mun ceci rayuwarsa, gaskiya Idan kuna son yadawo dede, wait is someone close him missing I mean his mom, dad or wife or any close one?

Muhassin cemasa yayi his mom is alive but sai kuma yayi shiru

DR yace to gaskiya to get him back saikun nemo masa abinda yakeso kuma kunyi avoiding abinda ke bata masa rai, muhassin daga masa kai yayi alamar gamsuwa sannan yamike yamasa Dr sallama yafito.

Jiki a sabule muhassin yakoma gun maleeka, fada mata duk abinda doctor yafada masa yayi, tagumi ta zuba tace ohhh ni inazan nemo meenal yanzu Kai Allah kakawo mana dauki.

Wayarta ta dauka takira mom da Bama ta kasar

Hello mom plss ki dawo wallahi maleek is seriously sick tafada tana shesshekar kuka

Cikin tashin hankali mom tace mayasameshi,

Mom he is in comma, wallahi mom am scared kar maleek ya mutu fa

Ina nan dawowa gobe insha Allah bangama kammala abinda nakeyi bane,

Haba mom  kinsan halin da maleek ya ke kuwa Kike fadin haka

Haushi ne yakamata ta kashe wayar baki daya takoma ta cigaba kuka Don halin ko in kula da mom ke nunawa akan su na bata mata rai.

NIGERIA

Ke  dan ubanki ba magana nake maki ba kike wani kwalo min wa ennan shegun idanun naki kamar na mujiya, shegiya me kama da aljanu, tafada cikin tsiya, dauki wankin nan  ki karasa min shi nace da kina tunanin zan ciyar daku a banzane batareda na more kuba

Jiki a sanyaye meenal taduka tafara wank sauran kayan dake waje ga sanyi yana kada ta hannunta kamar kankara,

Madou ne yashigo yace ke tashi ki koma daki,

ASanyaye tace mama ce tace inmata wanki

Ana wannan sanyi sai kace baiwa, dalla wuce ciki ,

Tawuce din Inci kan ubanta kuwa uban me takeyi a agidan da bazatamin wankiba zata ce min bata iya ba, Dade bamusan asalin balbela ba da nace daga madina take, dalla duka ki karasa wankin nan, kuma kigama ki daura mana tukunya.

Mama wallahi baki kyautawa Ana sanyi meyasa bazaki hada su da adama ba ingaskiyane sai kice tayi ita kadai To, tabarshi nizan karasa wankin.

WAllahi baka isa ba karamin Mara kunya fice kaban gurin kafin in Saba maka.

Wucewa yayi ransa a bace saiga kawo yashigo kallon meenal yayi yace ke me kikeyi nan,

Mama ce tasani wanki, tashi kafin in Saba maki, mikewa tayi sumsum tashige daki tana sharar kwalla, Don gaskiya abin mama yafara isarta gaskiya bazata iya ba Balain Kullum daban Ina dalili, magana zata Karama Abba akan kawai sutashi gidan nan.

Falmatace tafito tana tsiya, wannan de ba yi bane salon yaro ya raina ka yaza ayi nasa yarinya aiki kuhana ta min wallahi bazan dauki wannan ba dole tamin aiki tinda gidana tazo ehe kuma taki yi naci ubanta ba.

Da bulala kawu yabiyo tashige daki dagudu tana karasa maganar ta.

Kuka sosai meenal keyi madou ne yashigo ya zauna gafenta don yanzu kan tasaba da madou sosai shika dai take gayama damuwarta.

Meenal kiyi hakuri kinji ko nasani baa kyau ta miki Amma kiyi hakuri komai ze wuce,ki Dena rike mama a ranki,kuma wannan kukan da kika Maida tabia Bana sonshi,

haka ya dinga bata baki har ta hakura, cewa yayi to yanzu yimin murmushi nagani,

Boye fuskarta yi alamun kunya tana murmushi, to yanzu tashi muje nasiyo maki balangu, yafada yana kashe mata ido.........

Mrs Abdool ce

"MALEEK"Where stories live. Discover now