maleek 43 _ 44

428 43 0
                                    

43 _ 44

Not edited

"Within 50mins su abba suka sauka maiduguri, taxi ya dauka direct yawuce gida, yana shiga da sallama ya tarda meenal zaune tana share kwalla mama sai zazzaga mata tsiya take,

Sosa Kai falmata tafariyi tana yaken dole cikida boron kunya ,meenal ta Mike a sanyaye ta isa gun abba tace sannu da dawowa Abba, tareda karbar jakarsa,

Yawwa meenal kukan me kike yi, yake tayi tace Abba bafa kuka nake ba abu ne yashigan min ido, tana fada tayi saurin shigewa ciki don batason Abba yafara jefo mata tambayayi kala,kala.

Bayan Abba yahuta yaci abinci yashiga Bama su mamy labarin yanda ta kasance a Abuja, wani mugun farinci ne ya bayyana a fuskar mamy tace Alhmdullh ni daman inama Allah kyayyawan zato, Don nasan baze to zarta muba Allah y de yabiya wannan bawan Allah da mafificin alkhairi,

Takardun gida da makulli ya fiddo yanuna musa, to harda gida kasiya ashe Kai alhmdullh muma ashe zamuyi rayuwa mai yanci mamy tafada cikin tsananin farin ciki.

Meenal cikeda murna ta rungume iyayen Nata cikin farinciki tace congratulations Abba finally de Allah yayi zamu bar rayuwar kunci, wallahi abba har kasa naji inason famlyn bawan Allahn nifa yanda kabamu labarin yaransa,yanda suke mutuntaka,

Aikuwa meenal nikai ai na jinjina ladabi da kuma tarbiyar yaran yanda suke ganin suna da kudi ai kunga sai suta yanda suke so Amman kinga akasin haka.

Dadare Abba yaje yama kawo bayani filla filla yanda sukayi da Alhaji, sosai kawu yaji Dadi yakuma ma Abba murna har yakira alhaji ma yamasa godia.

2weeks later

Sungama hada komai nasu Wanda zasu tafi dashi can Abuja, wasu kayan ma duk sunbarma su kawu sbda a can gidan komai akwai, hakan da suke babu wanda ya Sanar ma falmata bata San abinda akecikiba,

Su mamy sungama hada komai nasu cikin jaka jira kawai suke gari yawaye tin asuba suka ma hanya, falmata ce tashigo dakin su mamy babu ko sallama tace "sai kuma Ina Naga Ana hada jaka" mamy da bata kalle taba tace "Inda Allah y nufa"聽 "to zaayi gaba kenan ashiga duniya to Allah y taimaka daman abinda kukayi kenan tin farko da yafi" mamay datayi banza da ita haka falmata tagaji da maganganun banzanta ta kara gaba, kada Kai kawai mamy tayi takyaleta Amman kalamanta sunmata ciwo, ganin daga gobe sunraba hanya yasa tayi banza da ita kawai don su rabu lpia.

Daddare daman abba sunyi sallama da kawu, kawu ya musu fatan alkhairi sosai da yan nasiha da baarasaba, yace masa insha Allah zaizo zuwa gaba.

Tinda wuri around 4am suka tashi sukashissirya sukayi sallar asuba bayan sallar asuba kawo yafito Don rakasu, duk sun fittito da kaya, sassaka kayan akayi cikin golf din da ke Parke kofar gidan kawo, mamy ce takoma cikin gidan ta kalli falmata tace, atsawon zaman mu Idan Nata ba miki laifi kifadamin in nemi yafiyarki don Bana son natafi da hakki, nide ne nayafe miki, haka itama meenal saida ta nemi yafiyar kowa agidan kafin suka fito,

Falmata tayo waje tace quranin Allah baze yiyuba, Abuja uban me zasuyi Abuja, kaikuma tanuna kawo da yatsa tace saboda rashin zuciya mamadin muma kamana hanyar zuwa abujan Amman kama wa ennan matsiyatan to yasin nima bazan yardaba sai nima an tafi Dani, Tokoma ciki da Jakarta ta fito Dan ita dagaske tAke,

kawo ne yakalleta cikin takaici yace sai randa kikayi hankali sannan zamu koma abujar,  au nikake ce ma mahauciya to wallahi bazaje abujar nan ba munafikai kawai shine akaki ko Sanar Dani tafada ta ciro kaya cikin butt din tana wurgi dasu, kowa da ido yabita don wata karamar mahaukaciya ta zama,kawu da falmata tagama kaishi karshi yace ma Abba Allah y kkiyaye hanya, Allah y kaiku lpia karku damu falmata  ku barni da ita bata muku lokaci kawai zatayi.

Drivern daze kaisu ne yaja motar, daga musu hannu kawu da madou suka shiga, adama komawa cikin gida tayi tana share kwalla, shima madou ta maza kawai yayi yashiga ciki Amman idonsa yayi jajur kamar zeyi kuka,

Suna tafiya kawu ya shiga cikin gidan ya karyo rashen dalbajiya dake tsakar gidan yayi kan ta yana zuba mata ita tako ina, ihuu tafara tana nashiga ukkuna Dan girman Allah kayi hakuri wallahi nifa wasa nake musu, zabga mata ita kawu kawai yakeyi ajiki yana tinda rashin hankalin naki yakai har haka gara nayi maganinki banza Mara tunani,

Saida yagaji sannan Dan kansa ya kyaleta,cikin yaranta kuwa babu wanda yazo kawo mata dauki, kawo ya kalle ta yace kicigaba Dan allah karki fasa, daman kule nake dake Mara mutunci kawai.

Tafiya su mamy sukasha ba yar kadan ba sai kusan magriba suka sauka Abuja, daman mai taxin har gida yaikusu,

Bude gida kawu yayi suka shiga da kaya, Banda kallon gidan babu abinda meenal keyi, tarasa wani ma irin farinciki zatayi.

Wanka sukayi don duk agajiye suke, horn din mota sukaji da waje, meenal tasaka hijab tafito, saurayi tahango Sanye cikin kanan kaya ya jingina da mota ya rungume hannuwansa, karaso wa tayi tagaishe shi,

amsa mata yayi yana mata murmushi, "Abba na nan ya tambayeta" daga masa kai kawai tayi tareda karbar basket din hannu shi tayi gaba yana biye da ita baya, har cikin falon, cewa tayi "kazauna bari inyi masa mgna"  "ok toh", zama yayi kamar yanda tace masa babu dadewa sai ga Abba da murmuahinsa yakaraso yana barrister Kaine da darennan, wallahi kuwa Dan durkusawa Ayman yayi yana gaishe da abba yace ga Abbinci inji ummie, to mungode Allah y saka mata alkhairi Ina gaishe ta insha Allah muna nan shigowa tareda iyalan baki daya, to abba nizan wuce, to Bar Ayman Ina doctor ace Ina gaishe to zeji yana asibiti yamusu sallama yafita.

Abinci ne laffiyayye aka kawo musu, zubbuwa sukayi suka ci suka koshi,  suna gamawa kowa yawuce dakinsa,

Meenal nashiga dakinta tafada kan laffiyayyen gadon tareda juyi, jin wayar ta na verbrating yasa tadauka, gani nayi ta daure fuska, tana amsa wayar da kyar,

Daga dayan bangaren yace: meenal kunsauka lpia i was busy shiyasa ban kiraba tindazu,

ATakaice tace Alhmdullh,

Meenal kin tafi kinbarmu da kewa ko,

Yake tayi tace to yaza ayi Ina adama, plss kagaista,

Ok itama tana gaishe ki ma,

Toh Ina gaishe ta good nyt ina jin bacci,

To meenal swtdreams

Mikewa tayi tashige toilet ta dauro alwala tayi nafilfilunta ta kwanta.

Washegari tinda wuri suka tashi nan akashiga kyare kyare, goge Goge da da yan kakkabe kakkabe nan da gida ya dau saiti ko ina sai kyalli yake ga kamshi da ke tashi me dadi,

Abinci sukayi lafiyayyye  bayan Abba yamusu cefene da yan siyesiyen duk abinda zasu bukata.

Dayamma su ukku kowa yafito cikin shiga ta mutunci zasu gidan Alhaji don yimusu godia, taxi suka samu wadda tasaukesu har kofar gidan Alhaji

Kai tsaye suka wuce ciki sukayi knocking a kofa, babu dadewa wata kyakkawar budurwa ta bude musu kofa wacce bazata wuce sa ar meenal ba, da faara a fuskarta tace sannuku dazuwa kushigo, shiga sukayi itakuma tawuce sama don kiran ummie babu dadewa sai ga ummy itama fuskarta dauke da faara tace maraba sannuku dazuwa ya hanya, gaisuwa suka shiga kamar daman sun san juna, abinci kala kala akawo musu suka Dan ci kadan suna cewa sunkoshi,

suna zaune sunafira sai ga murad yashigo cikin shigarsa ta doctors shima gaisawa suka shiga yi da su abba kafin ya wuce dakinsa, tuni daman meenal sukayi daka da yasmeen suka cigaba da fira Ayman na gefensu yana taya su don daman gun barkwanci da surutu ba daga bayaba

Bayan kamar awa guda suka Mike daniyar tafiya Don dare yafara yi yasmeen tare suka sauko da meenal ayman na biyadasu ummie ce tace oh ni Aishatu daman Kai kana cikinsu kuna fira, kallon yayi da murmushi yace to ummie kannenane fa miye aciki yafada yana Dan turo baki, toh Allah y kyauta cewar ummie,

To New frnd dinmu muna nan zuwa gidan ku numa cewar Ayman, ya ayman dinnan kacika ban dariya, toh sai kura ni kafin kuzo tinda kin karbi digit Dina meenal tafada tana kollonsu da murmuahu,ok bye sukayi sallama kamar karsu Rabu.

Bayan sun wuce yasmeen ta kalli ummy tace wallahi ummie I love her she's nice kinga yanda muke fira kuwa kamar min Saba, ummie tace haka ma mom dinta munyi fira sosai har munyi exchanging digit.........



Mrs abvdool ce

"MALEEK"Where stories live. Discover now