MALEEK 37_38

466 37 1
                                    

     37_38

"Shigowa tayi gidan tareda sallama bayan madou ya mata siye siye, saurin shigewa daki tayi Jin mama na shirin fitowa.

Zama tayi a daki ita kadai ta tasa kayan tanata kallo, duk sanda madou yamata siyayya muhassin kawai take tunawa Amma yanzun kam tadena kuka, sbda madou yace mata what ever ix disturbing her cryng is not d solution she just need to wise up kuma ta dauki hakan.

Mama dake suk'e da ita da yamma ta banko kofar dakin tana, ke tashi kije kisaka mana tukunyar tuwo,

Meenal dake kwance ta tajuya mata baya ko matsawa batayiba,

wai bada ke nake magana ba kokuwa fitsarar taki takai Ina miki magana kimin banza

Ayanda take Bama tada alamar magana, bare motsawa.

Cikin zafin nama mama ta kaimata duka mai azababben zafi a kwankwaso

Meenal da dukan yashigeta tana son kuka Amma tayi ta maza, mikewa tayi idonta jajur kamar wata zakanya tayo kan mama, mama da ta tsorata da yanayin meenal don dai karta gudu ayi abinkunya yasa tadake

WAllahi karki kuskura kisake daga filthy hands dinki akaina inba hakaba zakisha mamakin abinda zefaru azzaluma kawai mara imani,

Baki bude mama tayi tasaki wata uwar guda tana ehh lalle daman nasan arina to dama yarinya tashin kasar waje ba tarbiya ai dole, wato ke har nizaki kalla kifadama wadannan maganganun to wallahi kinfada ma Fatima bani ba shegiya tsintattiyar mage.

Anfada miki kedin wacece bafa uwata bace ke, ko kin zata tsoronki nake, to shiru shiru ba tsara bane Gudun magana ne, sannan yanzu nasaka takalmin karpe shirye nake da intake  kowani shege ehe don haka Ina miki gargadi da fita hanya ta.

Bata rufe baki ba taji saukar Mari a kucin, mamy dake daki tana jinsu tafito a fusace, ke falmata karki kuskura ki Kara tabamin ya azzalumar banza kawai, uban me ta miki zaki mareta eye, to abincine bazata dafa ai ba yar aiki bace, nayi kawaici nayi kawaici Amma Naga alamun ke bakisanshi to zamu saka kafar wando daya dake agidannan, kuma abinci kidena bamu kiga zamu mutu, kiyi hakuri insha Allahu wata daya bamu karashi a gidan nan, na kuma barki da Allah duk abinda kika mana wallahi duniya zata gyamaki banza wacce bata gaji aziki ba mama ta karashe cikin Karaji

Kekuma sokuwa wallahi daga yau bance kira raga ma kowa ba tinda abin ba Kara duk wanda ya taka ki,ki takashi tunda da ba ta iya rike girman ta ba mamy tayi kwafa cikin fushi.

Wata muguwar dariya falmata tasaka irinta yan duniya tana wargi dede nake da kugun kowa yasin, kuma muzuba mugani shege kafasa saikinyi Dana sanin zuwa gidan nan  tayi shigewar ta daki tana juya muzauna.

Suna shigewa daki meenal ta fashe da kuka tana mamy wallahi ni nagaji gaskiya kawai ki ma Abba magana nide mubar gidan nan ko Wanda bekai wannan bane nide gara shi da nan, hakuri mamy taba yarta kafin itama tawuce daki.

Maleek da kwanan sa ukku kenan a asibitin yana kwance baya magana se Ido kawai yana kuma motsa yatsunsa, abinci ma baya ci saita robar abinci.

Mom data dawo jiya tana zaune Gefen  maleek ta zuba masa ido,tinda tadawo maleek yaki yarda yabude ido taganshi Dayaji tashigo ze runtse idanun yana jin wani zafi aranshi harsai tabar gurun tukun.

Condition din maleek yafara damunta, office din Dr sultan tashiga suka gaisa tace yajikin nasa Dr, to madam wallahi jikinsa ix not responding at all babu wani cigaba, Dr kodai yarona yamutune bakusan gayamin, to hajiya Idan ya mutu zamu ajiye gawarsa mu ta kallo ne, da ransa Amman gaskiya yana jin jiki, it's seem akwai abinda ke damunsa akwAi abinda yake gani hankalinsa na tashi idai kuma kunason yawarke dasuri to gaskiya sai anyi nisa da abin, to nagode likita sai anjima ok bye.

Maleeka da mom na fita tashiga tana kallonsa cikin tausayi taga mood dinsa tasan tabbas baya son ganin mom kokadan Amma to yazatayi gashi likita yace sai ankauda abinda ke daga masa hankali kafin asamu heart dinsa tayi healing.

Bayan kamar sati dafaruwar abin Kawu na zaune a daki yana lazimi, Falmata tashigo dakin durkusawa tayi har kasa tace malam dama hakuri nazo baka akan abinda nakema su Fatima, insha Allah u bazan sakeba

Dawani mugun kallo yabita yace ke tashi kifita ban yarda da wannan munafincin ba, marairaicewa tayi, tace wallahi da gaske nake na tuba fa, to Allah y yafe mana baki daya, kokefa daman abinda nake ta nuna maki kenan kika Gaza ganewa.

To kafito kaci abinci, to inazuwa bari inkarasa

Fitowa yayi ya tarar da kowa ya hallara Amma Banda mammy da meenal, kallon falmata yayi yace Ina Fatima da meenal

Mallam nayi nayi su fito sunce bazasuci ba, ban gane bazasuci ba haka tace miki cewar Abba,

Eh wallahi Dana sake zuwa ma korata tayi ta zazzageni nifa bansan meke damunsu ba kwannan duk sun canza ko abinci nasu suke dafawa tafada tana tabe baki,

Madou ke mata  kallon mama kiji tsoron Allah don shiyasan duk abinda ke faruwa, asace ta wurga masa wani mugun kallon, sauke kansa yayi kasa yacigaba cin abincin shi

Mikewa abba yayi adan fusace yashiga daki, kan abin sallah ya tarar da ita, yace Fatima meyasa baki fito cin abinci ba, atakaice tace nakoshi, kinkoshi da kikaci me, kawai bana jin yunwa kuci kawai, Fatima kinga Bana son irin wannan halin ko,yanzu inbanda neman fitina meye nazagin falmata sbda tace kizo kici abinci to gidanta kikazo dole kibita sannan kuma ban yarda dawani abinci da kuke dafawa ba nasu zakuci,  in munkoma namu gidan sai kuci Wanda kukeso. Yakarashe maganar cikin fushi.

Mammy da abin ya bata mata rai yasa tamike tashige bayi tareda rufe kofar tana share kwalla.

Abba na mikewa madou yace baba bari naje nakira meenal din, to maza kirata falmata dake binsa da harara yayi kamar begantaba, tareda sallama yashiga dakin,

MEENAL dake kwance ta juyama kofa baya bata amsa ba kuma ba bacci take ba Sam kwannan tarasa Mike damunta kowa agidan haushi yake bata yanzu har madou, batada kuzari kwatata, wata muguwar kewar maleek ke damun ta, kuma gaban ta na yawan faduwa,

Meenal meyasa baki fito cin abinci, nifa kwana biyu kin canzamin Sam bansan meyasa ba ko wani abu namaki ne,

Shiru tamasa kamar bata San Abinda yake cewa ba, meenal nafasan ba bacci kikebe kitashi kawai muje plss, yadade yana mata magana ko juyowa batayiba.

Daga karshe jin ya dameta yasa tajuyo a fusace tace I said am not eating ix it by force plss I don't want to see u plss leave ta nuna masa kofa da hannu

Plss meenal....

Bai karasaba ta daka masa tsawa tace i want to be alone plss kafita,

Allah ya baki hakuri  Amma bansan meyasaba two days ki koma me zafi ba yafice jiki a sanyaye.

Kuma fa da gaskiyar sa kwana biyu ita Kanta batasan meke bata mata raiba kawai ttaita masifa duk wanda ya taba ta...........



Mrs Abdool ce.

"MALEEK"Where stories live. Discover now