maleek 33-35

516 41 0
                                    

❤️❤️   _*MALEEK*_❤️❤️


✍️ _*MRS ABDOOL*_

*33-34*

Mikewa tayi tashiga daki ta cinye abinta, tana gamawa tamike tashiga dakin su abba tare da zama, saida tagaishe su sannan ta Mika masa check dinda muhassin ya bata,

"tooo wannan uban kudi haka to Allah y saka da alkhairi wannan yaro daman yaron kirkine" abba yafada yanata murna,

Abba yakamata kasamu abinda zakayi ko bussiness ko aiki kaga nima da zaka samomin aiki a asibiti haka kaga karatun likita nayi abba sai yafi wannan zaman banzan." Meenal tace

"Hakane meenal Amma wannan shawarar ai da abbanki zamuyita shikuma suyi da kawu" Amma bayanzu ba cewar mammy

To mamy "Allah y tabbatar da alkhairi" tamike tana kokarin tashi abba  yace "meenal kiyi hakuri kinji duk abinda zaki gani ki Kai zuciyarki nesa nasan de daman kinada hakuri insha Allah Soon zamu bar nan."

"To shikenan Abba insha Allah" zanyi kokari ta musu sallama tafita.

Washegari tana zaune Akan kujerar tsugunno suna fira da adama jifa jifa, Adama dake daka tana bata labarin saurayinta,

"ke adama haka kikesonshi," tafada da yaren larabci tana gaurayawa da Hausa,

Adama tafashe da dariya don ta fahinci abinda takecewa tace

"tabb wallahi inasonshi sosai malamin islamiyar mune kibari ai yanzu baba yace muringa zuwa tare zaki sanshi" tafada tana wani juya ido,

"dariya meenal ta kwashe dashi tana cewa lalle na love Tintin, Allah y barku tare musha biki,"

"kinji wannan meenal din sai anyi magana kice ke bakida saurayi duk wannan kyan naki nifa ban yardaba to ki ma shirya wallahi yanzu zaafara rushing dinki",

"tabb wallahi nikaf zan rinka sakawa ma,"

" wai kekam bazakiyi aure bane," tace cikeda mamaki

"eh bazanyiba" meenal fada Adan fadace tareda juya mata baya.

"Tabe baki adama tayi tamike tashige cikin daki tace oho kar Allah yasa kiyi nide namakusa aure"tafada cikin gatse.

Madou ne yashigo tareda sallama, murmushinsane yafadada ganin meenal zaune tsakar gida, yace "balarabiya ke
ce ke daka salan hannunki yayi kanta ko,"

murmushi tayi tace "yaya wani irin kanta kuma", karbe tabaryar yayi yacigaba da dakan yana bata labari tana kalkyatar dariya, wai kinsan wani abu balarabiya abokina yafara koyamin labarabci dana cemasa inada kanwa balarabiya yakoyamin inrinka yimiki maki,

"dagaske to me kakoyo" budar bakinsa yace "Ana uhubbuki" I love u_ wara ido tayi tace "a Ina koyo wannan kuma kasan me kafada kuwa?"

gyda mata Kai yayi yace "nasani mana", "to menene barka da zuwa mana" kwashewa tayi da dariya harda dukawa, meyafaru kuma kike dariya Kara kwashewa tayi da dariya haka tadinga dariya kamar wata tabbabiya,

daure wa yayi yace "me kikema dariya kuma?"

tsaida dariyar tayi tana kallonshi tace "haka abokin naka yafada maka," eh mana, "to wallahi ba haka bane" takara tuntsirewa tayi da dariya,

"to nace kifada min sai wani dariya kike,"

"nikam bazan iya fada maka ba kadeje ka tambayeshi shida yafada maka,"

"to baruwana dake tinda bazaki fada minba,"

tsaida dariya tayi tace to zan gayama maka cewa kayi I love u tana fada ta kwasa da gudu tashige daki, dariya yafarayi shima yacigaba da daka.

Falmata tafito daga daki fuskarta murtuke tace "Kai da ubanyawe kuke kyalkyatar dariya,to wallahi kakiyayeni kakuma fita a idona don wannan shisshigewar dakakema yarinyar nan Bana so don kar gaba inji wani zance ya Taso ehe" tafada cikeda balai.

"Dallah bani tabaryar nan ka fice min"

Mika mata tabaryar yayi kawai yafice ba tareda yace komai ba

Egypt

Maleek yafi sati babu Inda yaje yana kwance a daki tunani yayi masa yawa, mikewa yayi ya dauki makullin motarsa tafita bai tsaya ko ina ba sai parking yayi dede Ana kiran sallar margib awani liquor palace kanshi tsaye ya shige, mutanene yagani birjik maza da mata wasu duk sun bugu wasu kuma suna zaune a table da kwalabe a agabansu, wani matashi ne yamike yana "maleek have a seat wace zaa kawo maka ne" lokaci guda maleek yaji mema yakawo shi nan ne mikewa yayi ze wuce matashin dazu mai suna Kabbab yace aa maleek inazaka kuma zauna mana yafada tareda jawo shi kan seat din

"U look worried maleek what's wrong," cewar Kabbab

Girgiza kai maleek yayi yana kokarin mikewa,

"Look meleek kome ke damunka just take a glass kome ze wuce koma meke damunka, kuma zakajika fresh babu sauran damuwa"

Kallonsa maleek yayi yace "I don't take wine,"

"Ah ah ai akwai non alcohol, ya zaka zo kawuce baa maka offering komai ba,"

"mikewa yayi ya bude fridge ya dauko wine ya juye ta cup ya Mike ma maleek tareda cewa it's non alcoholic" ajiye masa cup din yayi yace Allah y baka hakuri ya kuma yaye maka abinda ke dakunka,  yawuce.

Maleek sai kallon cup din yake, mika hannu yayi ya daga cup din ya kwankwade Karawa yayi haka yadinga har saida ya shanye kwalbar tass , gani yayi idonshi yafara juyawa ya Mike yaji kamar ze fadi,

Kabbab ne yazo yana masa killer smile yana baabaa yade, maleek yace Nomal wallahi cikin muryar mashaya har bayan isha yana nan joint din, wayarshi yagani tana ta ringing Amman yakasa dauka yamike da niyar tafiya gida yafadi, sake mikewa yayi Yana dafa desk din gurin, Kabbab yace let me drive u home tareda karbar makullin motarsa, daga maleek din yayi yakaishi mota sundanyi nisa Kabbab yafaka ya hankada maleek Gefen wani gutter, ya ciro wayar maleek  daketa ringing yayi dailing nomban maleeka da keta kiranshi tin dazun, cemata yayi tazo tadauki maleek ya fada mata address din gun, waishima nan yaganshi a titi shiyasa ya kira.

Yana gama fada ya wurga masa wayarsa bayan ya dauke wallet din maleek dake Dankare da kudi tareda firzar motar aguje suna kashewa da frnd dinshi "yace shege kadan ma yagani wallahi nayi alkawarin saina tar watsa masa rayuwa ko bajima ko ba Dade."

Maleeka ce tareda driver suka dinga bin address din harsaida suka iso gun dagudu tafito ganin maleek yashe a titi Gefen gutter, rungumeshi tayi tace me yasameka ne kayi magana mana, jin yana warin giya yasa tayi saurin jada baya tana masa wani matsiyacin kallo lokaci guda tadaga hannu ta kifa masa lafiyayyen Mari..........

*OUMM HANEEF*

"MALEEK"Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora