maleek 63 _ 64

512 58 0
                                    


  63 _ 64

Not edited

"Saukar da kanta tayi kasa cikin tsanan kunyar abinda maleek yamata kokarin Maida kwallan da yake neman zubo mata take, gaba tayi ta bude motar su tashige cikeda kunyar abinda maleek yamata.

Duk wa enda ke gurin basuji dadin abinda maleek yayi ma meenal ba Sam bade kamar mom, su Meena binta sukayi suka shiga motar suma, mom karasawa tayi tabude motar da yake ciki tazauna Itada maleeka, muhassin kuma seat din gaba na gefen driver ya shiga.

Motacin excort ne sukafayin gaba motar su maleek na tsakiya sai sauran escort na rufa musu baya.

Adede tankamemen gidan suka faka, dasauri maigadi ya Dannan remote nan da nan gate ta zuge suka Dannan Kai ciki, kasancewar harbar gidan data wadatu yasa duk yawan motocin suka dauke.

Dasauri daya daga cikin escort ya zagayo yabude murfin motar maleeka ce tafara fitowa da nan sai mom sai daga karshe gogan naku ya fito yana wata tafiya mai cike da takama,

Adede bakin kofar kowa ya tsaya maleek ne ya matsa gaba ya Dannan pin din kofar nan da nan kofar ta zuge duk suka shige ciki, bin falon suke da kallo sbda ya tsaru iya tsaruwa da kayan alatu na kyalelen duniya,

Maids ne suka fara dawainiyar da manyan warmers da wanda su mamy suka kawo, abinci aka dafa yafi kala 10, mikewa sukayi suka nufi draining mai cin mutun 12, meenal wucewa tayi daki Don bazata jure kallan da maleek ke aika mata ba, bayan kowa ya hallara mom ta waiga takalla meena tana banga meenal ba, go and call plss.

Mikewa meena tayi tanufi dakin, ganin meenal tayi zaune ta kifa uban tagumi idon ta jajur da gani kuka taci, kallonta meena tayi tace haba meenal miye maanar hakan ne plss ki kwamtar da hankalin ki yanzu tashi muje kici abinci everyone ix dere ke kadai ce bakinan, pretend as if noting happen tashi ki wanke fuskarki muje, da kyar ta lallabata tamike suka Isa dinning din sarving kadan tayi taja kujera ta zauna.

Shiru kakeji sai kas kas karar cokali, meenal wasa kawai takeyi da spoon din Amman takasa cin abincin, duk jitayi ta takura kamar Ana kallonta, dogo kanta da tayi yayi dede da na maleek kamashi tayi yana kallonta, yayi saurin Janye nasa idon, mika hannu tayi zata dau cup shima yasa nashi akan nata wani shock taji  tayi saurin sakarmasa ashe shima yasake, tass kakejicup din ya tarwatse a kasa.

Hakan shiya jawo hankulan mutanen gun, mom ce tafara magana subhanallah ya haka meenal hope bakiji ciwo ba, girgiza Kai tayi kawai mikewa maleek yayi zewuce ciki, mom takallesa tace Kai were to Beko kalleta taba yace am done tareda fita, kowa nagama kamalla cin abincin ya Mike nan maids suka shiga tattare gun.

Bayan kowa yayi sallah an huta, mom ta kalle kowa tace lets have a word zamu Dan tattauna, guri duk yayi tsit mom tafara magana kamar haka,

"Dan allah yayana ku yafe min nasan na aikata babban laifi agareku Amman Dan allah ku yafe min wallahi natuba sharrin zuciya ne, nayi muku alkawarin Gina muku sabuwar rayuwa mai cikeda Kula da tarairaya duk abinda kuka rasa ada nayi alkawarin yimukushi tafada jikinta a sanyaye,

Amman nasan Idan kukaji abinda na muku wallahi bazaku taba yafe min, Abdulmaleek nacutar dakai kayafe min Dan allah, sauke ajiyar zuciya tayi tana Nina kashe mahaifinku sanadiyar ziga dakuma son zuciya irin rawa Amman wallahi nayi nadama kuyarda Dani tafada kwallan takaicin abinda ta aikata ya zubo Mata,

Zubara maleeka tayi jikinta har rawa yake tareda bakinta cikin takaici tace mom ban taba sanin muguwar zuciyar ci takai hakaba I never knew u have reach up to that extent inalillahi wa inna ilaihi rajiun sbda duniya u choose kimaida mu ophans ke kuma widow sbda abin duniya anya mom kinada inamani kuwa, bana tunanin ke kika haife mu toshe bakinta tayi sbda kuka da ya kwace mata ajiye dan ta tayi tawuce daki dasauri ta kulle kanta tasaka key,

"MALEEK"Where stories live. Discover now