maleek 25

677 53 1
                                    


  25

"Tura maleek akayi cikin mota kamar wata tinkiya,mom tace ma guard dinda tace ya dauko motar maleek,

"Cire mata kayan cikin motar don nasan shitakewa mawa" tana gama fada tabi meenal da kallon irin zakiyi ragratting dinnan

Shi maleek kwata kwata hankalinsa bashida abinda mom ke shirinyi kawade hankalinsa ya raja'a gun meenal tausayinta yake sosai yana ganin yajamata wulakanci.

Wayarsa yaciro da sauri yayi typing text "plss muhassin kazo ka dauki meenal yanzu tareda tura masa address din gurun.

Kansa kawai yakifa acikin motar yana tunani kala kala.

Meenal datayi tsaye a gunda suka Barta kamar wata statue, alamar mota  taji ta faka bayan ta muhassine yafito yaja hannunta kawai suka shiga mota, Anan tabar ledojin da maleek yabata.

Bata cemasa uffan ba,sai kuka kawai takeyi a cikin mota shima baicemata komai yana isa kofar gidansu ta bude motar tafita batare da ta Kara kallon motarba.

Meena suna isa tawuce daki tana kuka sosai, tanacewa dama maleek meenal yakeso, sai a lokacin scene din baya suka rinka dawomata, sai a lokaci tace Amma ni sokuwar inace Dana Gaza gane hakan to in hakane kuwa tinkafin nazo suke son juna, Sai a lokacin Dana sanin abinda tama meenal yadinga damunta.

To yanzu meye mafita, Kai komade menene saina auri maleek he is my type not hers, Meena ke zaune tana mgna ita kadai kamar tabbata.

Kashau najiyo saukar Mari adakin mom dagudu nakarasa don dauko muku rahoto.

Mom kita marina inde akan meenal ne bazanji komai ba, karkuma kiga laifinta laifinane, nine nakesonta maleek yafada cikin dauriyadon Marin yashige shi sosai,

Wani bakin ciki furuncishi ke Kara saka mata, daga hannu tayi takara kaimasa wani Marin, tana huci kamar zakanya,

Dan ubanka nike fadawa wannan maganar, What d hell are u saying are u insane kodai kafara shaye shayene bansaniba, Abinda kazama kenan bansaniba, to wallahi aure next week ba fashi Idan an aura maka ita ku kashe kanku shasha kawai.

Mom naji zan auri meena Amma kisani bazata taba samun soyyaya taba, Bakuma zata taba samun farinciki da kwanciyar hankali ba irin Wanda kowace mace take samu, kuma bada dadedewaba zan aura wacce nakeso inafata bayan nacika burinki bazaki bijiro dawani zancan ba,zan miki biyyaya ne kawai sbda Inaso in gama lpia badan komai.

Yana kaiwa Nan yamike yana kwallan bakinciki yawuce part dinsa.

Aharzuke mom ta daga land line takira oga safwan, babu jimawa yashiga tareda dukawa cikin ladabi,

Dagowa tayi in a commanding tone tace oga Sani Inaso kusa kwakkaran tsaro akan maleek karyafita ko ina harsai an daura auren Nan nasu kana jina ko, karkuma kabar even dat he so called frnds suzo Inda yake, saura kuma kubarshi yagudu kamar last time,

Okkey ma, we will do as u say ya amsa mata cikin ladabi.

Meenal tinda tashiga daki take rikgaz kuka kamar Allah y aikota, mamy ce tashiga tace meenal mekefaruwane haka nagaji daganinki cikin wannan halin fadamin inji

kamar jira take nan tafara karanta ma mamy duk abinda yafaru,

Rungumeta mamy tayi cike da tausayi tace kiyi hakuri meenal kinji insha Allah komai yazo karshe, inason from today henceforth kimin alkawarin zaki cire maleek da duk abinda yashafe shi daga ranki kiji koh Allah zai baki Wanda yafishi Amma wannan azabar tayi yawa, zan kuma ga abinda zan iyayi haka mamy tadinga kwantar mata da hankali har tasamu natsuwa.

Tinda tafada ma mamy abinda yafaru taji sauki sosai kuma insha zatabi shawarar mahaifiyarta

Maleek yashiga kunci sosai fiyeda da gashi mom tahasa fita kuma tahana kowa yazo Inda yake kuma wayoyinsa duk ta karbe, dafe kansa yayi wande kemasa mugun ciwo yana, ya Allah what have I done to deserve all dis Astagfurullahi Allah Idan wani laifi nayi ka hukunta tani ta wannan hanyar kayafe min kakuma sauka kamin yafada ahankali kwalla na sauka daga idon sa.

"MALEEK"Where stories live. Discover now