21 A tsawace tace Kai nake sauraro, to wallahi kashiga hankalin aure maleek 21

632 45 1
                                    


21

A tsawace tace Kai nake sauraro, to wallahi kashiga hankalin aure ba fa shi nama gayama

Mom I told I haven't settled yet meyasa kikeson yimin dole, yafada muryarsa na rawa kamar zeyi kuka...

Wannan kalma ta settled tana masifar bata mata rai jitake kamar tamasa dukan tsiya"Kai Dan ubanka tell me uwarme zakayi settling wani issue gareka da harzakayi settling nace", tafada tana huci "wallahi inka kara furtamin kalman settled dinnan sai ka yabawa aya zakinta", zaka gyamin before if u are unsettled tayi kwafa.

Shiru yayi baice komai ba kanshi a kasa so many things are running in his mind.

In a serious tone tace Abdulmaleek "wallahi karkasake ka kunyatani a idon mutane, narigada na yanke hukunci and that is final, Nina haifeka ba Kai ka haifeniba, Don haka inada damar da zan yanke duk hukuncin Dana ga dama akanka I hope am clear".

Dagowa yayi idonsa sunkada sunyi jaa, tsantsar bacin rai ne kwance a fuskarsa da kyar ya iya bude baki yafara magana, daman ya Dade yana jiran wannan ranar

Ina a husky voice yace "mom yaune kikasan kin isa dani kokuwa yaune kikason kace kika haifeni, kinada hakki akaina har kike son In yi Abinda kikeso, tinda Nike kintaba min abinda nikeso, kokuwa kintaba bani kulawa irin wadda mahaifiya take ba danta, ko kintaba zaunar Dani kikaji abinda ke damuna kokuwa abinda nakeso da banaso, mom baki San yanda nayi rayuwa ba, bansan dadin uwaba, harta kaiga Wanda baida uwa yafini gata,Banda Wanda ze lallasheni, yaji matsala ta nayi rayuwa cikin kunci, damuwa da rashin Kula, Amma Alhamdullh hakan baisa nashiga wani hali ba,

Sai yanzu rana tsaka zaki bijiro da bukatarki kuma kice dole sai nayi, to meenal nakeso kuma ita zan aura, bazan yi rayuwa cikin bakin ciki ba kuma inkare a bakin ciki ba bazai yiyuba, Inaso nasamu farinciki, Kula dakuma gata Dana narasa a da kuma na tabbata meenal ce kadai zata iya bani hakan,

Rashin samun hakan ba karamar matsala zai haifarmin ba kokuma hakan yana nufi da bazana da rayuwata.

Yana kaiwa nan yayi ficewarsa ransa na kuna, direct daki yawuce yasaka key ya kulle kansa don yana bukatar ya kadaita, dafe kansa yayi abubuwa da sun dawo mai sabbi gadagal, Idan ya tuna bayada mahaifi kuma mahaifiyarsa bata damu dashi ba tasa duniyarta gaba akan komai, ita tafison cikar burinta da kawai bata damu da farincikinsa ba to ni haka rayuwata zata Kare babu jin dadi wani lokacin ma kudi basu da anfani don shide basu mai ba, yasan kila da talaka ne shi da sai yafi jindadin rayuwa, babu anfani kudi ba kwanciyar hankali.

Wansu kwalla ne masu zafi suka gangaro masa jiyake duniyar tamasa zafi.

Baki sake ya fita yabar mom jikinta yayi sanyi da maganganun maleek ashe bai manta ba, hmmm ammafa hakan baisa mom tayi kasa da gwiwa ba. Tana nan akan bakarta

Zazzabine mai zafin gaske ya lullube shi rufewa yayi da bargo yana shivering shi kadai, kwanan shi daya a dakin Amma mom batako leko ba balle tasan halin da yake ciki.

Meenal kam tafara ba kanta hakuri tacigaba da rayuwa warta saidai ba yanda tasaba ba yanzu magana ma bata dame ta ba sosai, kuma ta Maida hankali kan karatunta sosai ganin shi kadai ne zai taimaketa ta gashi sunkusa fara finals exams.

Maleek ganin abin gaba yake yasa ya kira muhassin a waya, jin haka, muhassin ba karamin tashin hankali yashiga ba, jinyarsa yayi sosai har ya warke, magunguna yake nema masa na musulumci ganin asibiti ta gagara, satinsa daya bai lpia sosai, Amma da taimakom magani dakuma ikon Allah yasa ya warke.

Kwanan sa biyu kenan kwance baya hayyacinsa kwata kwata, farkawa yayi a firgice yana furta sunan meenal, bayan muhassin ya karba masa magani a gun wani malami Wanda ya shaida masa sihiri aka ma maleek Amma da yarda Allah ze dawo dede.

Dafesa muhassin yayi yace calm down frnd, Ina meenal din take, plss muhassin bari inje gun meenal I need to see her, kayi hakuri ka warke tukun saikaje u are not strong, da kyar muhassin ya lallaba shi ya hakura ahaka suka cigaba da yin Maganin har ya warare.

Meena ce dauke da tray din break fast a hannunta tashiga dakin sa, good morning my king, wani mugun kallo ya watsa mata Wanda yasa ta Shan jinin jikin ta, mikewa yayi yashiga bedroom tareda buga uban tsaki,

Mikewa tayi jikinta a sanyaye ta fita da tray din.

Wanka yasha ya shirya Sanye cikin gezner fara sai kyalli take, ga uban kamshi yana zubawa kamar sabon angon, kallon kanshi yake cikin mirror yana taje sumar kansa da comb, agogonsa ya dauko na sinari da zobba ya zuba, black shades dinsa ya dauko masu Karama kyayyawar fuskarsa kyau yasaka, yayi kyau matuka sak balarabe Dan misra, saidai ramar dayayi tadan fito saidai duk da haka bata hana kyawunsa fitowaba wayayinsa ya kwasa da key din mota ya fita.

Parking lot ya nufa yana dannan keyn motar nan motar tayi unlocking, dribernsa ne yataso da sauri yana kokarin karbar keyn,hannu ya daga masa, yakoma ya zauna.

Wata shegiyar brabus kirar Benz mai mahaukacin kyau yashiga, bakace wuluk sai kalli take dindin take da tint, kana ganinta kasan mahaukaciyar tsada gareta.

Parking yayi a kofar gidansu meenal ya aika yaro yakira masa ita, tana zaune tana karatu yaro ya shigo kiranta, kace Ina zuwa, mamaki take waye zezo nemanta,inde muhassine ai shigowa zeyi ko ya kirata hijab dinta ta Saba tayo waje.

Dan kareriyar motar data hango Parke a kofar gidan su yasa ta tafara tunanin waye kuma wanann, koma waye gaskiya saidai yayi hakuri Don she's not ready.

Tinfitowarta gida ya kafeta da ido tacikin glass kasacewar tint ce she kadai ke ganinta ita bata ganin shi, wani shauki yakeji nadaban wata sabuwar soyyarta na fizgar shi.

Shagala tayi da kallon motar Don tayi mugun tafiya da imaninta, ganin anki fitowa yasa ta matsa ta kwankwasa glass din, zuge glass din akayi wani sanyi taji me hade da kanshi ya bugi hancinta, saurin dagowa tayi, four eyes sukayi da maleek tayi kamar ba shi ba, saurin Janye nata tayi gaban ta na faduwa a lokaci guda kwalla na taruwa a idonta............

Vote and comment

Mrs abvdool ce......

"MALEEK"Where stories live. Discover now