maleek 61 _ 62

490 36 0
                                    

   
   61 _ 62

Not edited

Rasa ma abinyi sukayi duk Sun daburce gabadaya meena ce tamike tashiga office din murad tana doctor help plss don Allah kataimaka plss, ganin a rikice take yasa yabiyota ganin meenal yasa hankalinsa ya kara tashi cak yadaga ta ko takan su abba be biba yashiga emergency da ita nan suka shiga bata taimakon gaggawa da kyar suka samo numfashin ta fitowa yayi agajiye yana kallon mamy yace karku damu shock ne bawani ba insha Allah zuwa anjima zata tashi mum mata duk abinda yadace Amman bata son hayaniya.

Kamar bayan awa hudu suna zaune suka jiyo ihun meenal da azama suka karasa dakin sai kalle kalleta take a dakin, sai a lokacin scene din dazun yadawo mata aka, ihuuu ta kwala tareda rufe bakinta tana kuka sosai plss Ina maleek yake karkucemin ya mutu nooo it can't be tafada tana firge drip din dake hannunta tana kokarin sauka, rirriketa akayi Ana kwantar mata da hankali Amman tace inaa itagun maleek zata haka aka Barta tafiya take tana Dafa ban go kamar zata fadi don jiwa ke debarta babu ko takalmi a kafarta,

Dede zata shiga dakin taga Ana kokarin fita dashi daga dakin, kamar mahaukaciya ta tare kofar tana Ina zaku kaishi wallahi be mutu maleek baze mutuba yanzu,

Kallonsu Abba yayi yace ku Batta taganshi plss, ahankali tashiga kamar tana tsoron gurin dukawa tayi dede fuskar sa tana kallonsa tadadetana masa addua tana kuka Amman wannan karan ba mai sauti ba saidai hawaye dake zuba idonta tamike da zumarfita kenan tareda goge kwallan dake idonta, kwallan ya gangaro ya sauka a fuskarsa, tayi kokarin Dena kuka Amman hakan ya gagara Bama tasan sanda kwalla ke fitowa mikewa tayi zatafi har ta Kai tsaki yar dakin tajuyo don masa kallon karshe babban yatsa sane taga kamar yana motsi,,komawa tayi da sauri ta duka tana kama hannun, hannunta tasaka a gefen wuyansa taji jijiyarsa na halbawa kadan kadan mikewa tayi a rikice tanufi office din murad, Doctor wallahi be mutu ba yana motsi doguwar suma yayi,

DA azama murad yamike yanufi daki nan da sauran doctors suka dukufa akansa, bayan kamar awa biyu murad yafito fuskarsa daukeda murmushi yana Alhmdullh his awake daman doguwar suma yayi Amman yanzu zamu canza masa daki Don basa kyayyawar kulawa.

Kamar hadin baki gabadayansu sukace Alhmdullh wani sanyi meenal taji ya ratsata lokaci guda,

Daki aka canza masa tare jona masa oxygen daze taimaka ma numfashinsa, ganin dare yayi yasa dukansu suka koma gida don yin salloli da con abinci, kasancewar doctorn yace musu duk sutafi sai gobe gobe ze tashi.

Kamar karfe ukkuna dare doctor Zahra ta zagaya duba patients kasancewar ita ke night duty, dakin maleek tashiga takunnan hasken dakin alluransa taduba tareda canza masa wani drip din tana gamawa harzata fita, sai tasake dawowa taja masa blanket dinsa tarufeshi sosai,

Ahankali taga yabude ido yana kallon ko ina a dakin, wani kayatattacen murmuahi tasakarmasa taresa cewa Alhmdullh kasa boye farin cikin ta tayi, shikuwa Banda ido babu abinda yake binta dashi bude bakinsa yayi da niyar magana Amman yayi yayi maganar takasa fitowa,

Kwallane kawai suka fara gangaromasa, zaro ido tayi tana subuhanallah meyaru kuma ai kamata yayi ka godema Allah kaida kwanan ka hudu kamar matacce, kokanason wani abu ne daga mata Kai yayi yana mata alamar ruwa yakeso,

Dasauri ta nufi office dinta ta hado masa tea tareda dauko bottle water guda daya tadawo dakin, dagasa tayi da kyar ta jinginasa jikin pillow tana "astagfurrulahh ya Allah kasan bada niya nayiba Banda yadda zanyine" tea din tadinga basa ahankali yana sha da kyar, da kyar yasha  Rabin cup din ya girgiza mata Kai, ruwa tabashi shima yasha kadan ya kauda Kai, baka bukatar komai kuma daga mata Kai yayi sannan tace bari naje saida safe zandawo daga mata kai yayi tareda yin Dan murmushin karfin hali, kashe masa wutayi tareda kulle kofar,

Tana komawa office dinta takiramurad nan take Sanar masa patient dinsa ya farka shima farin ciki sosai yayi yace saida asuba zai shigo.

MALEEK kuwa Banda tuna ne tuna ne babu abinda yacigaba dayi don barci yamasa kaura.

"MALEEK"Where stories live. Discover now