maleek 31-32

553 38 0
                                    


31-32

Zama meena tayi akan couch din palon momyn ta nan tacikata da abinci kala kala saida tagama ci sannan take tayi tafito Palo tatarda anty Naina nan tashiga bata labari bata boye mata komai ba.

Hakan yayi daughter u made d right decision, kinma kanki gata da yanzu kin kassara rayuwarki yarinya, now just stay here Allah zai kawo miki wani forget everything and live happily, toh insha Allah mommy, shafa kanta tayi tace dats my girl shiyace nakesonki y are so simple.

EGYPT

Maleek tinda yashiga bedroom dinsa yau kwanansa biyu baifito ko sallah saida yayi aciki gashi baya cin abinci,

Abin tafara ba maleeka tsoro ma datayi niyar tafiya Amma bazata iya barin maleek shika dai ba gaskiya in dis condition komai ma zai iya faruwa da shi, Inda ta mom saidai ya mutu.

Abinci ta kawo masa tace haba maleek so kake kashe kanka sbda wacce kila ma tamanta dakai a rayuwa ko abinci baka ci waya gyama ka Ana ma abinci fushi huh

Sister wallahi it's not my fault kokadan u won't understand how I feel, I tried so hard Amma nakasa I can't help it, my hearth iz aching me seriously yafada kwalla na ziraro masa daga ido.

I know but u just have to u are a man maleek u have understand, just have to be strong kaji kanina, kana tunanin ni ina jin Dadi yanda nake gajinka haka, plss maleek kayi hakuri kaji

Insha Allah sister but u know d most painful part kuwa momcefa toresu inji muhassin nasan yanzu tama tsaneni, kuma yanzu ko naganta yazanyi fuskantar ta, Kullum tunina shine Ina suka tafi, wani hali suke ciki yasuke rayuwa duk bamusaniba ni inda zan ganta ko bazata saurareniba San iya bata komai na mallake sujesuyi rayuwa mai inganci.
Bakomai mallek Allah natare dasu mom kuwa nasan hakkinsu baze bartaba Amma Ina mata addua Allah y ganar da ita.

NIGERIA

Su kawo ne zaune kan tabarba sai firar suke ta yaushe gako gwanin ban shaawa, abba nata basu labarin tin bayan tafiyarsu,

Itakuwa meenal tamayizurfi cikin tunani Don babu abinda tasani gameda Abinda suke tattaunawa, kaji take ta kallo da suke wasa a tsakar gidan, itafa gidannan sai ahankali anya kuwa zasu Dade a nan duk ko ima kashin kaji kuma wai ahaka kawo nada rufin asiri, su da ma akacema talakawa a wancan kasar wallahi gidan su ya ci uban wannan, koda yake ai d country seems dirty ma, duk ita kadai ke zancen zuci daga karshe tabe baki tayi takoma ta jingina da bango

Falmata na hango zaune bakin murhu tana tuka sai turo baki take gaba Tacika bam, tace shegu Ina nan inafama da murhu suna fira kwafa tayi taja tasaki, tana share kwallan hayaki daya dameta.

Wata budurwa ce tayi sallam kana gani kasan yar kawuce bazata wuce tsarar meenal, da fara arta ta karaso tace baba baki mukayi tare da juyowa tana gaishe su,

Aikuwa gasunan yanuwanki ne gama kawacan kinyi kuwa yafada yaren Kanuri

Matsawa tayi kusa da meenal fuskarta dauke da murmushi, itama meenal din murmushi tayi

Adama tace mata _Nda doubdo_ (good evening) in kanuri

Wara ido tayi tace _Anaa saaiid jiddan bi muqaabalatak_ (Am very glad to meet u) _lam Asmaa lughataki_ (but I don't understand ur language) tafada tareda murmushi _ismii meenal_ (my name is meenal) _maa issi muki_ (and what ix ur name)

Dariya su kawu suka sa suka to baki jin nata bata min naki to ya kenan,

Adama tace kamar labarci takeyi daga ina suke, kawo yace kasar larabawa

Jiyowa adama tayi tace kinajin Hausa da hausarta irinta yan maiduguri eh Ina ji Amman kadan kadan dariya adama ta kwashe dashi jin kalar hausarta Tata, to shikenan ya kike kinzo lpia, lpia Lau cewar meenal

Haka suka fara fira kamar daman sun San juna daga karshe mikewa sukayi suka nufi daki Don sallah, suna gamawa adama ta kwaso musu tuwo, itade meenal se kallo take takasaci, tambayar mamy tayi tace _maa haza_ what is dis harara mamy ta watsa mata taja bakinta tayi shiru.

Suna zaune saiga saurayi yashigo mai kama da adama, gaishe da su mamy yayi tareda tambayar kawu, baba suwaye wa ennan jide war can suna yanayi da adama da sai haske data fita, kawu yace yan uwanka ne, wara ido yayi suka sake gaisawa, kallan meenal yayi yace ke ya baki cin abincin, mamy ce tace wai bata sanshiba, falmata dake gefe tace aikin banza inace de nan ne cibarki inma zaki ware kici kici mubamuda wani sai shi.

Madou ne yace haba mama ta na iya yiyuwa bata Sanshinba yan mata mekikeso ci yanzu, bata dago kanta tace shawarma, to shikenan madou ya fito ba dadewa sai gashi da shawarma guda biyu da drink ya mika mata murmushi tayi tace _shukran_ murmushi yayi yace nima haka tasa dariya

"MALEEK"Where stories live. Discover now