MALEEK 09

881 58 1
                                    

09

"Tin karfe 10 nasafe suka isa gida tana aje kayanta ta shirya tawuce skul Amma ahaka tagama shawaginta ba muhassin ba muhsin ba maleek duk Ranta ba Dadi ahaka takoma gida.

Maleek kuwa yasamu sauki sosai Don yana samun kulawa sosai daga gurin likitoci da muhassin da kuma sauran maid dinsa.

Toh mister man kazo mukoma gida ko tinda kawarke ni nagaji da zama hospital dinnan, nifa ban warke ba gaskiya cewar maleek ,murmushi muhassin yayi yace karkadamu kakusa warkewa.

"Tana komawa gida kamar daga sama taga Kiran muhassin dauka tayi da gaggawa suka gaisa yace I hope kindawo, eh nadawo, to leter zanzo zamu danfita to tace ta takashe wayar,

Bayan awa daya saiga muhassin gaisawa sukayi da mamy sosai takawo masa abinci yaci sannan aka kira masa meenal, ganin yanda suke fira da mamy yasa tadinga mamaki haryaushe suka Saba da mammy haka cewa yayi oya lets go Amma Danje kiyi makeup, komawa daki tayi tasako gown din atamfa da hijab dinta me hannu ta mutsika yar powder da kwalli tafito, mikewa yayi ganin mamy bata mata mgna ba yasa tabishi,

Balle motar tayi tashiga yaja suka tafi, saida ya tsaya ya sayi fruit Abinda yasan maleek naso Apple, grapes, banana dayawa Sanan suka nufi asibitin dede gurin parkin din ya tsaya tafito yamika mata ledar yace inmuje ki ajiye, tace toh, binshi tadingayi saida taga sunzo VIP yayi knocking aka bude,

Kwance yake kan gado yana game da waya suka shiga, jitayi gabanta yafadi tasauke ajiyar zuciya Amma har ga Allah taji Dadi Dadi kujera muhassin ya nuna mata tazauna, daure wa tayi ta dedeta muryarta tace sannu ya Jiki dago wa yayi yaji farinciki fal zuciyarsa kamar anmasa Bushara da aljanna Amma sai yakara langabewa yana da sauki fa yadan matso kusa yayi kasa da murya yanda muhassin bazejiba yace kinga yanda kika illatani ko harara taimaka masa yayi saurin dafe hannu yana wash Allah, muhassin ne yace lpia,

wallahi hannuna ta fama min baka gyamata hannuna na da problem ba

mamakine karara afuskarta tana yaushe nataba Hannun,

saida yafaici idon muhassin ya kwashe mata ido daya,

Harara ta watsa masa tareda kauda Kai

muhassin dariya ya gumtse Dan duk yana kallansu, yakuma ga zallar soyayyar maleek a idon meenal

Mikewa yayi yace to malam mu zamuwuce fa ga fruits meenal tasiyoma,

hannu yamika yana murmushi yace tankuu yan mata,

ya mutsa fuska tayi ta mike tace Allah ya Kara sauki,

kokarin mikewa yake Don rakasu yar Kara yasaki tai saurin jiyawa saitaga yana murmushi Don dama Don ta juyo yayi hakan tsaki Taja tace mutum sai rakin tsiya, cewa yayi ai dayake kece kika nakasani saurin ficewa tayi tana murmushi a mota ta tarda muhassin yaja suka wuce har kofar gida yasauke ta sannan yajuya yawuce.

Wani irin nishadi take ji kawai Wanda batasan dalilin sa ba ko dan hakan yanada nasaba da ganin muhassin ne ko maleek oho

Yana dawowa daga Kai meenal ya Taras maleek har yakusa cinye kayan da meenal takawo masa, kama baki muhassin yayi yana mamakin maleek, maleek yajuyo yace yasin bazan Kara kwana asibitinan ba gidan zani akarasa budani a gida, muhassin yasheke da dariya yana tho lover boy tashi ai dama nasan kawarke Don tsabar rashin ta ido ko kunya bakaji.

Kwashe kayansu sukayi driver yakaisu gida

Washegari meenal ko bataje makarantaba sbda tasan ko taje ba ganin mutanin nata zatayiba

Bayan yakoma gida sau biyu meenal taje gaishe shi itada muhassin, Amma bata gigin nuna masa zunzurutu soyyayar da take masaba

Bayan jirginsu mom yasauka da dare tinsafe maleek yashirya yaje sugaisa

Zaune yake kan red Royal chairs dinta a mini Palonta mom, inakwana ta amsa masa a dakile KO tambayar jikinsa batayiba,

Kai tsaye tace me Kake zuwayi a unguwar da Akace anaganin ka,

Kai tsaye batare da wani tunani ba yace gun budurwata nake zuwa,

Amma kaji kunya Anan kake neman min suruka toh kasake tunani Sam baze yiyuba kana magajin SALMAL duk cuku cukun danake don natara ma dukiya Amma kakare a daukomin yar talakawa Ina budurwarka meenah,

bata rai sosai yayi yace mom karmufara haka dake niba mace bane da zaki zabamin mata so allow me I also have a test,

Wayarta ce tadauki Kara aminiyar tace takirata sai da tayi murmushi sannan tadauka jinayi tace to saikin zo, jiyawa tayi tace maleek I have a guest bani guri, har ya mika tace emm nanda next 2weeks akwai meeting na shareholders a Phoenix and Kai magajin salmal Ana bukatar kayi signing so sai ka shirya, baice mata komai yafita Don mugu taici.

Bayan like 2hrs saiga hajiya kubra tashigo cikin faraa suka gaisa da mom tace hajajju kenan sai yau kika dawo kenan wallahi kuwa nan da 2weeks ma zamuje meeting da maleek, Dan Danan hajiya kubra ta bata rai sai tai saurin yin yake tana hajiya Abdul bazeyi aurebane mom tace ai his still young inaga haryanzu baisamu wadda tayimasa bane

Hajiya kubra tace wai hajiya Ina maganar mu ta kwanaki kinsan hajiya kinason cikar burinki ki kauda maleek kawai kamar yanda kikayi da gyatiminsa, zero ido mom tayi cikin tsantsar bacin rai tace kina nufin nakashe shi kome kinsan yanda nake sonsa kuwa dukiyar ubanwa nake taramawa toh shine magajin kamfanin kan ubansa fa wat did mean by ur speech takarasa maganar tana zaro ido cikin masifa,

"hajiya kubrace ta hadiye wani abu tana yake tace hajiya Maida wukar wasa fa nake miki ke kuwa yazance akashe auta ni wallahi dama zaki hadasa da Laila sunyi matching, mom tace wace Laila, tawajena mana kinga yanda tazama budurwa kuwa she's 23 fa, murtukewa mom tayi tace hajiya wallahi nagaji lets talk gobe Ina son nahuta to hajiya a huta lpia sainadawo ko jibi tafice tana wallahi baki isa ba sai munci dukiyar nan muma muguwa Marar alkhairi.

"Cikin kwana kinnan meenal jitake kullum wutar San maleek kara ruruwa take cikin kokon Ranta Amma agabansa wulakanci take masa wai Don karya rainata

"Ana gobe tafiyarsu maleek yaje har gidansu menaal yace meenal zantafi kuma bayanzu zandawo ba zanje na nemo mai sona tinda kinkini baki sona bansan menamiki ba amma duk abinda na miki kiyafe min Allah kuma ya kaddara saduwar mu innadawo toh inkuma nasamu wadda take sona a Can shikenan sai muzo muku yawo, yakarashe maganar cikin da bacin rai kamar zeyi kuka Don Sam bayasan tafiyar mom ce ta matsa masa yana fadar haka yawuce ranar meenal kwana tayi kuka sbda tunanin rayuwarta ba maleek sai yanzu tagane ashe da shakuwace tsaninta da muhassin ba soyyaya ba Don bata tabajin Abinda take ji gameda shi ba yanzu.

"Dasafe muhassin yazo daukarta akan taraka maleek airport jirginsu zaitashi bai 10, suna isa suma suna isowa waya muhassin yama maleek akan sun iso excusing kansa yayi daga gun mom ya Taras dasu a mota fita muhassin yayi ya basu guri ya Dade yana kallonta yasan har ga Allah yasan yana mugun son meenal, itama kallonsa take wani mugun sonsa na fisgarta gudun kar ayi abin kunya yasa tasauke nata idon,

" cewa yayi inasonki meenal kisa aranki koda sonki ze kashe ni bazan Dena sonki ba kuma duk yanda zanyi nisa dake zuciya ta na tare dake I love so much, no word I can use that can express d love I have for u , kimin addua saina dawo miss u baby, jin taki amsa masa yasa yafito da envelop fari ya ajemata yafice Don mom nata kiransa ganin ya fita yasa ta kwace da kuka mai cin rai tana kallonsa jitake kamar takirasa tace masa itama tana sonsa kwatan kwacin ko ma fin yanda yake sonta........

MALEEK safe trip a dawo lpia..

MRS AVBDOOL CE.......

"MALEEK"जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें