maleek 67 _ 68

497 28 0
                                    

   67_ 68

Not edited

"Mom kuwa har lokacin tana kwance tana barzar kuka" maleek jin kukan mom yake har cikin ransa lokaci guda zuciyarsa ta karye, balle murfin motar yayi tare da fitowa yanufi part dinsa, dafe kansa yayi jin yanamasa masa wani mugun ciwo.

Maleeka ma fitowa tayi zuciyarta duk ba Dadi tawuce ciki, mikewa mom tayi tana kakkabe jiki tareda share kwalla, hakan yayi dede da shugowar su mamy wanda mom dince tamusu waya tana Sanar dasu abinda ke faruwa, mamy ce tafito da sauri tana kama mom taresuka shiga cikin palourn suka zauna har lokacin mom na kuka kallonta ta mamy tayi tace
"Kidena kukan nan hajiya babu abinda ze Kara miki ki zauna muyi settling komai, Ina su maleekan suke" nuna mata kofar Dakinta tayi, mikewa mamy tayi tanufi dakin Kai tsaye bata tsaya knocking ba turawa kawai tayi tashige kwance taga maleeka tana kuka sosai, tausayin ta mamy taji sosai ta matsa jikin gadon tareda dafata dagowa tayi da jajayen idanunta tana kallon mamy, sai takejin daman mamy ce ta haifeta don tana son matar sosai, to wai meyasa ma ba haka tasu uwar takeba, ganin kallon da maleeka ke mata yasa tagane tana tsananin bukatar kulawar uwa tana neman me lallashinta,

Jawota mamy tayi ta rungumeta sosai cikeda kulawa, kuka kawai maleeka ta kwace dashi mai cin rai, mamy bata hanata ba sbda tasan kila Idan tayi kukan zata samu saukin abinda takeji cikin Ranta, kuka sosai tayi don tafi minti 10 goma tana yi, jin tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa yasa mamy tasaka hannunta a bayan maleeka tana bubbuga mata kamar karamar yarinya cikin sayin murya tace

"Ya isa maleeka nasan it is very painful dole kiyi kuka, Amman abinda nake so kisani shine lokacin kuka ya kare kutashi kawai a gyara Barakar da ta faru, kiyi hakuri nasan ke yace mai biyayya wanda kowane iyaye zasuyi fatan samun Amman sai kuka samu uwa Mara Kula wanda kanta kawai tasani Amman wannan duk yawuce yanzu insha Allah mom tayi nadama kuma tagane kuskurenta she promise to be a good mother Dan Allah kiyafe mata kinji daughter nasan u have a good hearts kuma zaki yafe mata Amman ko zuwa gaba lets bygone be bygone kinji ko"

haka tacigaba da fadamata kalamai masu sanyaya zuciya.

Da kyar maleeka ta dago jajayen idanunta tace "mamy babu abinda zaki rokeni na kasa miki shi ke uwa ce tagari Allah y saka miki da alkhairi na yafe ma mom duk abinda tamana"
tafada tana sauke kanta kasa.

Sake rungumeta mom tayi tace haka nake so Allah yayi maki albarka kinji daughter, Ameen mamy tafada a takaice.

To yanzu tashi muje Palo sai mu sasanta komai Amman kafin nan shiga bathroom ki wanke idonki,

Mikewa tayi jikinta ba kwari tashiga badadewa tadawo,tare suka fito da mamy Dade abba ma suna shigowa da maleek bayan ya lallashe shi.

Mom Sai binsu take da idanu tayi tsamo tsamo kan kujera abin tausayi.

Mikewa mom tayi taje gaban maleeka har kasa ta durkusa cike da nadama tace maleeka ki yafemin nasan na cutar daku Amman WAllahy nagane kuskurena kuma nayi nadama, karku tafi kubarni nikadai ku kadai Allah ya bani aduniya dake da maleek Idan kuka tafi kuka barni wa zan dinga gani Ina jindadi tafada tana kukan nadama

Dagata maleeka tayi ta tarungume ta daman ta Dade tana kwadayin wannan yanayin, cikin kuka tace mom bazamu tafi mubarki ba munyafe miki duniya da lahira mom muna son ki sosai, dago maleek mom tayi tahada su ta rungumesu tare tana ina sonku fiyeda komai a duniya Allah yayi muku albarka ya hada mu agidan ajannah tare, ( hmm kalmar da bakin mom be taba furtawa ba kenan)

Ba su maleeka ba hatta su Abba sunji Dadin hakan sosai

Kara matse su mom tayi kamar wani ze kwace mata su lokaci guda kuma wani mugun shauki da kaunar yaranta na ratsata( hmm uwa da d'a sai Allah, Allah Kara mana kaunar iyayen mu kuma ka karama yaranmu kaunar mu)

"MALEEK"Where stories live. Discover now