maleek 10

791 55 1
                                    

   

10

"Anan Inda yabarta taduka tana barzar kuka kamar Allah y aikota, shikuwa gun muhassin yaje sukayi hands shake yace kakula da ita sannan yawuce shiga jirgin yayi ranshi a jagule.

Muhassin komawa yayi gun meenal, tana ganinshi takara fashe wa da kuka tana plss kacemai yadawo wallahi nima inasonsa sosai fiyeda yadda yakesona takarashe maganar tana shessekar kuka, muhassin jiyayi wani abu ya tsirga mai zuciya Amma yadaure, baihanata kukan ba saida tayi me isarta sannan Dan kanta tayi shiru,

shiga yayi motar yaja suka bar airport din, direct supermarket yashiga da ita yamata siyyaya sosai sannan yawuce da ita gida, direct dakin ta tawuce Don idanunta dasukayi luhuluhu tana kwanciya bacci yayi gaba da ita, sai bayan zuhur tatashi tagabatarda sallah, tafito ta iske su zaune Inda suka Saba cin abinci a sabule  jikinta ba kuzari tazauna abimcin da aka zuba mata tasa cokali tagama cahukulashi yinkurin amai ne yazo mata dasauri tamike tashige toilet tana shiga kuwa ta kwararo shi mamay ce tamike da sauri ta isa tana subhanallahi lpia meenal, dauraye bakinta tayi tafito, mammy ce takai Hannu a wuya ta taji mugun zafi, inalilahi meenal da baki lpia kikayi shiru, tin yaushe itade batace komai ba mikewa tayi takoma daki ta dukunkune cikin bargo ta dauko envelope din da yabata tana budewa wani frame tagani mai mugun kyau da leter a aciki kwallane suka fara kwaranya a idonta masu zafi tana tuna maleek da rashin mutuncin da yayi mata da farko,a zuciyarta tace wannan wace irin jarabta ce haka, jin antaba kofa yasa tayi saurin goge kwallan mamy ce tashigo rikeda magani da cup din ruwa tace meenal tashi ga magani, kallan ta tayi tace kuka kuma kikayi meenal,aa mamy kaina  fa ketaciwo  To meenal Dan kanki na ciwo sai kiyi ta kuka maza karbi maganin kishaye kinji, karba tayi ta watsa su baki takoma ta kwanta.

Ranar  da zazzabi ta kwana sosai baccinta kuma cike da mafarkin maleek, abangaren  maleek kuma tin da suka sauka Phoenix baida time his so busy meeting ne suke yi sunki karewa  saudaya ma sukayi waya da muhassin mom duk ta matsa masa basu nan basucen Abinkaa da Dan Hutu duk baisaba da wannan abunba.

Kwananta biyu zazzabinta yaki sauka Sam ,muhasine yasamu labari yazo har gida gaishe ta tareda kayan dubiya  nomban maleek yabata yace takirashi anjima zamuyi magna sannan yabargidan,

Dadare kuwa haka akayi miss calls ukku tamasa no response da text Amma shiru kwalla ne suka fara Zubo mata Allah de yasa ba fushi yayi ba, kilan ma yana can yasamu baturiya suna soyyaya itanan daren ranar batayi bacci ba sai sharbar kuka take, shikuma maleek tin 8pm suka shiga meeting Amma basu suka fito ba sai after ten direct bacci ya kwanta baima tsaya duba wayaba.

Sai washegari yaga miss calls ganin bakuwar nomba yasa bai ma bi takantaba, su meenal kuwa saida tasha drip da allurori Sanan tawarke, muhassin kuwa nakokari gun Kula da ita Dan yanzuwa akai akai kuma yanzu tarage damuwa sosai aranta Amma Kullum dadare sai tayi kuka, kuma haryanzu basuyi waya da maleek ba.

Ranar wata Friday muhassin yace ma meenal zasu Dan fita zuwa unguwa dama sungama magana da mamy, tin wajen ten yazo daukanta direct gun make up yakaita akamata makeup sosai tayi mugun kyau akasaka saka mata wata Turkish abaya mai kwalliyar duwatsu ajikinta masu kyau da daukar Ido saida aka kammala komai Sannan aka kira muhassin kallonta ya tsaya yi Don shima baisan meenal nada kyau haka ba, direct wani hall yaje da ita which is well decorated ga kayan ciyeye kala2, idontane yasauka akan katon cake anrubuta happy birthday meenal gamuka wani kyalle mai kyalkyaki anrubuta happy born day har ga Allah tamanta yau birthday dinta, murmushi tasaki cike da murna tana kallon muhassin Dan batasan mezatace masa jitake kamar tayi tsalle ta rungumeshi Don tsananin murna, sai da taci komai iya cinta sannan yadauketa suka wuce park gun wassanni, wasa sukayi kala kala har ta manta da kawai wata damuwa aranta sun sha pix kala kala wani tana dariya wani kuma tare suka dauka suna dariya wani kuma duk yashafa mata icing din cake a fuska haka ranar cikin farinciki tayi ta sosai, kuma daman muhassin yayi haka Don kawar da damuwa dake Ranta, suna hanyar dawowa taga wani bakery Ana gasa shawarma tana ta kallo yawunta na tsinkewa kamshi duk ya cika ya, muhassin fakawa yayi yasauka yasiyo mata dayawa yamika mata karba tayi tana tunanin yaakayi yasan Abinda take so kenan, bashakka muhassin yasan ta yasan damuwarta yakuma San Abinda takeso, har kofar gidan su ya sauketa yaciro wani bracelet mai mugun kyau yace  handle it with care inya bace friendship dinmu ya kare godia tadinga zabga masa sannan tawuce shima yawuce.

Two days later tashiga skul suka hadu da sholy sunfira sosai takebata labarin yanda take son maleek yanzu takuma nuna mata pic dinsu na birthday, wow aiko kinyi kyau kwata Ina cake dinmu, walalhi nima banwaniciba duk nagama rabarwa to ai shikenan, meenal tace zanuwuce gida nikam, ok toh muje naraka ki, Amman meenal sai naga kamar book dinki a can ko duba kiga inshini kidauko, tana tafiya sholy taisaurin duba Jakarta tazare pix dinda sukayi ta tura Jakarta, meenal tace banawa bane ke irinshine, ok ai nazata nakine oya muje ga jakarki suka fito ta rakata itakuma tawuce gida.

Ana gobe maleek zedawo taje saloon ta gyara kanta sai kamshi yake tamasa cup cakes Don tasan yanaso, ranar dawowarsa kuwa makeup tasha sosai dawata gown mai masifar kyau baka tayi rolling din gyalen tayi kyau matuka kuma takara fitoda da haskenta,

suna isa airport jigirsu na sauka, wani farinciki take ji Mara misaltuwa, kallon shi take sanye cikin black suit maimugun kyau da tsada iska tana kada sumar kansa yayinda yake saukowa daga matakalar jirgin idonsa Sanye cikin shades, sai taga yakara mata kyau, haske da kwarjin,aranta ta furta gaskiya maleek kyayyawane na karshe  gashi yakoma Abdulmaleek dinsa nada sak,  Karasowa yayi kusada muhassin sukayi hands shakes while mom tana can suna gaisawa da mutane, hango meenal yayi tayi mugun kyau saidai tadan fada sosai, saurin kauda kansa yayi gefe guards dinsa nata miko gaisuwa yashige mota gidan baya while mom na gefenshi, aguje aka fixgi motar suka bar airport din, meenal kuwa statue tazama a tsaye kwalla na kwaranya a idonta........


MRS AVBDOOL CE.......

"MALEEK"Where stories live. Discover now