Page 11

4.6K 113 5
                                    

🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

1⃣1⃣

Da zuwa na ajin mu na fara shiga na zauna har lokacin yin assembly ya kai na fito ban ga su salma ba abin ya dame ni matuka duk a zato na koh latti suka yi nai ta saka ido amma shiru har muka gama muka koma ajin mu class teacher din mu ce ke fada mana wai ai an yi rasuwa gidan su falmata wani kanin ta ne ya rasu jiya da dare shi yasa basu zo makarantar ba yau

Kawayen su na ta jin tausayin su ciki har da ni da muka hadu jiya

Class teacher ce ta ce mana kawayen su uku su shirya in an tashi break za'a je gidan su da malaman makarantar domin yi musu ta'aziya

Biyu sun fito safiya hafiz da precious Matthew aka rasa wa zai cike na ukun kowa a zaton shi ni zan fito in cike su nikuma gaskiya Abbu ya hana ni zuwa koh nan da chan in ba a cikin makaranta bane

Tunohaka haka ya sa nace musu ni bazan je ba in an tashi zamu tafi ni da baba na sun ji mamaki ganin yanda muka saba sosai a jiyan amma in ki zuwa gidan su gaisuwar rasuwa a karshe dai da su su biyun aka yi tafiyan dan babu wanda ke son zuwa saboda bala'i irin na su salma da falmata (yarinta kenan a ce an rasa rai ana son ayi aikin lada amma kowa ki yake yi wai saboda wani kankanin dalili Allah ya sa mu dace)

Ana tashi break suka tafi ni dai Allah ya sani naso tafiya amma ina tsoron Abbu ya zo ya ji cewa na bar makaranta ba tare da izinin shi ba

Da suka dawo ne safiya ke gaya min wai ai sun ce a ce min sun yi fushi ban je gidan su tsakani na da Allah sai na fara kuka sabbin kawaye na sun yi fushi da ni toh nikuwa yau sai na tayar ma Abbu da rigima mun tafi gidan rasuwar in ya so na sami hanyar kubuta daga zuwa makaranta

Tunowa da nayi da wannan idea din ne ya sa na yi murmushi nace ma safiya
"Ai zan tafi gidan su in an tashi daga makaranta"ta ce toh

"Amma kin san gidan"
Na ce a'a ki gaya min sai ta ce min a ta federal housing gidan yake kenan kusan wuri daya muke tunda mu a 2/1 market muke su kuma kafin a zo nan anguwar mu suke

Malaman mu sun shishigo kuma duk wanda ya shigo sai ya kira attendance wanda ya sa duk wanda aka kira sunan shi sai ya tashi ya amsa toh ta nan na kalle yan ajin namu daya bayan daya ban dai rike sunayen da fuskokin duka ba amma na san wasu

Mun tashi a makaranta kamar jiya muka fito bakin gate in da muka jira Abbu jiya yau ma a nan muka jira shi da ya zo sai na gaishe shi na gaya mishi abin da ya faru yau wanda aka gaya mana a makaranta

Sai yace
"Toh mama na ya za'a yi yanzu kin ga anjima akwai Islamiya"

Ai tunowa da nayi da yaran nan sai kawai na hau dadaga Kafa akan ni dai mu tafi gidan su salma saboda suna so na

Kallo na Abbu yayi shi dai ya san ban da rigima bayan surutun tsiyan da nake da shi sai gashi yau ina gwada mishi rigima karara
sai ya ce mama na toh na ji zamu tafi amma ke kin san gidan ne?

Da murna nace ai safiya ta ce min a federal housing su ke

Ya dan tsaya na wasu yan mintoci yana nazari idan dai bai manta ba toh federal housing angwar masu hannu da shuni ne toh ita wannan a ina ta samo kawaye masu kudi haka

Da naga shirun yayi yawa na dauka fasawa yayi sai kawai na saka kuka

Ya yi saurin dago kan shi yana tambaya na lafiya

Na ce "Abbu ba ka fasa zuwa da mu bane kuma ka ga hasina kanwar salma kawar ummi ce toh kuma Abbu sai ka ce baza mu tafi ba" na cigaba da kuka

Abin ma mamaki yake ba Abbu sai ya ce

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now