Page 61-62

346 7 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

*wannan shafin kyautar shi naku ne Brilliant Writers Association Allah ya bar zumunci*

6⃣1⃣➖6⃣2⃣

Kwanaki sun ja sosai dan yanzu kusan sati biyu kenan da dawowa ta amma Abdulrahman shiru duk hankali na ya gama tashi dan ban san ta yadda zan yi reaching ɗin shi ba tun ina boyewa har ya fara fita sarari dan ko da ummi ta kawo mana ziyara ban wani yi ɗoƙin ta ba kamar yadda ya kamata ita kaɗai ce ta lura dan haka kafin ta tafi gidan ta ta same ni in private da fari ɓoye mata na yi sai na dai sanar da ita shawarwari ta bani haɗe da min alkawarin taya ni da addu'a akan Allah ya sauƙaƙa min godiya na mata at least na rage heaviness da ke zuciya ta..

A haka na cigaba da rayuwa har na yi resuming aiki kimanin wata guda babu shi babu dalilin shi ayyukan shi da ke kamfani na wanda ya kamata a ce shi ke yin su ni na koma yi mai daurewa kawai nake yi dan ba na so a ce da matsayi na da sunana da yayi ƙauri a duniya ina shiga wani hali saboda ɗa namiji rufe komai nake yi ina saka fake appearance ba dan ina so ba abu kamar wasa sai da muka kai watanni uku bamu saka juna a ido ba iya rikicewa na rikice dan gani na yi kamar duk abubuwan da suka faru tsakani na da shi mafarki ne ba gaske wasu lokutan kuka nake rufe kaina in yi dan Abbu ba mazauni bane aunty mama tana ji da business din ta yawwanci a boutique ɗin ta take yini saboda takan share watanni bata tafi ba saidai ta rinka monitoring ta waya toh in ta tafi duba business din takan jera sati biyu zuwa uku tana zuwa toh zaman ta yakan dan yi karanci most of the time sai dare take dawowa around 6-7 ni kuma around 5-6 intervals din hiran tamu bai da yawa sai kowa ya wuce makwancin sa ko da weekends takan tafi ni kuma dole zaman gida ya aure ni during the weekend dan ban ma cika son zuwa gidajen aminai na ba gudun kar wani ya gano halin da nake ciki ummi ƙanwata ce bai kamata on rinƙa zuwa gidan ta a duk sadda nake less busy ba toh ta hanyar da nake rage loneliness ɗi na shine ziyara zuwa orphanage homes un zauna mu tattauna da su un ji matsalolin su in taimaka masu a duk ranar da na kai masu irin wannan ziyarar da annashuwa nake kwana in tashi dan jin dadi nake yi a haka wani watan ya kuma wucewa kenan kusan watanni biyar babu Abdulrahman babu labarin shi aunty mama ta yi tambayar har ta gaji ta bari dan ta lura kamar ban cika son jin maganar shi ba dan haka take kiyaye yi min maganar shi sai dai in wani abin ne mai muhimmanci da ya taso kuma ya zama wajibi a saka shi toh sai ta saka sunan nashi cikin hikima ta yadda zunan ba zai taso min labarin shi ba a haka na rinƙa binne soyayya ta for that 5 months..

A wata na shida ne kwatsam ina zaune ina aikin fama wato zane wanda da zarar na dauko abu mai ma'ana sai in kauce hanya in ɓige da karasawa da fuskar shi sai na ji ana buga min kofa kafin in bada izinin shigowa har ta shigo dan haka ban sami damar karasa ɓoye papers ɗin ba sai ta hango wasu murmushi ta mim ta ce

"Bar ɓoye su baby na gani"zama ta yi kusa da ni ta fara shafa min baya na tana ɗan murmushi ni kuma na yi lamo ina jiran cewar ta

"Baby yanzu ke dai baki da wani abu mai muhimmanci a rayuwar ki sama da Abdulrahman?komai kike yi sai kin zauna tunanin shi?duk abubuwan da kike yi hatta da profession ɗin ki kina wasa da shi akan Abdulrahman? Ma'aikatan ki shida kika kora daga aiki duk dan sun shigo maki a daidai lokacin da kike tunanin Abdulrahman a jin ki in shi Abdulrahman ɗin ya san wannan lalacin da kike yi zai yi murna da ke ne?ko kina ganin a yau in ya dawo ya ji cewa Aisha Murad ɗin shi ta chamza daga active most serious painter zuwa lazy unserious painter zai ji daɗi?kina ganin ko zai cigaba da alaƙa da ke ne wai dan ya san ki tun da? Ko zai cigaba da nuna maki so da ƙauna haɗe da kulawa ne kamar da? Noo baby no ba zai miki ko daya ba namiji yana son mace da ke da talent namiji yana son mace mai ilimi kuma mai amfami da ilimin ta wurin gudanar da abubuwan yau da kullum na rayuwar ta namiji na alfahari ya nunawa duniya matar sa a matsayin jigo na rayuwar shi saboda ya yarda da ita dan ya san ita ɗin mai ilimi ce da hikima dan haka bai da fargabar nuna ta a ko ina but the moment namiji ya san cewa mace is too weak a kan shi kuma bata iya aiwatar da komai da zarar ya ɓace mata na ɗan wasu lokuta kin san me zai fara gwada mata"? Na girgiza kai na ina share hawaye na dan maganganun ta sun min tasiri

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now