Page 73-74

654 39 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_Wannan shafin naku ne masoyan soyayya mai garɗi ƴan group ɗin Taskar surayyahms,Ajalin so fans,Surayyahms novel,Zauren brilliant writets,Siyama ibrahim fans page and soyayya mai garɗi fans nagode da soyayyar ku gare ni haƙiƙa SOYAYYAR KU MAI GARƊI CE nagode_

_ina alfahari da ku Faltex Farhana,Ameerahraji,Zara kyari,Zainab pindigi,Suwaiba,mmn bilal teemah aji_
7⃣3⃣➖7⃣4⃣

Kowa a wurin fuskar shi cike yake da tension except Barrister Umar wanda ya san wace ake zargin sai dai bai ambata ba salma da ke tsaye duk ta zaƙu ya furta sunan dan ta san ta inda zata fara gudanar da binciken ta an yi shiru ana jiran shi jiran ƴan mintuna kaɗan ya furta sunan wanda abin ya zo ma salma a riƙiɗe dan kuwa ji ta yi kamar hearing capacity ɗin ta ya ragu kamar jiyo sunan ta yi daga kan hanya an furta sai ta ɗauke wuta ta tsaya a wurin kamar mutum mutumi na wasu lokuta kafin wani irin muguwar zuciya ta zo ta ɗebe ta ta sauke mai wata mummunar marin da bai shirya karɓa ba ta nuna shi da yatsa

"Idan kana surkullen ka ka rinƙa sanin da waɗanda kake yi idan kana ƙarerayin ka da ka gado daga wun ubanka ka ka rinƙa bin turbar da yake bi dan shi baya fitowa ɓoro ɓoro sai ya ma ƙaryar tasa ado kafin ya fitar ta dan haka tun kafin rai na ya ɓaci hankali na ya gushe ka san ba da ƙaramar Human right archivist kake wasa ba dan yanzu zan maka abin da ba zaka taɓa mantawa da ni ba tun wuri ka gyara kalmar ka ka faɗi ƴar iskar da kuka haɗa kai kuka ɓatar min da aminiya"a matuƙar harzuƙe ta ƙarasa maganar dan ta ɗau maganar a matsayin shimdiɗar mafarin zance ne bata ɗau maganar a matsayin abin da kunne zai ɗauƙa ba bare har hankali ya aminta da shi..

"Calm down dear calm down bari ya kuma maimaita sunan maybe ya ruɗe ne shi yasa ya furta sunan". Wani tsaki ta saki gamida banka mai harara ta tsaya tana jiran shi bai fasa ba sunan dai da ya faɗan shi ya kuma maimaitawa wannan karon babu wanda ya lura da wani irin ɗamƙar da ta kai mai sai da aka ganta tana ƙoƙarin aika shi lahira dan tsabar baƙin ciki sai tari yake yi jan ta mijin ta yayi yayi waje da ita yayin da ɗan sandar kuma ya mai da hankalin shi akan Majeed da ke yashe kamar marar rai dan kuwa salma ba wasa ba in ta damƙi mutum ƙiba ne da ita kuma ƙibar ba ta iska ba dan akwai ƙarfi kamar wata mai jinnu..

An yi nasara yana numfashi amma ya jigata dan haka aka yi saurin kirar likita dan ya duba shi..

Sai fisge fisge ta ke
"Mine ka bar ni in koma in ci mai mutunci wannan wani irin wulaƙanci ne da cin fuska ta hanyar gidan uban wa ya san ta da zai saka ta a shirgin ahi wannan ai domestic abuse ne ba zan bar shi ba case ɗin shi biyu a hannu na sai ya gwammaci mutuwar shi da ƙaryar da ya min ka bar ni in tafi mine " ta fincike ta kama hanya amma muryar shi ya mata iyo a kunne ta juyo kaɗan ƙaɗan ta rinƙa bin shi da kallon tuhuma girgiza mata kai yayi ai ko ta yo kan shi da masifa

"Mine are you thinking properly at all? kaima wannan ɗan iskan ya juye maka kwakwalwa ne? did he"? ta daka mai tsawa ya haɗa ta da bangon wurin itama na daka mata tsawar

"Babu juye min brain da yayi Falmata committed this crime ita ta haɗa hannu da shi aka ɗauƙe Aisha come back to reality Mrs Amodu come back and accept the truth your Falmata is the culprit did you get that"?? Sulalewa ta yi ta faɗi ƙasa sai ga hawaye biyo ta yayi a ƙasan shima ya durƙusa yana facing ɗin ta ɗaga mata haɓa yayi ya rage murya ya ce

"Salma my blood sister my very own sister is the culprit ita ta saka shi ya haɗa plan ɗin shi da nata suka yi a lokaci ɗaya Falmata is the culprit ki daina takura kan ki kina kokarin karyara maganar shi dan iya gaskiyar shi kenan salma ki tuna fah cewa yayi her best friend in ba ita ta sace Aisha ba kenan ke kika sace ta?noo Falmata ce ni na sani kuma na daɗe da sani rashon evidence ne ya sa ban fallasa ba amma yanzu da ya faɗa da kan shi kin ga ai bana ɓuƙatar wabi shaida abokin aikata sharrin ta ne ya faɗa ko har kin manta da labarin da na baki ne jiya akan waɗanda suke da hannu a kisar mahaifan Abdulrahman? Zuba mai ido ta yi kamar statue tana bin shi da kallo cigaba da maganar yayi

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now