Page 35-36

579 40 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

_this page is for you my lovelies friendy surayyahms u are a very nice, caring,selfless and important persons to me ina matukar godiya ga duk alkhairan da kike min you are my motivator ina miki fatan alkhairi a rayuwar yadda baki da kyashi ko na misƙala Allah ya raba miki hanya da masu kyashi da masu mummunar hallaya ya baki abin da kike so na alkhairi duniya da lahira i love u so much Allah ya baki lafiya_

_Sis jamila musa{meelat musa} ban san kalaman da zan yi amfani da shi ba wurin gode maki kina da kirki da mutunta dan adam baki da girman kai balle wulaƙanci Allah ya bar zumunci ya ƙara haɗa kawunan mu baki ɗaya_

_My Miss Thomas Allah ya bada sa'a_
3⃣5⃣➖3⃣6⃣

  Da asubahin ranar asabar na tashi da wuri na yi sallah na yi azkar har zuwa karfe bakwai na safe na nannade sallayar da zanin sallar na wuce sashen Abbu na gaida shi yana zaune a palon shi morning news yake kallo inda yake tambaya ta how was my day yesterday na sanar mai da cewa it was the best except that jiya mun kara barging da juna ni da Abdulrahman a boutique har na fasa mai waya dakatawa Abbu yayi da kallon da yake yi ya ce subhanallah me kika ce mai
"Abbu bai fa bani breathing space ba ya yi gaba abin shi nima sai na wuce"na ida maganar ina cunno baki irin ni an bata min ranar juma'a ta murmushin manya Abbu yayi ya ce

"Mama na yaushe zaki girma ne waiin kin yi laifi ki bada hakuri as simple as that kin san wannan mutumin fah bai cika mua'amalar shi a nan kasar ba zuwa zuwa ne dan haka bana son ya sami bad impression akan ki saboda nan gaba kar ya gi misunderstanding din ki"

Shiru na yi sai kuma kamar an tsungule ni na mike tsaye
  "Abbu i wanna sleep muna da dinner da na fada maka about conjunction din mu da su Khadijah sai na fito".

Sarai ya san gudun maganar nake son yi dan haka na saba yi a duk lokacin da ya turƙe ni da laifi akan in bada hakuri alhalin nima an min laifin...

*************
  Sai 12 noon na tashi daga baccin da na koma da safe kuma kiran falmata ne ya tashe ni ina daukar wayar na ji kukan ta wai yaya kabeer ne jiya kayan da ta saka na bacci ta tafi yi mai sai da safe kawai budan bakin shi sai ya kirata da karuwa wai shi zata gwadawa barikanci ta je shopping jiya ta kwaso kayan ƴan iska marasa tarbiya ko wato ita ƴar karamar yarinya da ita har ta san namiji ya sadu da ita ko saboda tsagwaron rashin ta ido tana kuka tana bashi hakuri amma saboda rashin imani tsananin kiyayar da yake mata haka ya ma falmata kaca kaca forgetting that ita din virgin ce ya mata lis sannan ya tsalake ta ya wuce da kyar da azaba ta lallaba da rarrafe ta shiga bayin gidan ta tsunduma cikin bathtub ta fashe da kuka tana da ta sanin auren son maso wani da ta yi da irin cutar da ta min a ganin ta haƙƙi na ne ke bibiyarta shi yasa tana fitowa daga toilet din ta kwanta bacci mafarki ta yi da ni shi yasa ta kira ni tana kuka ta ida bani labarin""

Zuwa wannan lokacin hawaye duk ya gama wanke min fuskata zuciya ta kuma ta gama cika da tausayin aminiyata dan tun asali bata kasamce mai mummunar zuciya ba bata kyashi ko baƙin ciki da cigaban wani amma ita ce kaddara ta saukowa irin wannan na aure na ƙudiri niyar bin shawarar salma kawai in nemi yaya kabeer dan wannan hallayar da yake nunawa falmata ai ya zama cin fuska da rashin sanin daraja da haƙƙin mace shi da kanwar shi ke zaman lafiya da jin daɗi a gidan wan yarinyar da yake cutarwa kamar bai taba sanin ta ba in shi ne aka yiwa salma haka ya zai ji.

Hakuri na shiga bata na ce inshaAllah next week zan zo dan yanzu yau da gobe ina da planned schedule ɗi na but ta ƙara hakuri kuma kar ta sanar da salma da iyayen ta i will help her out haka muka yi sallama duk tausayin ta ya ishe ni..


🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now