Page 23-24

577 39 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

*This whole page is for u maman mubeena u are different from all others and very dear to me thank u so much and i heart u sincerely*

_*Assalamu alaikum wata ƴar sanarwa nake son yi yau da safe na ga saƙo ana mai sanar d ni cewa sabuwar group dina mai taken siyama ibraheem fans page an tsinci maza a ciki toh ina mai son baku hakuri da ku gafarce ni haka da gangan ba zan saka maza a group di na ba kuma wallahi yankan baya aka min dan wasu ne suka fitar da link din har mazan suka yi joining amma ba intentionally na yi hakan ba da fatan zaku amshi apology di na ku fahimce ni*_


2⃣3⃣➖2⃣4⃣

Da sauri aka turo gadon emergency na asibitin inda aka yi saurin dora falmata a kai aka yi wheeling din ta zuwa cikin asibitin da zuwan su aka danna ma likita kira yayin da nurses din ke kokarin resuscitating din ta an yi sa'ar daidaituwar numfashin ta sai dai an saka mata oxygen(abin shakar numfashi) koh da likitan ya zo ya dudduba ta ya sanar da Baba matsalarta akan zuciyar ta ne ke son buga wa kadan ya rage ya buga da an kara tsawon lokaci kafin a kawo ta asibitin dan haka ya yi kokarin sanar da su dokokin da za'a bi dan a kiyaye tayar da abin godiya suka mai mai tarin yawa kafin yaya kabeer ya kira su umma da Abba akan su zo asibiti ya fada musu asibitin suka mai tambayar waye bai da lafiya bai boye musu ba ya ce ai falmata ce some minutes later suka iso asibitin tare da su salma da hasina..

An hana shiga a duba ta har sai bayan awowi shida dan haka salma ta ce ita zata kwana a asibitin su kuma iyayen su tafi gida kawai tunda kafin ta farfado dare zai yi sosai da haka suka tafi amma mama ta ao tsayawa koh dan ta ga farfadowar ƴar ta ta kuma tambaye ta matsalarta amma taga kamar in ta tsaya ta nuna rashin kara ne ƙarara kuma ga salma da ta nuna musu kauna ta ce zata zauna ta kwana toh ita me zata yi kawai sai ta bi motar suka wuce gida amma tana ta faman tunanin menene haka da zai daga hankalin ƴar ta a irin wannan rana mai muhimmanci a gare ta toh koh dai abin ya daɗe yana damin ta ne bata taɓa gaya mata ba tunda ance bugun zuciya ne kuma babu yanda za'a sami ciwon zuciya farart ɗaya sai da kwakwaran dalili sai dai in ya daɗe ne a jikin mutum toh za'a ce falmata ta daɗe da ciwon ne bata taɓa gaya musu ba sai kuma ta juya zuwaga Baba da shima yake nashi nazarin a zuciyar shi ta ce baban faruq kana ganin falmata ba rufe mu ta yi ne"??

Shiru Baba yayi kafin ya dora da cewa  anya kuwa bana tsammanin hakan dan komai yarinyar nan ke nema ana bata sai dai in gamo ta yi da wani abin a wurin liyafar ta su amma koma dai menene zan ji dalilin da ta ke son halakar mana da kanta muna zaune kalau""

  da waɗannan tunane tunanen suka isa gida yayin da chan motar su Abba ke tsammanin koh dai wani abu muke mata ta kasa sanar da su ta boye ta gwammaci ta zauna da damuwar ita kadai tunani dai kala kala a ran su suka dawo gidan..

Yaya Kb ne ya sayo magungunan a cikin pharmacy da ke asibitin ya zo da su a hannun shi yana tambayar salma koh ta farfado ta ce mai a'a da haka ya zauna itakuma tace mai zata tafi ta kwaso kaya haɗe da abubuwan buƙata tunda kwana zata yi drivern gidan mu ya kira akan yazo ya dauke ni bayan mintuna kaɗan sai gashi ya iso suka tafi gida a lokacin da suka shiga ne motar yaya umar ke koƙarin fitowa dan shi bai ma san abin da ya faru ba zama yayi a masalaci sai da ya shigo gidan ne yake ji a wun hasina..

Lokacin da salma ta gama haɗa kayyayakin ta ne ta shiga duba yaya Aqeeb dan bata gan shi ba tun da aka fara hayaniyar nan sai ta shiga ɗakin shi ta gan shi zaune a kasan gafon shi ya cire boturan rigar shi yana famar shan wani abu a kwalba irin kwalbar turare din nan yana ta faman surutai marasa ma'ana..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now