Page 12-14

707 45 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

1⃣2⃣➖1⃣4⃣

Koh bayan mun isa gida sai na fara jin kewan kawaye na saboda wata irin sabo ne ya shiga tsakani mu farat daya toh dama chan ni ba kawayen gare ni ba Koh da muke Abadam daga ni sai kanwata ita kuma in banda shirmen da zata yi ta saka ni dariya ba na iya wani iya doguwar hira nake yi da ita ba dan bata san komai ba ga rayuwar kadaici da na taso a ciki babu uwa babu kawa mahaifi na ba zama yake yi ba tafiye tafiye in zai yi tafiyar shi  gidan wani amininshi shi yake kaimu kafin ya dawo toh shima aminin ya zo ya bar garin saboda yanayin rigingimun da ake yi barin shi garin da wasu yan watanni ne Mahaifin mu yayi tafiya  yana ta tunanin inda zai kaimu saboda gudun fadawa hannu mara kyau sai yayi ta jinkirta tafiyan har dai Allah ya kawo kanwar ummar mu da kaddara ya fada akan ta

Da kewar su na kwana na rungumo ummi sai ga hawayen da ban san dalilin shi ba saboda a lokacin ba wai gama sanin ciwon kai na na gama yi ba hawayen sai ya dinga saukowa kamar an balle kan abin ruwa ashe wai kadaici ne ni ban sani ban taba jin maraici ba irin na ranar koh me yasa hakan ban sani ba

Da muka tashi sallah da asuba sai kawai na juye ruwan wankan mu muka yi ni da ummi kafin muyi sallah hakan da nayi ya ma Abbu dadi ganin yar shi ta fara hankali da wayo har sai da ya furta da zai hada mana abin kari

Ni ko sai cewa nake ai Abbu kai ne kaki koya min yanda ake hada abinci sai ka ce wai ban gama wayo ba ga ya Ibrahim nan ka koya mishi kullum shi ke yi kuma in ya dawo daga makarantar ma shi zai cigaba da yi gashi in yana girkin har gwalo yake min ya ce ai ban iya komai ba nikuma na ce na mai alkawari in ya dawo yanzu ni zan fara yi mana abinci Abbu pls ka koya min wallahi zan mayar da hankali in koya da kyau na karashe maganar ina saka fuskar tausayi

Sosai Abbu yayi dariya ya ce eh lallai mamana kice gasa kuka dasa ke da yayan naki toh ai kuwa zan taimaka miki koh dan saboda  ki cinye gasar nan

Da murna na ce da gaske kake yi Abbu ya jijiga min kai alamu eh da gasken yake murna akan murna zan koyi girki kafin yaya Ibrahim ya dawo gidan kuma gashi salma ta ce min zata yiwa abban su magana a canza min Islamiya mu rinka yi tare

Tuna wannan abubuwan sai na yi ta washe baki ina gayama ummi ina ta murna matuka Abbu ya tausaya min ganin yanda nake ta murna akan zan koyi girki da ace mahaifiyar mu na nan yanzu ai da na kware kware fannin girki saboda mahaifiyar mu ta kasance gwana ce a fannin girke girke koh a zamanin da sukayi rayuwar su kafin ta rasu ita ke girkin ta da kanta bata yarda yan aiki su yi mata ga kyau da diri suman nan yalala babu ta inda ban daukota ba a jiki face no din dai ban da jikin da take dashi saboda yar dumaduma ce wanda a yanzu jikin yana son dawowa wun ummi ne dan mashaAllah tana da jikin hutu ga haske ba kamar ni ba da nake da duhu da surutun tsiya wanda aka rasa inda na gado shi

Yayin da ummi kam tun a lokacin miskilanci ne da ita kamar wata yar sarki dan wasu lokuta da dama in aka mata magana akan ta bar yin abin da take yi toh koh da ta bari din sai ta dauki lokaci kafin ta sake da kai koh wani irin magana zaka mata sai ta maka banza wannan hali nata yakan dan dami Abbu wani lokaci tunda shi babba ne ya rigada ya gama hasaso irin halin da zata yi a nan gaba in ta girma wanda shi kuma ba zai so hakan ta faru ba ya fi son ta kasance kazar kazar kamar yanda nake amma lokaci bai kure mishi ba zai san yanda zai tankwasa ta inshaAllah

Abin mamaki sai ga Abbu na murmushi alokaci daya kuma yana hawaye ban san dalilin shi na hawayen ba sai na fara surutun fama ce min yayi ban ga yana dariya ba na ce eh yace toh ai saboda murmushin da yake yi ne yasa hawaye fito mai sai nace toh nima bari in gwada yi abin ya bashi dariya amma sai ya hana ni yace in yi in gama mu tafi kar mu makara da haka ya min wayo dan ya lura in yana biye min da yawan tambayoyi na watarana zai iya yin kuka a gaban mu kuma ba zai so hakan ta faru ba dan koh na tambaye shi ba zai san amsar da zai bani ba

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now