Page 25-26

541 47 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣5⃣➖2⃣6⃣

Kalau muka sauka a filin saukar jirgi ta ƙasar Egypt inda daga nan na wuce zuwa taxi da zai kai ni har masauki na wanda da taimakon yaya Kb aka shirya min ƴar ƙaramar safe apartment dina babu ruwa na da komai daga school sai gida har bakin ƙofar aka sauke ni na biya ƙudin na wuce ciki dan dama akwai wanda nake ta communicating da shi shi ya kwatantawa mai taxi din har muka iso a wun wata mata na ƙarbi makulin gidan na shige..

Wanka na yi na bi salolin da ake bi na daga bisani na fiddo da soyayiyar miya ta na juye na shige kitchen din na dafa noodles shaf shaf na juye saura a kula na bar shi a kitchen din na fito da na plate din na zauna a falon ina ci sai da na yi nisa har na kusa gamawa na dau wayata na saka sabuwar sim dina ta ƙasar da na siyo a hanyar zuwar mu gidan na duba nambobin su Abbu shi na fara kira muka dan taba hirar mu ya dora da nasiha da jan kunne dan ya amince da tarbiyata shi yasa ya bar ni in ba haka ba sai dai in hakura har yake cemin da ummi ce babu inda zai ma bari ta tafi haka muka rabu na kira kawaye na muka sha hirar mu bai musu ba suka ce min anjima kafin in kwanta in yi connecting mu yi video call dan suga environment din da nake da toh na amsa musu muka sauke wayar ajiyar zuciya na yi kamar mimtuna goma sai na kira yaya kabeer kashewa yayi ya kira ni mun dade muna magana kamar kar mu rabu haka shima muka rabu sa shi akan anjima zu yi video call da shi..

Fita na yi na ɗan zaga gida ba babba bane amma akwai tsari da kyawun kallo two bedroom flat ne da toilet sai kitchen yar daidai chan bayan gidan akwai swimming pool da ƴar karamar garden ni mamaki ma abin ya bani ganin ni da nazo karatu har wani gidan hutu aka samo min Allah ya sakawa yaya kb da alkhairi dan shi ya daɗa convincing Abbu akan zuwata kasar yin karatu...

Chan cikin dare bayan na idar da sallah ne na zauna shiru though na saba da kaɗaici amma ban taɓa yin nesa da gida irin haka ba ya zanyi ni na ji na gani ai ina cikin wannan tunanin na ji ƙarar waya ta dauka na yi sai na ji muryar yaya Ibrahim

"Angon falmata da ummi" sai yayi shiru kafin yace me kike nufi da angon falmata da ummi kuma?

Shiru nima nayi dan subul da baka na yi sai na yi saurin canza topic din na ce
"Yaya Ib ya makaranta duk kewar ku ya ishe ni wallahi" dariya kawai ya min ya ce haka zan saba mun ɗan taɓa hirar mu kafin mu ajiye wayar kamar jira na yake ina ajiye wa na ji kira dubawar da zan yi na ga yaya kabeer ne murmushi na yi na janyo hijabi na na saka dan banda towel din da nayi wanka da shi ban saka komai ba har ta kusa tsinkewa na yi saurin dauka na saita a kan teburin karatu na

"Haba sweetgirl tun dazu fah nake ta kiran ki amma baki daga ba koh duk a cikin jan ajin ne"

Dariya maganar tasa ta bani dan haka na dara kaɗan kafin in tsagaita na ce mai
"A'a wallahi yaya na yi hakuri ba zan kara ba forgive me"

Haɗe girar sama da ta ƙasa yayi wai akan me zan na ce mai yaya bayan na san ya hana ni kiran shi da yaya wata dariyar ya daɗa bani dan haka na kuma yi a karo na biyu
"Wai toh me kaje son ina kiran ka da shi ne yay..."sai kuma na yi saurin rufe baki na dan kalamar yaya da ta so fito min a bazata shima dariyar na bashi amma murmushi kawai yayi ya kyale ni dan ya san sunan da ya bani in rinka kiran shi ba zan taba amfani da shi har sai ƙila mun yi aure shiyasa shima bai damu ba sai muka cigaba da hirar mu a nan yake min bayanin in tabbatar da gobe na gama komai nawa a school saboda next day din in fara attending lectures di na yace min wannan mutumin zai taimaka min godiya na daɗa yi mai muka yi sallama na kara saita wayar na kira salma a lokacin hira suke yi a sashen su falmata dan haka tare suka yi receiving call din da murna muka taba hirar mu har tsokana ta suke yi wai matar babbar yaya ta taho ƙasar larabawa har wata hijabi ce da ni a cikin daren nan ni dariya kawai na musu dan in har zan biye musu toh ba zan yi bacci ba ga shi na gaji maruka ina son rintsawa sun lura da hakan sai suka min saida safe muka rabu saka wayar nayi a chargi na cire laptop di na na ajiye a bedside drower kashe light din na yi na jawo duvet na tofa adduo'i na kwanta da gefen dama daga nan sai bacci..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now