Page 21-22

569 44 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣1⃣➖2⃣2⃣


  A firgice yaya Aqeeb ya tashi tsaye yana nuna yaya Kb da hannu sai ya kasa cewa komai ya tsaya tana kallon shi shima da dariya a fuskar shi yace
"Yes today is Aisha's Birthday which rhymes with her graduation celebration so am happy to wish you a very big happy sweet 17 dear"

Tafi ne kawai ya kaure a hall din dama abu na yan boko yan duniya gasu yan Abuja da ketare hakan ba abin mamaki bane a gare su, gabaki dayan yayyen mu tasowa sukayi suna bawa yaya kabeer hannu tare da yi mai godiya ta musamman illah yaya Aqeeb da ya fita daga hall din ba tare da sanin kowa ba..

A nan fah sabuwar tattaunawa ya kaure tsakanin yan jaridu da mu ni da na rasa abin cewa dan shaf na sha'afa  da wai yau ne Birthday dina sai yanzu ban gama warwarewa daga murnar liyafar da aka haɗa mana ba ga wani gagarumin kyauta kyautar da koh Abbu da ke mahaifi na bai bani ba na rasa abin cewa kuka zan yi a'a godiya zan yi a'a koh rawar murna da jin dadi zan yi ganin irin wannan kyautar da ban taba tsammani ba nan kusa a rayuwa ta ba..

Tashi Abbu yayai ya zo gare mu ya rike hannun yaya kabeer tare da kiran sunan shi

"Kabeer wannan kyautar da ka yi bamu da abin cewa sai godiya da yi maka addua'a da fatar alkhairi amma kabeer wani hanzari ba gudu ba me zai hana ka ajiye wannan kyautar har sai Aisha ta kara girma da wayau tunda yanzu dai ka gani yau take cika 17 bata wani gama hankalin kanta ba ka bari har sai ta kai koh irin 20 years and above din nan ina ga kamar in har ban maka katsalandar ba tsakanin ka da kanwar ka ba ka yi amfani da na wa shawarar a gani na hakan zai fi" daga haka Abbu ya ja bakin shi yayi shiru already Abba da umma sun fara fahimtar wani abu game da wannan kyautar ta yaya Kb dan haka ƙalla basu ce ba suka zuba mai ido kawai yanda kowa ma ya zuba mana idanu..

  Juyowa yayi a hankali yana mai kallon Abbu kamar wanda ya nemi abu aka hana shi sai ya sunkuyar da kan shi ƙasa ya fara magana

"Abbu da farko dai ina so in nemi afuwar ka na yin kai tsaye akan ikon ka kuma dolen ka ba tare da na nemi izinin ka ba Abbu ka yafe ni amma ni a gani na yau ce ranar da ya kamata duk mu haɗu mu saka Aisha farinciki duba da ganin cewa marainiya ce bata da wanda zai bata irin kulawar da zamu bata a yanzu bata taso cikin mutani da yawa ga kadaici da ya ta dawainiya da ita in har zan iya tunatar da mu Aisha bata taba celebrating birthday din ta ba so yau ce ranar farko da ya kamata a haɗa mata duk wata farincikin da ta daɗe bata yi irin shi ba wannan shine dalilin da yasa na ce ni kuwa zan shiryawa Aisha babbar surprise da zata y farinciki a rayuwar ta ita ce dalilin da ya sa n haɗa wannan ƴar liyafar saboda ina ganin koh baka kusa ni mai iya yi ma Aisha komai ne a matsayi na na wan ta kuma kanwa a gare ni amma yin hakan ya bata maka rai ina mai baka hakuri da daɗa neman afuwar ka Abbu ka yafe ni""ya ida yana mai haɗa hannayen shi wuri ɗaya alamun roko

  Kamar ruwa ya cinye Abbu haka ya yi tsit a wurin shi abin da yake nufi daban ne kuma yana tsoron kar jama'a su zarge shi da son kanshi da yawa bayan ga kannen kabeer din nan bai basu kyautar kwatankwacin abin da ya bama bare ba shiyasa ya yi kokarin dakatar da shi sannan tunanin da shi bai yi ba tuntuni shi kabeer din yayi wato hada min kwaryakwaryar birthday koh da sau ɗaya ne a rayuwata amma bau taba qamnan tunanin ba daidai da rana daya sai gashi wannan ya haɗa wa ɗiyar shi da zuciya daya amma ta eaaa da me zai saka mishi sai disappointment hakan kamar bai dace ba sai Abbu ya kalle shi ya fara magana

"Kabeer kar ka min mummuna kokuma bahaguwar fahimta kyauta tsakanin ka da Aisha babu wanda ya ke da ikon hana ka yin shi ciki kuwa har da ni mahaifin ta hakan da nayi nayi ne dan ganin kamar kyautar tayi yawa amma ba wai dan ban yaba ba amma ni ma ina mai baka haƙurin yin kai tsaye a kan hukuncin ka tsakanin ka da kanwar ka kabeer da fatan za ka fahimci nufi na da kyakyawar fuska"

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now