Page 27-28

512 43 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣7⃣➖2⃣8⃣

"Barkan ku da zuwa taron aure na ni da masoyiyata sahibata wacce take tare da ni tun yarinta na wacce ta amince zata aure ni a mafarki na ohhh na manta aunty habiba(kanwar umma ce uwa ɗaya uba ɗaya a kasar jamis take aure shekaran ta 15 da aure amma Allah bai taɓa bata haihuwa ba) ban faɗa miki ba hmm kin san kuwa jiya na yi mafarkin mun yi aure ni da ita wai mun zo muku ziyara har kike ce mata ta zauna a hankali saboda cikin dake jikin ta har fah fushi na yi dan kin nuna son kai da yawa koh da na tashi sai naga ba ita bace wai mafarki naje yi yau kuma wai aka ce min za'a yi kamuuuuuuu" ya ɗan dakata daga nan ganin kowa kallon shi yake kamar wani sakarai sai ya daɗa hade fuska ya cigaba da maganar shi

"Kin cuce ni kin cuci amanar da na baki ta zuciya ta na so ki son da ban taɓa yiwa kaina ba duk wani mafarki da tunani na ke ce a cikin su rayuwar da na daɗe ina mafarkin shimfiɗa ta duk da kece koh daidai da rana ɗaya ban taɓa cire ki a zuciya ta ba duk saukar numfashi na kece amma kika rasa gane hakan kika kasa buɗe idanuwar ki ki gani har wai kika amince aka yaudare ni da sanin ki da saka hannun ki aka min yankan baya why why whyyyy""

Tsit hall ɗin ya dauka kowa da abin al'ajabin da ke yawo a zuciyar sa gefen amarya sun matukar firgita da jin waɗannan kalamai ace ango a ranar kwanakin bikin shi ya ƙi halara a wurin taro sannan ya shigo a bige yana maganganu marasa madafa da ma'ana kuma wai da wannan ake so a haɗa zuri'a na har abada inaa ba zai taɓa yiwuwa ba sai dai a fasa wannan aure dan suna ji suna gani ƴar su ta shiga irin wannan ahali kuma ta yu zaman din din din da mashayi dan haka ba zai saɓu ba..

Gefen iyayen ango da ƴan uwan shi kuwa abin kunya hakan ta kasance a gare su dan koh da a mafarki aka ce musu yaya Aqeeb zai kalli wani abu wai barasa za su musanta bare a ce har ya kai ga shan ta wannan abu ya zame musu abin kunya kunya babba kuwa dan duk kafafen yaɗa labarai na ɗaukar rahoto wannan abu da ban mamaki yake salma da ke digesting maganganun yayan nata ta kasa hakura ta yi saurin dumfaro shi da azama ta rike hannun shi

"Yaya me yasa me yasa a ranakun bikin ka ka nunawa duniya halin ka na ɓoye da bai kamata a gani ba why yaya i thought we were done with this issue why now baka tunanin ya aunty mufeedah zata ji a zuciyar ta ganin abin nan da ka ke displaying"??

Fisge hannun na shi yayi ya ce

"Allow me to pour out my mind she cheated she cheated kid sis" da karfi ya kai karshen maganar yana zub da hawaye zuwa lokacin amarya mufeedah ta fara fita a hayyacin ta dan tuntuni controlling kan ta take yi saboda son da take ma yaya Aqeeb ya ɗare wanda yake mata because ita ta nuna zakuwan ta akan ayi maganar auren su dan kar ya kufce mata ganin ta in aka yi auren komai zai lafa akan wannan ƙaddararen suna da yake kira mata kullum ranar Allah ta'ala ashe ruwan dafa kanta ta ɗebo wannan wace irin fitina ce gaskiya ba za ta iya ba in dai haka son da ya ke yiwa yarinyar nan ya kai toh ba zata iya zaman auren takura ba dan zai kasance kamar gangar jikin sa ta aura ba tare da ruhin shi ba saboda ruhin shi da nutsuwar sa na wun wancan yarinyar oh ya salam me yakamat ta yi kafin a sani kawai sai aka ji saukar wata ƙara tasss daga inda ya birkita ɗaukakin jama'an hall ɗin dan kuwa yaya Aqeeb ya amshi wannan zazzafar marin daga wun amaryar shi aunty mufeedah sai huci take tana zubar da hawaye ta daga yatsan ta tana nuna shi

"Aqeeb me ya rage in yi maka a duniyar nan da zai nuna maka cewa kaunar ka nake yi ba son ka ba me zan yi in janyo ra'ayin ka zuwa gare ni duk na wulaƙanta na hargitse na rasa hankali da tunani na duk saboda kai Aqeeb why are you torturing me why are you humiliating me da me ita waccan kucakar ta fini eyee? Kyau koh iya kwaliya,ilimi koh iya magana,dirin jiki koh akasin haka huh?? Answer me for crying out sake na gaji Aqeeb i can't i just can't saboda ko na aure ka mutuwata na aura dan kai ne *ajali* na a *ajalin so* da nake maka zai yi *ajalin ajali* *na* saboda haka na barka na barka ka ji daɗin duniyar ka kai da yarinyar da kake neman yin *ajalin* kanka a kai yarinyar da bata san kana yi wacce take kaunar ɗan uwan ka shima ya ke kaunar ta yarinyar da koh a yanzu aka ce ta zaɓe ka ba zata taɓa zaben naka ba wa zai auri matsala mashayi babu sai ni son da nake maka ya sa har laifin iyaye na na gani amma kai baka damu da ni ba it's ok na fahimce ka ni na nace maka shi yasa nake kwasar wulaƙanci amma na hakura da kai na yafe gomma in mutu da ƙaunar ka a zuciyata da in aure ka in yi rayuwar ƙunci da takaici dan har abada bazaka taɓa zare soyayyar yarinyar nan daga zuciyar ka ba"..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now