Page 33-34

568 46 2
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

3⃣3⃣➖3⃣4⃣

"Kai"?.
  Da mamaki Khadijah ta ce
"A'ish dama kin san shi ne"?

Gyara tsayuwar sa yayi  tare da zare tabarau da ke idanun sa wanda ya kasance baƙi ne wuluk kuma ta kusa rufe fuskar ta sa a firgice na karasa tashi tsaye dama a tsugune nake juyawa na yi toh ganin fuskar sai ta firgita ni ta saka ni tashi tsayi gabadaya

"My D ka san ta ne"?
  Gyatsine yayi yana kokarin share tambayar  Khadijar kara dakatar da shi ta yi da nanata tambayar dazu a lokacin nima nake kare mai kallo kamar ina son cire wani abu a fuskar ta shi sai na tsinkayo muryar sa cikin kwantar da murya sai maganar yayi tasiri instead in ji haushi sai abin ya bani mamaki

"No i don't know her me kuma"?ya karashe yana mai kafe ta da idanun sa masu kyawun kallo da ke rikita Khadijah a duk sanda ya kafa mata su ita kanta ta san son da take mai ya fi karfin wanda yake mata dan saboda tsananin so da kaunar da take mai har ji take tsab tana iya halaka ko kuma salwantar da rayuwar duk wata macen da ta kuskura ta raɓe shi da sunan son shi take ciki kuwa har da yar uwar ta ta jini kasancewar su su biyar ne a gidan su babbar wan su shine Dr Abubakar Alhassan babban likitan zuciya ne wato cardiologist a halin yanzu babu labarin shi tun wani lokacin da gobara ta kama a gidan shi shi da matar shi aka nema aka rasa har dai aka hakura aka bar wa Allah na biyun su mace ce hajiya aunty a yola take aure ƴaƴan ta uku biyun farkon ƴan biyu ne maza sai autar ta mai sunan maman su Khadijah wato halimatu sadiya ana kiran ta hajja sai na uku wace ita ce khadijah sai kannen ta biyu jabir da ke kasar cyprus yana karatu sai hajara mai sunan kakan su Khadijah.
Toh a haka take kaf kaf da rayuwar wannan my D din nata kamar ran ta shi kuma ganin irin haukacewa da take yi akan sa yasa yakan wahal da ita ta hanyar kyale ta na tsayin lokaci akan abin da bai kai ya kawo ba ita kuma son shi ya rigada ya gama yi mata illah bata iya jure fushin sa ko ta haura da kanta zata sauko saboda tsanani son da take mai ya sa ta manta da burin ta na zama cardiologist dan tun lokacin da yayan ta ya bace ta dau alkawarin mayar da gurbin shi a kasar nan ko da ba zata zama kamar shi ba exactly she wants to be known amma saboda shi sai ta yi deciding ta yi pleasing din shi ta hanyar karantar painting amma ba wai dan shine ra'ayin ta ba yana sane da duk moves din ta dan ya san ba ita ce mace ta farko da ke fadawa cikin tarkon son shi ba da zarar ya yi coming in contact da su yawancin wadanda suka yi conjunction tare ta hanyar fadawa a trap din sa ne dan shi ya yarda da kan sa fiye da yadda ake ganin sa..

"Nothing can i introduce you to each other"?
A karo na biyu ya kuma yamutsa fuska kamar wanda yayi doguwar tsayuwa

"Make it fast"
  Da murna ta juyo gare ni ni dake tsaya mamaki ya gama kaahe ni a tsayen

"This is Aisha my best friend a Egypt muka hadu jinin mu ya hadu sosai da ita a nan kusa take a zone 2 take"

Ta juyo zuwa ga ni tana murmushi mai bayyana sirrin zuciyar ta ta ce
  "A'ish this is my D my happiness my life my everything"
Ina jiran jin cigaban bayani sai ta yi shiru tana murmushi dan sunan nashi yana mata nauyi da wuyar faɗa dago idanun ta tayi ta kalle ni alama na mata da ina jin ta dada sunkuyar da kai ta yi kafin ta ce

"He is my hero Architect Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor and the best painter round the world".tana kaiwa nan ta dada fadada murmushin ta

Tabdijam goge zufar saman goshi na nayi wato dama a jiya da shi na hadu da yake dare ne sai ban gane shi ba yau kuma da muka hadu yana sanye da tabarau ban sami sararin kare mai kallo ba sai yanzu da ya zare tabaron but how comes dazu ban gane shi bahow can i be so stupid oh ya salam dama shine my D din Khadijah ban taba kawo hakan ba ko daidai da rana day thank goodness ban taba ce mai komai ba tun daga jiyan har zuwa yanzu zan ji dadin kama shi a sawwake wai shi dan duniya mu hadu sau biyu wai amma ya ce bai san ni ba lallai zan yi maganin shi.

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now