Page 15-16

579 45 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

1⃣5⃣➖1⃣6⃣

  Da saurin mu muka karasa shiga dakin da zuwan mu abu na farko da muka fara kokarin yi shi ne ja mata skirt din ta da muka fara kokuwar yi amma ya ki fita saboda wani shegen kiba ta kara a cikin wadannan watannin da muka yi a gida tunda babu abin yi makaranta ne kuma yanzu babu shi..ai da sauri ta ce mana

"Ku menene haka kuma ya kuke abu kamar wasu kananan yara ne koh baku san cewa kun girma ba ne ha'an" ta ida maganar tana wani cicin magani ita a dole an ce mata girma ya zo mata

Da mamaki muka tsaya cak kamar ruwa ya cinye mu ganin haka sai kuma ta ga kamar tayi overreacting sai ta riko hannun mu gabadaya tana kallon mu da dan damuwa ta fara cewa

"Kun ga umma ce ta ce min na girma saboda na fara ganin jinin haila na ba ciwo na ji ba ashe ta kuma ce min dole in kara kama kaina dan yanzu da da ba daya bane in nayi kuskuren barin wani namiji ya taba min koh da hijabi na ne sai na dau ciki tace min daga yanzu zan daina rashin hankalin da nake yi dole in rinka kama kai na in rage yawan wasa da wawan zama har fah ce min tayi yanzu zan fara ramukon azumi da fashin sallah toh fah abin da tace min kenan shi yasa ma kuka ga na hana ku ja min skirt dina amma in kun yi fushi ku yi hakuri  ta ce zata zo ta mana nasiha gabadayan mu anjima in zata kawo min pad din da zan saka dan kar in bata kayana da jini""

Jin haka ya sa duk muka saka mata dariya muna ce mata Ayyah yanzu shikenan babu ita babu wasa kuma ga fashin sallah da azumi ga shi in ta bari ta kuma hada kafada da maza shikenan ciki zata dauka tunda ita dai har ranar graduation din mu sai da tayi rigima da adebola saboda ya mata dariya wai graduation gown din ya mata kadan shine fah ta ce da wa Allah ya hada ta in ba shi ba sai da aka rabasu kafin a sami salama

Kuka ta saka mana sosai dan dama can aikin ta kenan abu kadan kuka har ta sa yaya aqeeb saka mata suna wato "Idon kuka" tana cikin yin kukan ne umma ta shigo tana mana fada akan me zai sa mu rinka tsorata ta bayan muma nan kusa muna gab da farawa ai da jin haka sai muka natsu muka daina mata dariya

Nasiha da fadakarwa sosai umma ta mana musamman saboda ni ta yi wannan fadakarwar saboda nice ban da uwan da zata koya min in lokacin koyawar ya iso falmata na da uwa haka salma so da dama takan kira mu kitchen in tana girki ta ce mu rinka kama wasu abubuwan mu yi koh kuma in zata yi aike zuwa kasuwa sai ta ce mu tafi tare da driver sai a bamu list din abubuwan da za'a siya mu mu siyo duk saboda ni take yin hakan dan tausaya min take yi ba na wasa ba ganin rainon mahaifina ne kawai sai yaya ibrahim wanda duk da hakan tana ganin bazai ishe ni gudanar da rayuwana ba ga shi ina da kanwa mace duk wani abin da zata yi nan gaba a rayuwar ta zai kasance rainon da na mata  ne  toh idan nima ban sami isashiyar rainon ba ta yaya har zan koyawa kanwata wadannan dalilan ya sa ta kan zage ta koya mana abubuwa sosai a fannin mama wato maman su falmata ma ba'a bar ta a baya ba in har muna sashen su toh bata barin mu haka kawai dan jajjage yankan albasa goge wurin d aka bata yayin da ake girki da dai sauran kayan aiki da ya shafi ƴa mace a rayuwar ta saboda itama kallon tausayi take min kuma tana jana a jiki hakan ya sa bana shiga kadaici ga hasinah da ta zamewa ummi kamar ƴar uwarta ta jini komai za'a siya mata sai ta ce ina na farida dan ita da faridar take kiranta wai ya fi dadi ba kasafai take kiran ta da ummin ba sai dai in ta yi laifi za'a hukuntata sai ta fara cewa ummi ki taimake ni umma zata min duka toh hakan da take yi sai ya rinka sanyaya jikin umma ganin in ta dake ta toh lallai ummi zata na mata kallon marar imani shi yasa da zaran hasina ta yi laifi in ta gudo zuwa gun ummi toh umma bata iya hukuntata sai dai in ummin bata nan toh koh shi yaya aqeeb din bai isa ya hana a daketa ba

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now