Page 43-44

553 45 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

4⃣3⃣➖4⃣4⃣


"Enough of all this stupid drama of yours stop pretending that you don't know what is happening"a tsawace ta gama maganar kamar zata dake ni na girgiza dan ban san ina maganar nata ya dosa ba zan yi magana ta hana ni

"Please Aisha kar ki maida ni karamar yarinya mana tun yaushe nake maki gargaɗin kar ki kuskura wani abu ya shiga tsakanin ki da Abdulrahman? eyye? baki da bakin magana right? na dauki amana da aminci na baki ina shiru ba dan komai bane sai dan ina ganin aiki ne ke saka ku kusanci da juna amma ba haka bane if not in har magana zakiyi da shi me yasa baki yi mai tun a cikin conference room din ba sai da aka fito zaki wani kira shi gefe kina son yi mai magana ba fa ki taba neman izini na ba in zaki yi magana da shi kai tsaye kike mai magana gaban ki gadi ohhh ke ga boas lady koh? bari ki ji in gaya miki wallahi bilahilazim i won't spare you in na ji ƙishin ƙishin wai son sa kike yi kar ma ki fara ina ja maki kunne dan babu wacce ta san Abdulrahman sama da ni sai ni ni kadai dan haka da ni ya dace ba ke ba ko wasu banzayen marasa asali ba mtsww"tana kaiwa nan ta biga wata uwar ashar tare da tsaki ta yi gaba abin ta leaving me in deep shame and restlessness of mind kuka zan yi ne da ƙazafin da dija ta min kokuma kuka zan yi da abin kunyar da ta raba min gaban ma'aikata na masu ganin daraja da ƙimata oh ya Allah ka taimake ni ban san ya zan daga kafa na in kara wani step ba balle in masu magana sai na ji muryar shi cikin fushi da tsantsar bacin rai yana masu tsawa

"And what the heck are you standing there watching if you don't leave before a second you all will be fired right this moment shameless beasts"

Ai kafin ya furta wata kalma suk sun yi clearing wurin dan haka na sami damar karasawa zuwa office dina da sauri na zauna a kan kujera na yi kokaein daurewa da danne zuciyata amm bazan iya ba kazafi duk kankantar ta cin rai ne da ita dan haka hawayen da ke tseren fitowa daga ma'adanar sa haka ya balle kofa ya fara bulbulowa kamar ba zai daina ba yana shigowa karfin hawayen na kara daɗuwa ƙala bai ce min ba sai ya dau cup ya tsiyaya coffee ya zauna yana shan abin shi yana kallo na haka na rinka risgar kuka na kamar an ce min na rasa Abbu sai da ya gama shan coffeen tas sannan ya mike tsaye yana ce min

"Ms Murad am leaving i have so many important things to do before i leave for my trip dan haka in kin gama kukar sai ki tafi ki bata haƙuri for making a step to steal her fiance humm"?

Yana furta wannan kalma ban san inda hawayen suka bi ba amma nidai na san na neme su na rasa sai na ji wani irin ƙuna a rai na yanzu yanzu a gama cin zarafi na akan shi akan abin da ban ji ba ban gani ba amma ya rasa abin ce min sai in je in bata hakuri for making a step to snatch him wani irin raini da wulakanci ne wannan at least he should respect me ko dan nayi kuka a gaban shi ne yasa yake gayamin abin da ranshi ya so cikin zafin rai nima na tashi tsaye

"Excuse me Mr Abdulsalaam baka da hurumin gaya min magana kai tsaye dan gida na kazo ba ni na taho gidan ka ba kana gani a gaban ma'aikata na aka tozarta ni akan abin da ban ji ba ban gani ba sannan ka zo kana kokarin kara bata min rai da kalaman ka da wanne zan ji"?

Daga kafada yayi irin oho abin ya bani haushi dan haka na ce mai

"please you can go because seeing you alone increase my anger" murmushin gayya ya min ya juya zai fita sai ya dakata

"Ms Murad you don't cry over an issues like this if you begin now then nan gaba me zaki yi in an maki wanda ya fi wannan hala kashe kanki zaki yi saboda public shame" kaiwa nan yayi gaba abin shi

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now