Page 65-66

699 46 2
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

'''friendy surayyahms shafin nan naki ne Allah ya bar ƙauna ya ƙara mana kyakyawar alaƙa da fahimta a tsakanin mu u are indeed a good friend luv u dear'''

*INA MIƘA GAISUWA TA GARE KU MASOYAN SOYAYYA MAI GARƊI A DUK INDA KUKE GUDUNMAWAR KU YANA DA TASIRI A GARE NI ALLAH YA SAKA MAKU DA ALHERI YADDA KUKE BULBULA MIN ADDU'OIN ALKHAIRI KUMA ALLAH YA BAKU ABIN DA KUKE NEMA NA ALHERI ❤*

*_Ina taya ki murnar kammala littafin ki Asmeenat Xeeyan Allah ya baki ladan darussan da kika kawo a littafin_*
6⃣5⃣➖6⃣6⃣

Ji na yi an ja ni sai na kai duba na ga mai jan ashe ummi ce sai surutu take ta yi wai ana nema na na ɓace bin ta na yi a baya har muka karasa zuwa cikin harabar gidan mu inda ake gudanar da shirin gabaɗaya ƴanuwa da family friends kamar dai families  ɗin su aminaina biyu duk sun zo kuma sun min karamci anokanan aiki mata sun zo tunda taron na mata ne ina jin wani iri wani iri har aka gama taron dariyar yaƙe kawai na ke yi da ciwon kai na kwanta ranar dan sai da na saka ma aunty mama kuka ina cewa ita ta ja min gashi ana min auren dole ga khadijah sai kallon azzaluma take min ko bi ta kaina bata yi ba ta miƙa min wani pill na sha bayan ta sa an kawo min abinci wayoyi na ta kashe su duka ta rufe kofar da lock key ta waje dan in sami isashen barci babu daɗewa barcin ya ɗauke ni ban tashi ba sai wuraren 10am dan bana sallah shi yasa ta bani maganin na sha da na farka na yi wanka na koma na kwanta dan jiri jiri nake ji effect ɗin maganin bai gama sake ni ba kwanciyar ba dadewa wani barcin ya ɗauke ni sai 12 na tashi a lokacin na ji daidai na yi kokarin fita na ji kofar a rufe abin mamaki wayoyi na duk banu su salin alin na koma na zauna ina tunanin irin zaman auren da zamu yi nu da shi gashi dai muna son junan mu har mafarkin mallakar juna muke amma kuma babu kwanciyar hankali intruding factors su mana yawa ga koshi ga kwanan yunwa shi ne wannan al'amari ina tsaka da tunanin naji kici kicin buɗe kofa na daga kai ɗaya daga cikin matan nan ne masu min gyaran jiki ɗaure fuska na yi ganin shigowar ta dan zuwan ta bai cika kasancewar da alheri ba duk sadda za ta shigo da jiƙe jiƙe take shigowa kamar wata mai maganin gargajiya abin takaici yakr bani aunty mama ce ta bar mata wuƙa da nama sai ta ke son wuce gona da iri dan ta mayar da ɗure ɗuren kamar ruwan sha sai dai bata shigo ba daga tsuguna a kan wannan rushin sai shanye wannan sai tsotse wannan azaba kawai take gana min wai shi gyara gashi in ta fara murje min jiki kamar ta ga dutse ban yarda ta kai kirji na sai in ce ta tafi zan yi ba a son ran ta take incomplete work ɗin da take min ba kawai ta san ni ɗin ba yarinya ba ce bare ta min dole ta san zan yi ɗin aiko tana tafiya zan yi sama sama in rufe ƙofar minti goma mai kyau ban kaiwa nake zuwa in wanke in ta dawo in ce na yi saidai ta yi shiru toh a yanzu ɗin ma abinci ta kawo min ganin bana walwala ya sa ta ce
"Hajiya mamanku ta ce a kawo maki abincin ta ce tun jiya rabon ki da abinci"da toh na amsa mata ta tafi ina murnar bata kawo min surkullen da ta saba ba na buɗe abinci shar a ido na yi serving kai na na fara kaiwa baki ai da sauri na furzo shi waje na buga wata tsaki ina masifa ai dama na sani wannan mata babu alheri a zuwan ta wato ta san na gaji da shaye shayen magungunan da take kawo min shi ne ta saka min a abinci wannan wace irin jarababbiyar mata ce na buga wata tsaƙin na ɗau abincin a tray da ta kawo na yo ƙasa da shi sai hayaniya ake ta yi a gidan na wuce ɗakin aunty mama da abinci na ajiye mata a gaban ta

"Gashi nan ke kika saka matar nan ta raina ni ko wani lokaci cikin magunguna sai ka ce ni na ce mata ina laulayin ciwo da ko wani lokaci ban da shikir a gidan nan abinci magani ruwa magani da tana da hali ma barcin da nake samin yi magani zata bi ni da shi wannan wani irin takura ne ni fah na gaji"na ida ina kwafa jan hannu na tayi ta ce toh zauna baby na zauna kira ta yi aka kawo min wani abincin tsoron cin abincin nake yi ta ce in ci ba komai na kai spoon ɗaya na ji kamar ba komai sai na sake jiki na ci sosai har na yi rabi na ce na koshi ta miƙa min ruwa na sha ina ajiye cup din na ji ɗaci kamar na sha maɗaci sai na fara ƙaƙarin amai
"In kika fara zaki gamu da ni dan gidan ku"yamutsa fuska na yi na saka fuskar tausayi irin ana zalinta na din nan

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now