Page 9-10

658 45 0
                                    

SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

9⃣➖1⃣0⃣

_Asalin Labarin_

*ABADAM MAIDUGURI BORNO STATE*

  Shine ainihin sunan garin mu da yankin mu mai suna Abadam

A chan aka haife ni aka kuma haifi kanwata mai suna farida wanda muke kiranta da ummi saboda sunan mahaifiyar mu ne da ita

A tarihin gidan mu mahaifin mu ya kasance dan kasuwa ne wanda kasuwancin nasa bai tsaya a nan gida nigeria ba yakan tafi kasashe saboda saro kayayaki ya kawo nan kasan ya sayar ma yan kasuwa

Duk da haka arzikin shi bai taba saka shi yayi sakaci da kula da taebiyar mu ba a matsayin shi na uba mai rauni sakamakon rasa ummar mu da yayi tun lokacin da ta haifi farida.

Ina da shekaru biyar a duniya aka haifi farida rashin uwa yasa na zame mata komai na rayuwar ta ni da mahaifin mu

A wannan yanayin kula ta taso har lokacin da ta kai shekaru uku a duniya wanda ni kuma nake da shekaru takwas

A daidai wannan lokacin ne kuma iftila'i ya sauko mana saboda mahaifin mu ya yi tafiya zuwa Cotonou saro kaya ya bar mu a gida ni da Ummi tare da wata kanwar mahaifiyar mu da ta zo tun daga yobe domin kuma tuntubar mahaifin mu da maganar ya bar ta ta tafi da mu amma yaki sai ma yace mata ga amanar mu nan ya bar mata har ya dawo daga tafiyar kasuwancin sa..

Tafiyar shi da kwana daya fitina ta taso mu gaba a inda aka shigo gidan mu aka dauke komai sannan aka yi wa kanwar mahaifiyar mu fyade kafin su mata kisan gilla dan a zaton su ita din mahaifiyar mu ce saboda tsananin  kamanin da muke yi da ita da kuma yanda suka ga ta kasa ta tsare akan bata yarda a taba mu ba sai suka mata wannan rashin imanin

A dai dai lokacin ne kuma yan fashion suka tare mahaifin mu a hanyar sa ta dawowa daga Cotonou suka kwashe kayan suka ma yan motar duka duka ba na wasa ba har sai da wasu numfashin su yayi kokarin daukewa ciki har da mahaifin mu

Bayan sun gudu ne sai ga motocin yan sanda da suka zo zagaye suka tarar da ta'asar da aka yi a wurin toh su suka taimaki mutanin bayan sun yi bincike suka gano yan fashi ne suka yi aika aikar

Koh da aka gwada tambayar mahaifin mu addireshin gidan shi har ma da garin shi bai iya basu amsa ba saboda yanayin da yake ciki sai da aka share kwanaki uku kafin a samu yayi magana har ya bada shaidar abin da ya sani sannan aka dawo da shi gida

Mu kuma a chan gida bayan yan bindigar sun fita ne na shigo kwala kirar jama'a da su kawo mana agaji sai a lokacin mutani suka sami damar fitowa daga gidajen su saboda suma boyewa suka yi jama'a sosai suka shigo mana a nan suka san halin da muke ciki bayan sun tabbatar da cewa kanwar mahaifiyar mu ta rasu

Kuka sosai muka yi saboda yanayi na yarinta bamu gama sanin komai ba ilah abin da muka gane ma idanun mu

A washegarin da aka dawo da mahaifin mu ne ya tarar da wannan abin al'ajabi gashi babu kowa da take da shi a yobe face dan ta mai suna ibraheem dan shekaru goma shabiyu toh shima yana makarantar kwana na sakandire mijin ta ya dade da rasuwa kakannin mu ma bamu sansu ba saboda sun bar duniyar tun kafin a haife mu

Rashin babu wanda za'a kira a chan ya sa aka mata wanka aka kaita

Da jimami aka samu mahaifin mu ana mishi ta'aziyar rasuwar toh a nan ake sanin cewa ashe ga abin da ya faru da shi abubuwan da yawa suke

Jaje sukai masa kafin su tattafi mu da muka ga mahaifin mu ni da ummi duk sai muka je muka fada a jikin shi ni kuka ummi murnar taga baban ta saboda ya rigada ya saba mana da zama kusa da shi hakan ne ya sa sabo mai karfi ta shiga tsakanin mu da mahaifin mu

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now