Page 57-58

653 44 3
                                    

🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

'''This page is for you my wattpad fans thank u for the love i really appreciate it'''

5⃣7⃣➖5⃣8⃣

Juyowa na yi kamar mai jin tsoron haɗuwa da kumurci kaɗan kaɗan na karasa juyowan ina jiran saukar kwandon faɗa daga gare shi sai na ji yayi shiru runtse idanuna na yi a tunami na ko ma wari na zai yi sai na ji shiru da sauri na buɗe idanun na zuba mai a yadda ya dan daka min tsawa da na shigo na yi tsammanin zai min wani abin sai na ga akasin hakan instead sai ya kwantar da muryar shi ya ce

"Mama na daga ina kika fito tun dazu ake kiran layin ki ba ki dagawa an kira ƴar uwar ki ta ce bakya gidan ta maman ku ta yi ta kiran layin ƙawayen ki sun ce basu san inda kika shiga ba secretary din ki ta ce baki da appointment da kowa dan haka ba ki je office ba ina kika tafi"?? Tsuru tsuru na yi da ido dan na rasa amsar bashi in yi ƙarya ne ko dai in faɗa mai gaskiyar lamarin tunda tsakanina da Abbu babu boyewa sai na gyara tsayuwa zan fara jero zance karaf aunty mama ta fito tana magana

"A'ah baby har kin dawo daga meeting ɗin kenan na na ɗauka kin ce min sai 7pm zaku gama kun taƙaita kenan"? Da wani irin non verbal eye gesture ta ida maganar wanda ya saka ni gane cewa taimako na tayi daga hell ɗin da na kusa shiga a wun Abbu sai na yi saurin amsa mata

"Eh kin ga ai ba ni kadai ba ce musulma lokacin sallah ya gabato shine muka ce su takaita in ya so gobe sai mu karasa kawai shiyasa kika ga na dawo da wuri"gaba na sai bugun tara tara yake yi dan ƙarya ba hali na bane a ranar da na yi shi sai nake ji kamar Abbu zai dago mu sai na ji ya ce

"Amma mama na an yi shirmammiya shine kika kasa sanar da ni emergency meeting kika tafi attending kika bar ni ina ta tambayar ki"? Toh how was the meeting da fatan komai ya tafi daidai? Saurin amsa mai na yi ji Abbu da wata magana wai ban mai bayani ba bayan bai bar min breathing space ba ya rinƙa min tambaya
_(jan hankali dan Allah kar budurwar da ta yi gangancin yin abin da Aisha ta yi na bin saurayi su haɗu a wani wurin daban sannan ta dawo gida ta yiwa iyayen ta karyar wani abu mai muhimmanci ne ya tsare ta har ta sami goyon bayan matar mahaifin ta itama ta ce eh haka ne yin hakan bai da ce ba a zamanin nan ba'a cika samin matan uba masu hallaya irin ta aunty mama ba sai ɗaiɗaiku dan haka ita a nata nufin ta fitar da Aisha ne daga zargin da mahaifin ta ke son yi mata saboda ta san hallayar Aishan kuma duk abubuwan da ke faruwa da Aishan ta sani kuma ta masu kyakyawar fahimta dan tana da ilimi da hikima kuma ta san Aisha ba zata taɓa aikata mummunar abu ba shi yasa take kare ta bayan haka wallahi wasu matan uban ba za su taɓa kare ki ba sai dai su ƙara wa barkono raɗaɗi wasu kuma zasu karen amma ba dan tsakani da Allah ba dan in nasu ƴaƴan ne da suka haifa ba za su taɓa yarda hakan ya faru ba dan haka wannan scene ɗin is necessary to the story shi yasa na saka ƙalubalen mu mata kar ki taba daukar wasu abubuwan littatafai ki ce suna faruwa a reality kice zaki yi practicing if it worked for the star a littafin it might not work oit for you dan haka nake jan hankalin ku da ku guji biyewa makauniyar soyayyar da zai saka ku bin ɗa namiji a zaman da ya kasance mace da namiji ne waɗanda ba muharramai ba ne na ukun su shaiɗan ne koh a fannin su Aishan haka ne amma Allah ya kare babu abin da ya shiga tsakanin su amma suna jin bakon yanayi wanda sai da suka yaƙi zukatan su kafin su rabu kenan in su sun iya yaƙi da zukatan su ku fah? Ba lalle bane ku iya yakar zuciyar ku da abin da yake kwaɗaita maku dan haka ni Siyama Ibraheem ina mai gargaɗin ku da kar ku yo practicing abin da Aisha ta yi da waɗanda zata yi nan gaba kafin su zama muharraman juna ita da Abdulrahman dan kar wata ta zo ta yi kuka da ni ta ce ai na saka a littafi na my hands are clean and my mind is pure Allah ya sa mu dace)_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now