Page 31-32

551 47 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

*_Wannan shafi naku ne soyayya mai garɗi fans da siyama ibraheem fans page ina matukar ji da ku fiye da yadda kuke ji da ni i heart you all_*

3⃣1⃣➖3⃣2⃣

7:30 pm na dawo gida ruwan sama yayi tsanani sosai ina shiga na yi parking motar na fito kamar dole na shige ciki zaune na iske su Abbu ummi da yaya Ibrahim coffee suke sha ummi da yaya Ibrahim na zaune a ƙasa opposite direction ɗin juna danna waya suke yi suna ta faman zuba murmushi in sun yi sai su kalli juna su cigaba da gani chatting suke yi Abbu kuwa news paper yake karantawa daga murya na yi na ce

"Assalamu alaikum"

A ɗan firgice ummi ta ɗago ta amsa kamar wata marar gaskiya na maka mata harara Abbu ya ce min tun ɗazu yake ta kokarin reaching ɗi na amma wayar ta ki shiga na ce mai network ce tambaya ta yayi ya na baro su na gaya mai ai gidan falmata kawai na je dare yayi ban sami zuwa gidan salma ba sai dai koh jibi jin sunana falmata ya sa yaya Ibrahim dakatawa daga chatting ɗin da yake yi da ummi itama ganin babu reply din tambayar da ta mai sai ta dago ta kalle shi bai lura ba sai kawai ta danna kira ai ko ƙiii sai ga ƙarar special tune ɗin da ya saka mata firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga yana kokarin saka wayar a silent me zan yi in ba dariya ba Abbu ma murmusawa yayi kawai dan ya ga ummi ta gama ɓata yaya Ibrahim da rashin kunyar ta tashi na yi na  ce bari in je in chanza kaya na Abbu ne ya kira ni

"Mama na in kin gama ki zo ki same ni a garden ina da maganar da nake so mu yi" da toh na amsa mai na haye sama zuwa ɗakina da ke kallon na ummi ban wani ɗau doguwar lokaci ba na fito cikin night gown ɗi na doguwa har kasa na dora hijabi na sauko na nufi garden direct

"Mama na har kin gama" da eh na amsa mai na nemi wurin zama na zauna

"Ga shi ki gani"ya miko min newspaper da ke hannun shi karba na yi na kai duba na izuwa news paper ɗin
*ABDULRAHMAN ABDULSALAAM ABDUL SHAKOOR*

Shine sunan da na gani a gefe ƙadan daga gefen painting din duba ɗayan shafin na yi na ga full picture din shi a tsaye ya cika pagen sanye yake cikin grey suit mai haɗe da ta cikin ta ya saka black necktie yadda suit ɗin ta zauna mai ba abin misali ba ne ƙafar shi sanye cikin curve shoe baƙaƙe idanun shi sanye da ƴar ƙaramar transparent glasses dan har kwayar idanun shi ana iya hangowa agogon hannun shi kuwa wata rolex ce baƙa suman kam sa ya gyaru gyara mai kyau bata kazanta ba dan MashaAllah suman ya asku irin ta zamani ga kyawun kallo dan kamar a kannanaɗe yake sai kyali yake yi sajen shi mai kyau bai ajiye gemu ba sai ya yi kyau idanun nan kamar ta mage dara dara sai dai yanayin yadda yayi tsayuwar hoton sai bai buɗe idanun na agi sosai ba murmushin ma kadan ya yi ta a lissafi na ba zai wuce 33-35 years ba na shagala ina anaysis ban karanta abin da aka bani in karanta ba bugun teburin tsakiyar kujerun na ji ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi har kwarewa na yi Abbu ya miƙa min kofin ruwa na karba na kurba kadan na ajiye ina goge fuskata shi dai Abbu ido ya zuba min kar dai a ce abin da ake fada game da yaron nan akan mata ya zamo gaskiya har ma yake neman faruwa da tashi ƴar..

"Abbu me ka ce in yi da jaridar ma" na yi tambayar ina mai kokarin daidaita natsuwata dan kar Abbu ya ga kamar am not serious

"Hmm mamana baki na yi dan ki karanta article ɗin" a ɗan kunyace na mayar da hankali na kan jaridar tafihin asalin tushen painting companyn din ne da shekarar da aka kafa ta da ceo da suka gabata har izuwa yanzu da wannan mutumin ne akai irin painting din da suke yi collaborative painting companies da ke harka tare da wannan company ɗin karshe duba sunan companyn na yi
*"D'AA FLAME PAINTING COMPANY"*

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now