Part 49-50

609 44 1
                                    

🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

4⃣9⃣➖5⃣0⃣

Tafi aka saka sai yi take yi tana mana kallon wulaƙanci kafin ta dakata ta tsaya tana ƙare mana kallo daga ni har shi shiru muka yi ni nafi kaɗuwa akan shi dan in ma ya kadun ma bai nuna ba unlike me da na kasa boyewa

Wannan matar ba kowa bace face khadijah wacce ta shigo mana a bazata ba tare da sanin mu ba sai da ta mana kallo tas ta zauna a kujerar ɗakin muka bi ta da kallo kafin ta ba ma wanda suke taren izinin shigowa shigowan yayi yana kallon mu irin zaku gane kuren ku ɗin nan shima zaman yayi a karo na biyu muka kalle su su biyun

"Hmmm Ms Murad boss lady mai kamfanin "M Motives da elegant Arch Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor the owner of "D'AA flame paintings most well known and popularly known as the number one best painter"tana isowa nan sai ta yi shiru na ƴan seconds sannan ta cigaba

"Kun ban mamaki wato hero ina nan ina mana yaƙi akan soyayyar mu amma kana nan kana shagalin ka da wannan?humm?hero ina chan ina ƙoƙarin ganin an yi fixing mana ranar auren mu da kai amma kai ko a jikin ka? na tsiyace na cire kunya ta na ƴa mace na zage na yi faɗa da aminiyata akan ka amma kai kai hero kaine ke backing ɗin ta ka gama nuna mata cewa dama chan nike ɗawainiya da son ka ni ke burin auren ka amma kai ba son hakan kake ba"ta ɗan ja fasali kafin ta ɗora

"Na san ni ke son ka amma kana ganin na chanchanci wannan wulaƙanci daga gare ka? eyye?sai ta saka kuka"

"Tun da nake da kai ban taba haɗa soyayyar ka da na kowa ba tun ina kankamuwa ta na tasho da son ka da kaunar ka a jinin jiki na amma haka ka zaɓi yi min?dan ni ke son ka?a da in na tambaye ka ko baka iya soyayya bane sai ka nuna min eh baka iya ba dan baka taba yi ba sai ni ce da ke mace na koma nuna maka soyayya a fili ko ba haka aka yi ba?yanzu da kake kokarin nunawa wata banzar so ai gashi nan ka san yadda ake ecpressing so a wurin wannan abin"..

Numfasawa tayi ta ɗora da
"Toh albishirin ki Aisha Murad daga ke har shi baku gaba na saboda baki isa in yi kishi da ke ba tunda kika dauke mar hankali a kaina toh na bar maki shi but ki tuna saƙon da na turo maki akan ki tanadi kayan yaƙi ki jira dawowa ta gashi na dawo unexpectedly yanzu kuma za mu fara dan na miki rantsuwa da mahallici na ke da kwanciyar hankali har abada bar ganin cewa na bar maki shi ki ɗauka wai ko bana son shi ne a'a na bar maki shi ne dan na fi ƙarfin haɗa abu da ke amma am telling you today ki rubuta ki ajiye tashin hankali ya buɗe babi kenan a rayuwar ki Aisha Murad"ta na kawowa nan ta tashi tsaye ta kalle shi ta ce

"And for you" tana mai kallon yaya Aqeeb da suka shigo tare

"Ga ta nan in zaka mayar da hankalin ka kan matar ka ka mayar dan ka gane ma idanun ka irin sheƙe ayar da take yi da sunan aiki kai bata bar ka ka zauna lafiya ba sannan bata bar ka ka aure ta ba tana wahal da kai amma kana chan kana azabtar da kan ka bayan kana da matar ka kyakyawa ƴar asali ba wasu ba da ba'a san asalin su ba mtsw" da tsaki ta karasa maganar tana mai dalla mana harara for the second time da na ji zafin yi min gorin rashin asalin da ake yi da farko aunty mufeedah ta min a yau kuma khadijah why me? ban san cewa na fara hawaye ba sai da na ji saukar hawayen a ƙirji na na kai duba na gun na ga hawaye na kai hannu na kan kumatu na na ji ruwa ruwa alamun hawayen ne ya fito min ba tare da na shirya ba a zuciye na goge fuskata na matso kusa da ita na ɗaga hannu na na nuna ta da yatsa na manuniya

"Khadijah ya ishe ki haka ba zan dau wulaƙancin ki ba for the second time ki bini har building ɗina ki gaya min magana son ran ki sannan kiyi tunanin zan bar ki ki tafi haka nan kin yi karya dan haka ki bude kunnuwar ki da kyau ki ji ni Abdulrahman is nothing to me because mazan da suka fishi kyau da aji ban saurare su ba ballantana shi shi da yake saura sauran ma sauran ki mutumin da na tsinta a hanya ba a gida na ba wanda ban san asalin shi ba ban san ko shi ɗin waye ba kike tsammanin zai yi tormenting ɗi na da wani abu da yake da shi?kina ganin ke ɗin kin cika mace ne da har zaki tsaya kina exchangimg words da ni a kan ɗa namiji? kenan baki cika mace ba dan ni ɗin nan da kika gani ban taɓa son namiji ba sai dai ni ya so ni kuma ai kin ga hakan da idon ki sau uku yaya kabeer shi ya ke mutuwar so na shima wannan ɗin na nuna yaya Aqeeb shima shi ke so na ban ma san yana yi ba jabeer ke shaida ce ban taɓa nuna mai so ba shi yayi ta bulaguron sa sai a kan wannan na juya na kalle shi ido cikin ido na cigaba wanda ban taɓa daukar lafuzan bakin shi da ƙima ba shi kike tunanin ni Aisha Murad zan tsaya ina chanza kalamai akan shi bai taka waɗannan matakai ko ba dan a second hand nake kallon shi mutumin da ke mu'ammala da second hand shima ai second hand ɗin ne"buɗe idanuwan shi yayi cikin nawa nima na cigaba da kallon cikin idon na shi for a moment kafin in cire idon na wa na mayar da shi kan yaya Aqeeb da ke tsaye kamar gunki

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now