Page 5

843 60 5
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

5⃣

 
    _"Dr me zai sa baza ka rubuta resignation letter ba tunda kaga kana da asibitin kanka da kake running which is under your control kana da NGO's da kake programs sosai haka nan kana da isashen kudin da zai ishe ka yin rayuwar ka har ma da yet to come family din ka..., ka ga idan har ka rubuta resignation letter din nan you can be able to stay away from those heartless men at same time fasten ur visa saboda ku yi ku bar kasar nan kamar yanda maman su khadi'atu ta gaya maka ka ga idan ka yi hakan babu wanda zai fuskanci wani abin hakazalika babu wanda zai zarge ka da cewa harda saka hannun ka a abduction case din nan balantana a yi ceasing license din ka akan cewa kayi wrong practice wa patient_
  _A yanda na lura your reputation can be ruined easily in har ka tsalake maganar su kokuma kayi yunkurin fallasa su kamar yanda suka gaya maka kuma gaskiya tsakani da Allah ba yanda za'a yi mu cigaba da ajiye wannan yarinyar a wurin nan ba tare da hospital authority din nan sun sani ba kai kan ka kasan ana sanin wannan issue din kashin mu ya bushe daga kai har ni da ban san da maganar ba sai yanzu hakazalika idan ka yi la'akari da suffar yarinyar nan zakaga cewa ba daga gidan wahala ta fito kuma babu sanin ahalin ta akan bacewar ta su kansu na san ba'a barsu haka nan ba if not da an fara neman ta tun jiyan duba da sunan familyn da take amfani da shi.._

  _Saboda haka likita ni dai in zaka bi nawa shawaran ka yi abin da na ce maka ni kaina zan fara annual leave di na in d next 5 days saboda sa'adatu zata dawo next week(deputy metron) kai kan ka kasan halin ta sarai bazata taba amincewa da wannan labarin naka na boge ba hasalima tana ji kara zata kai zuwa authority in ko haka ya faru mai kake tsammanin zai biyo baya??_

   _"Asirin da kake kokarin rufewa zai bayyana rayuwar family din ka zai kasance a tangarda kafin jami'an bincike su shigo lamarin killa ma sun cutar da ku before then"_

_Kuma kana sanne da cewa tana da ciki we can't commit such a hug crime by seducing her with toxins a jikin ta gaskiya am not a murderer so the earlier the better likita ni dai iya abin da zan iya gaya maka kenan a matsayi na na ƴar uwar ka a musulunci and not as a professional colleague_

_Ka yi tunani da kyau likita idan aka ce ƴar cikin ka ne hakan ya faru da ita ya zaka ji ya zaka yi reacting_




Tsawon mintuna bai iya min magana ba karshe dai tashi yayi yana share zufan da ke ta tsatsafo mai ya ce min zai yi tunani a kai

   Har ya kai kofar fita daga office din na dakatar da shi na ce

  "Likita da ka shigo wa ya bude maka gate kuma wa ka hadu da shi a harabar ajiye motoci"??

  Sai ya dakata ya juyo da dan mamaki yana duba na nace mishi "yes i need to know saboda mu rufe musu bakin su if not za'a sami matsala"

Ya kuma sharce zufan kan fuskar sa ya ce min

"Anthony ne ya bude min gate while na hadu da baballe a parking lot"

Na girgiza mai kai ina mai kafe shi da ido na
"And the diagnosis"???

  Daga kan shi sama yayi kafin ya bani amsa da

"They are all fake diagnosis Hajiya lafiya kalau aka kawota hasalima kamar daga bacci suka dauko ta"
Ya ida maganar yana juya fuskar shi zuwa gefe saboda sun riga da sun rikiɗe zuwa jajjaye "sai kuma ya ban tausayi
Wato idan kaddara zata sauko ma mutum haka Allah ke lamarin sa dole sai ya saukko maka just last week yake zagaye asibitin nan da family din shi kafin ƴaƴan shi su koma inda suke karatu amma sai gashi wai wannan mummunar kaddarar ta sauko mishi ba tareda ya shirya ba.. Al'amarin ubangiji kenan""

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now