Page 37-38

568 44 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

3⃣7⃣➖3⃣8⃣

  NOTIFICATION!! NOTIFICATION!! NOTIFICATION!!

_Dear readers ku natsu a hankali ku karanta tarihin Abdulrahman da zuriar sa kar ku yi karatun jarida dan in kun yi hakan ba lallai bane ku fahimci labarin  ku bi a hankali labarin ba mai wuyar ganewa bane dan wasu zasu ce sun sami confusion_

  *_Asalin labarin Abdulrahman Abdulsalaam_*

Cikakken sunan sa Abdulrahman ɗa ga Architect Abdulsalaam jika ga Alhaji Architect Abdulshakoor

Asalin su ƴan garin Adamawa ne cikin membila tun daga kakanni da iyayen su ƴan fulanin membila ne

A cikin zuri'ar su Alhaji Abdulshakoor shi ne ya fita zakka dan tun yarintar sa yake da wani boyayyen hazaka wanda ba kowa ya san da hakan ba sai mahaifin shi da ya gano hakan wato mallam Abdulrahman..

Su shida ne a cikin su  Asiya ita ce babba sai Abdulhakam shine na biyu Abdulrashid shine na uku, Abdulgaffar na huɗu, Abdulshakoor ne na biyar sai Abdulsalaam shine na shida wanda Architect Abdulsalaam ya ci sunan sa

Duk cikin waɗannan ƴaƴa na na mallam Abdulrahman ƴaƴan sa biyu sun fita zakka wato Abdulgaffar da Abdulrashid sun kasance ƴaƴa masu ba wa mahaifin su damuwa da janyo magana a cikin gari kasancewar mallam Abdulrahman mutum ne mai wadata da girma a garin dan haka ko sun janyo maganar akan share su dan mahaifin su mutumin kirki ne dan a cikin zuri'a ba'a rasa bata gari in ba haka ba duk sauran ƴaƴan sa na mayar da hankali akan tarbiyar da iyayen su ke ba su.

  Ya gwalgwal wato Fatima shime sunan mahaifiyar ta su macr ce mai hikima da iya tafiyar da duniya a duk yadda ta zo mata dan haka duk son da take yi wa ɗan ta Abdulshakoor bata nunawa gudun kar ƴan uwan sa su janyo rigima a tsakanin su wanda hakan zai bata ƴanuwantakar su amma har da haka Abdulgaffar da ya kasance rigimamme sai ya nemi janyo kace na ce tsakanin sa da Abdulrahman shi dai bai biye mai a haka suka girma da kishin sa wato Abdulgaffar da Abdulrashid yayin da ita babbar yar su Aisha ta ke kokarin haɗa kawunan kannen nata auren haɗi aka mata ita da ɗan babban aminin mallam Abdulshakoor wato mallam jibo jimeta babban ɗan sa halilu aka aurawa Asiya yanayin auren da ba wata soyayya suka yi ba haɗa su aka yi dan haka da dadi ba daɗi haka suka zauna lumui har Allah ya azurta su da ƴaƴa uku amma dukka Allah ya dauke abin sa tun daga haka bata sake haihuwa ba karahe taso halilu gaba aka yi akan sai ya sake aure haka ya kuma auro wata hansatu inda ta baza ƴaƴa da yawa ha su takwas ga gori ga yada magana duk akan Asiya sanadiyar hakan ya janyo mata ciwo mai tsanani har yayi ajalin ta tun daga nan gaba ta shiga tsakanin iyalan halilu da kannen Asiya wanda suka dau alkawarin sai sun karar da zuri'a halilu tunda ya kashe masu ya kun san bafulatanin mutum da riko da haka ana nan har sai da suka karar da ƴaƴan halilu tas kafin su dawo kan sa shima suka karasa sa wannan aikin Abdulgaffar ne da ɗan uwan sa Abdulrashid dan sauran dai ba ruwan su haka aka share shekaru har an fara mantawa da labarin Asiya sai dai a zuciyar ya gwalgwal ba hakan ba ne dan a lokacin yarintar Asiya bata nuna mata kauna ba dan ita ce ƴa ta farko..

  Kusan shekaru goma a lokacin mallam Abdulrahman ya gama amincewa da ɗan shi na da baiwar zane dan haka karatun bokon da aka kai cikin garin su ya yi ruwa yayi tsaki har dai Abdulshakoor ya samu yayi firamary ya gama a nan ya yi kokarin jan ra'ayoyin ƴan uwan shi akan su shiga makarantar amma suka ƙi wai su kiwo zasu yi kyale su yayi ya fahimtar da mahaifin su akan yana son cigaba da karatun nasa ganin yana so kuma mahaifiyar sa na taya sa ya sa mahaifin ya nemar mai makaranta ta hamnun mai garin dan ƴaƴan shi na birni na karatu haka ya tafi makarantar gaba da firamary

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now