Page 39-40

600 45 1
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

'''JAN HANKALI'''
_A fagen da ya gabata wato page 37-38 an sami harɗewar sunaye inda na saka Abdulshakoor a madaɗin mallam Abdulrahman na saka Aisha a madaɗin Asiya a wun profession din su Abduljabbar ma na yi kuskuren sunayen su madadin Abduljabbar ne da ya gaji mahaifin ahi kamar a farkon tarihin sai na saka a wani passage Abdulshakoor ne ya karanci aikin mahaifin madadin shi da ya karanci business shi kuma Abduljabbar ya karanci Architecture da fatan zaku min uziri dan har na gama editing ban lura da kuskuren ba hope you akl will understand me love u_

3⃣9⃣➖4⃣0⃣

_NATIONAL HOSPITAL ABUJA_

Da sauri aka shigar da ita dan daga hasina sai su mama wato mahaifiyar su falmata su suka san da labour din tana gida ta danna wa hasina kira akan ta zo kasancewar ranar yaya umar na da serious case a kotu ganin ta cikin wani yanayi duba da date din ranar sai yake tunanin hala ma haihuwar ce ta zo mata duk ya bi ya damu ita kuma bata son ɗaga mai hankali gudun kar ya ki mayar da hankalin shi kan case din client din sa sai ta yi pretending kamar babu abin da ke damin ta alhalin tun kwanaki uku kafin ranar haihuwar take jin wani iri ai kuwa tafiyar shi babu dadewa ta fara experiencing intense labour pain shine ta kira hasina daidai ita kuma ta dawo morning lectures din ta kenan a lokacin da ta yi kiran mama da umma na zaune a falo suna hira akan bikin hasinar shine ta ke sanar da su ai salmar ce kamar haihuwa zata yi sai mama ta ce bari ta biyo ta su tafi tare suna tafiya gidan tana kara jin azaban zafin an ce za'a kira yaya umar ta hana wai case ne da shi kar su tayar mai da hankali toh in the process ne ta kira ni a lokacin pains din ya dan yi subsiding muna cikin wayar ne kuma pains din ya dawo mata sabuwa..

Straight intensive labour ward din asibitin aka wuce da ita sai salati ta ke ta yi ga azaban da take ji a marar ta ga ciwon baya duk ya taru ya mata yawa ta rasa ya zata yi ko da aka duba ta bata gama kaiwa lokacin haihuwar ba dan da sauran awowi biyu kafin lokacin da aka sanar da ita kuka ta saka tana ta yi in ciwon ya lafa sai ta dan yi bacci da ya tashi kuma kamar zararriya take komawa a wannan halin na tarar da ita mama na ta petting din ta hasina na kuka wai rasa yar ta zata yi ko ni da zuwa na kenan act ɗaya na gani amma sai da na zubar da hawaye a haka har muka share awa ɗaya da rabi zuwa lokacin falmata ta iso itama dan da gani itama lolayin ta ke fama da shi karfin hali ne yasa ta tawo asibitin wani irin murdaɗen karar da ta yi ne sakamakon juya mata da cikin ta yayi ya sa muka tashi a tsorace rungume juna muka yi da falmata sai hawaye shar shar kafin a sani sai na fara kuka mai sauti har zafin ya tafi ta koma bacci amma ni kuka na ke ta yi an yi rarrashin dan kowa a zaton shi ko dan azaban da na ga aminiyata a ciki ne ya sa nake kukan basu san cewa kukan mai dalili bane dan dama mai jira yake aka harbe shi da dutse kuka nake yi kamar ni ce ke cikin matsalar few hours ago i couldn't pour out the pains in my heart yanzu da na sami kafa sai na rinka risgar kuka ban daina kuka ba sai da na ji ana cewa a yi preparing din ta ma second stage haihuwar ta zo da sauri na share hawayen ni da sauran muka isa zuwa kofar dakin haihuwan at least ta dau kusan 15-18 minutes tana pushing before she finally pushed out the baby da complete Apgar score din ta ta fito saboda da kuka da kuzarin ta ta fito kukan ta ke ta ratsa faɗin unit din hamdala muka yi baki ɗayan mu yayin da bacci mai daɗi da gajiya ya dauke salma kamar mintuna biyar aka fito tambayar relatives din ta muka taso midwife din na murmushi ta mana barka tare da cewa it's a bouncing girl ta miƙa mana da barin hannu na karɓe ta sak babu inda ta rage salma dan ƴar kutubebiya ce tubarkalla kyakyawa ga hanci da farin fata sai mutsu mutsu take yi tana fiddo harshen ta alamun yunwa take ji ta wani fannin kuma in aka kura ma babyn ido kamar ta ɗaya da falmata sai da na gama ƙare mata kallo na mata addua'ar albarka a rayuwar ta na miƙawa mama itama addua'ar ta mata kafin ta mikawa hasina da sauri ta karɓi babyn tana mata surutai wai ita ce auntyn ta yanzu dariya ta bamu matsawa na yi na kira layin aunty mama a nan nake sanar da ita cewa salma ta haihu na faɗa mata asibitin nace ta sanar da Abbu kar ya ga ban dawo da wuri mun gama na kira dija na sanar sa ita haihuwan barka ta min daga nan na dawo na zauna ina jiran farfadowar ta babyn na hannun falmat tana ta jijigata dan sai kuka ta ke ta yi kuma ance a bar maman baby ta huta kaɗan by then mama ta sanar da su umma batun haihuwar dan haka aka fara shirya tarbar ta dan mama ta ce wankan gida za'a mata ko ta kan angon ƙarnin ba su bi ba..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now