Page 3

1.2K 73 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

3⃣

   Chan dai da naga abin da nake yi ba zai fishe ni ba sai na daga kakafata izuwa inda gadon yake na tsura mata idanu na sai kuma ta juyo ahankali tana kallo na kamar ba ita bace yanzu ta gama kyakyatawa

  Zugum tayi tana kallo na ta bude baki ta fara magana da sassanyar muryar ta mai cike da sanyaya zuciya tace

   "Baiwar Allah DanAllah kije ki dauke min shi walahi kashe min shi zasu yi dazu ma sai da suka kuma nanata min ai nasan ke ba halinku daya da su ba,ce min suka yi fansar rayuwata kadai zai kubutar da shi na ce musu na amince amma babu wanda ya saurare ni hasalima ce min sukai in koma in kwanta lokacin bacci yayi""

Ta karasa tana share kwallar da ke tsere a kan kyakyawar fuskar ta

Ikon Allah na fada a cikin zuciya na,, toh wai ita wannan mai ta yi da har zai sa a kawo ta irin wannan wuri wurin da kowa ke gudun sa wurin da koh jahili ya ji sunan shi sai ka ji yana "Allah ya kare mu"

Sai gashi yau mace har mace wacce da ka ganta ka san hutu da ilimi sun ratsa ta sosai wacce bata da wata maƙutsa ta ko ina ta tsinci kanta a wannan wuri( _jan hankali mind you a psychiatric hospital ba wai wun ajiye mahaukata bane a'a hasalima idan da mutum zai duba daki daki yanayin ward ward da ke asibitin zai ga cewa babu ward din mahaukata ko daya a asibitin saboda dama ba dan su aka yi asibitin ba_

_Mutanin mu na da wani irin believe da perception about psychiatry har suka ce ai asibitin mahaukata ne wanda ba gaske ba ne dalili kuwa shine psychiatry wuri ne da ake kawo mutani wadanda ke da matsala da striking balance tsakanin internal and external need din su wadanda ke yawan samun matsalar "obsession" zan yi bayanin shi a wani page din,masu ta'ammali da miyagun kwayoyi masu saka mutum maye da juyewar tunani,mutani da ke da matsala bayan rasa wani daga cikin mafi muhimmanci a rayuwar su sai suka shiga state of depression har suke kokarin committing suicide.._
_Toh kenan kun ga ai baza'a kira wadannan set of individuals da mahaukata ba directly since akwai dalili_

_Again mata da suka haihu sai suka samu ɓallewar jini suma ana admitting din su a psychiatric hospital ana kiran condition din da puerperal psychosis haka ma duk macen da infection ya shige ta bayan haihuwa tana da tendency na samun matsalar da zai yi requiring admitting din ta a psychiatric hospital saboda suna zuwa direct ne su taba kwakwalwar mutum we vary in person wasu hakan zai faru da su amma ba abin da zai same su while others ba haka bane_

_Matan da suka haifi babyn da bashi suke so ba kamar haihuwan ɗa namiji alhalin an kwallafa rai akan ƴa mace yana iya janyo matsalar damuwa da zai yi requiring admission a psychiatric hospital ana kiran condition din da "baby blues"_

_In fact a 3years old child has accommodation in psychiatric hospital yaron da zai kasance bai da aikin yi sai kukan banza da birgima haka siddam that child is considered as a mentally ill child kokuma ya rinka throwing tantrums anyhow_

_Toh wannan ma za'a kirashi da hauka ne? Koh ke zakiso a cema danki ya haukace ne saboda abubuwan da yake yi ai bazaki ji dadi ba toh haka ma wata bazata so kice ma dan ta mahaukaci ba_

_Old men and women na da unit din su a psychiatric hospital_

_In nutshell ina so in yi correcting mana misconception din mu akan psychiatric hospital akan ba wurin mahaukata bane rather is a place where one's problems are being solved instead_
_Akwai su dayawa i can't start listing all the reasons da ke kai mutum psychiatric hospital amma wadannan are the least Allah ya shige mana gaba)_
  Toh koh dai ba ita bace aka zagaye dazu misalin mintuna talatin da biyar da suka wuce ba?

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now