Page 71-72

698 36 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

7⃣1⃣➖7⃣2⃣

_ROYAL HIBISCUS HOTEL_

  Zaune suke shi da ita suna ɗan hirar su na masoya ta kalle shi ta ce
"Hayati ina ji a jiki na kamar na kusa haɗuwa da amana ta kamar Abdulrahman ya kusa bayyana in gan shi"!!

Rungume ta yayi ya ce

"Habebati ina tare da ke kuma zan cigaba da yi mana addua'ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan sarƙaƙiya InshaAllah mun kusa tona waɗannan azzaluman da suke bibiyar mu ba mu ji ba ba mu gani ba"sai ga ƙwalla a idon ta yayi saurin goge mata

"Kar in ƙara gani Habebati sau nawa zan rinƙa gaya miki cewa matuƙar Abubakar sadik na raye toh ba kya buƙatar zubar da hawayen ki akan wani ɗan ƙanƙanuwar abu"share mata hawayen yayi ya rungume ta rasa abin cewa ta yi dan haka ta lafe a jikin shi tana mai magana muryar ta chan ƙasa shi kuma yana ta murmushi daga baya ma sai ya saka dariya yana faɗin

"Habebati baki da dama ko kaɗan kin san fah gandama gandaman ƙanne ne da ke har uku duka maza ga matayen su har da ƴaƴan su amma kike waɗannan kalamai haba big sis ɗin D'AA's"Dariya suka saka gabaɗayan su dan abin ya basu dariya karshe wasar ƴar ɓuya suka shiga yi har dai ya kamata suka shiga kyalkyala dariya...


***********

_ABJ_

  Barin MJ building ɗin ya koma gidan shi ya danna kira ana ɗauka ya ce
  "Ke wai wace iriyar yarinya ce na baki lokaci amma kina son ƙure ni koh toh bari ki ji ni barin ƙasar nan zan yi gobe kin sani sarai in har na bar ƙasar nan baki fiddo da yarinyar nan ba matsalar ki ce dan babu wanda zai zarge ni da ɓacewar su sai ke in aka kama ki kuma kin san makomar ki"yana kaiwa nan ya katse kiran yana faman huci wani lambar ya kira aka ɗauƙa

"Dad na gama abin da ka ce in yi ba yi releasing ɗin shi amma ni tafiya zan yi dan haka ka yi clearing komai na yi ƙoƙari na to make you proud but duk ba ka gani i gotta get out of here kuma kar ka neme ni dan ba zan kuma dawowa ba yanzu"ɗif ya kashe kiran yayi wurgi da wayar ya fara ƙwalawa Tina kira

Da sauri ta zo tana haki
"WTF? I have been calling you but you ignored me right? are you deaf"? Da sauri ta shiga girgiza kai tana

"Sorry sir i didn't hear you"kwafa yayi ya bata umarnin ta shiga ta haɗa mai kayan shi ta amsa ta mai juyawa zuwa direction ɗin ɗakin shi shi kuma ya cigaba da huci kamar zai ci babu dan wani irin takaici yake taso mai na rashin nasarar da ya samu a rayuwa biyu babu ba trust ɗin mahaifin shi babu fame a duniya kamar yadda ya tsara..

Kira ta yi tana haki kamar wacce ta yi gudun fanfalaƙi ta ciro wayar ta daga aljihun gaban rigarta ta danna kira ba'a jima ba aka ɗauka

"Sir,boss asked me to arrange his important documents and gadgets i think he want to run away"ko me ya faɗa sai ta ce

"Ok ok yes i understand i will i will alright"ɗinn ta kashe wayar ta cigaba da harhaɗa mai kayan na shi ta gama ta fito ta sanar da shi cewa ta gama haɗa mai kayayyakin miƙewa yayi ya nufi ɗakin ya duba ya ga komai daidai sai ya buƙaci da ta kawo mai coffee fita ta yi ta haɗo mai ta kawo miƙa msi tayi tana tambayar shi ko yana da buƙatar wani abin kallon banza ya aika mata da shi kafin ya yi sipping ya bata amsar

"Just leave will you"!? Juyawa tayi ta na tafiyar a hankali shi kuma ya cigaba da gwagwaɓar coffeen kafin ta bar ɗakin tuni ya ɓingile a wurin ya fara baccin dole da sauri ta danna wata lamba ana ɗauka ta ce

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now