Page 47-48

634 50 14
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_Ina maku fatan alkhairi ummerherny nerserller da fatima usman a cikin rubutun gasar ku da zaku fara Allah ya taimaka ya baku nasara da ikon lashe wannan gagarumar gasar Allah ya baku damar fidda BWA a faɗin duniya ba iya duniyar marubuta ba All the best_
4⃣7⃣➖4⃣8⃣

  
Na shafe awowi biyu a sume ba tare da na san inda kaina yake ba a cikin waɗannan awowi biyu an yi presentation din da ya kamata in yi kuma Alhamdulilah an sami kyakyawar sakamakon da ake saka ran samu su ahmad sun taka rawar gani gurin tabbatar da cewa komai ya kammalu yadda ya yakamata dan sun gudanar da abubuwa akan tsari.

  Koh da na farka a cikin office ɗi na na gan ni kwance saman couch ɗin offishin daga ni sai shi da ke zaune saman kujera na ya ɗan yi leaning ya lumshe idanun sa kamar baya tare da hankalin shi a offishin gama bude idanuna nayi sai kan fuskar shi na juya idon naga a cikin office din na ne tunowa da na yi da abin da ke rubuce cikin papern nan sai na tashi a birkice zan fita ga jiri na ɗiba na ga azababben ciwon kai ai daga zaunen da yake ya wani janyo min hannu na kamar kiftawar ido sai kuma yayi saurin sakar min hannun yana hade fuska

"What are you trying to do Ms Murad"? Koh ba ki san baki da lafiya bane?

Kallon shi na yi kawai sai na kara yunƙurawa zan tashi ihu ya min wanda ya daɗa haddasa min ciwon kai ban san lokacin da na koma na zauna ba ina kuka shima zaman yayi yana facing ɗi na

"Please let me go bana son wani abu ya faru da su saboda ni bana so ta sanadiya ta su rasa rayuwar su ga ƴaƴan su in na bari ƴaƴan su suka zama marayu har abada ba za su yafe min ba dan haka ka bar ni kawai in tafi Mr Abdulsalaam"

Komai bai ce min ba dan im gani nake ta sanadiyata wasu zasu rasa rayukan su toh shi fah

"Ms Murad babu inda zaki tafi in baki sani ki sani yanzu your blood pressure has risen kuma yayi elevating beyond your age koh so kike ki yiwa iyayen ki asarar ɗiya kamar ki?bakya tunanin ni kuma ba zan taɓa yafewa kaina ba in har ta sanadiya na kika rasa farincikin ki kuma rayuwar wasu ya salwanta saboda in kina ganin laifin ki ne suka shiga halin da suke ciki ni kuma ai nine dalilin shigar su halin da suke ciki dan ba ke suke hari ba ni suke hara amma suka fake da amfani da ke dan su ɓata maki suna"..

Sai na share hawaye na na fara magana

"Ba laifin ka bane laifi na ne da na yarda na fidda sirri na ma wasu har aka yi ƙokarin yin amfani da shi dan a cutar da nawa na jiki amma ba kai ke da alhakin abubuwan da suka faru ba saboda haka ka bar ni kawai in je in basu abin da suke buƙata in rabu da su lafiya"

"Didn't you get it?na ce maki ba ke suke hari ba ni suke hari dan haka just forget about that issue it has been handled already" furzar da iska yayi daga bakin shi nikuma mamaki ya gama cika ni ta yaya ya san wanda ya turo da saƙon har ya yi handling matsalar bayan koh ni ban san wanda ya turo da wannan abin ba sai shi kuma ta yaya ya san ma da family din da ake nufi

"What did you mean it has been handled bayan baka san familyn da aka kaiwa harin ba sannan baka san wanda ya turo da saƙon ba"!!

Murmushin takaici ya min kawai sai ya ce

"Kece dai baki san wanda ya turo ba amma ni ina sane kuma very soon zan yi exposing ɗin shi"

I was a little bit shock toh waye sai na yi directing mai tambayar
  "Toh wanene wannan ɗin kana ji fah ya ce nan da wasu mintuna za'a nemi labarin su a rasa ta ya ka san cewa wani ne wanda kake tsammani"??

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now