Page 63-64

630 47 4
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

6⃣3⃣➖6⃣4⃣

Miƙewa tsaye na yi na matsa baya ina kallon shi ban san ta ina ba amma wani mugu mugun ƙaunar shi ke shiga na ina jin ba zan iya rabuwa da shi ba amma dole in kiyaye son zuciya da son kai na tare na gansu da khadijah da ita ya fara soyayya ni tsakanin su na shiga ban ma soyayya adalci ba in har na amince da auren shi dan tun yanzu ga halin da ta shiga duk a dalilin son da take mai tana neman salwantar da rayuwar ta duk dan na shiga tsakanin ta da masoyin ta me ya kaini shiga tsakanin su tun farko me yasa na kasa bude idanuwa na tun farko sai na bar su a rufe ina biyewa son rai na yanzu ga abin da ya janyo min ta ina zan fara ga son da nake mai ga tausayin dija da nake ji na katsalandan da na mata yayin da take tsaƙa da jin daɗin soyayyar ta anya na yiwa kaina adalci kuwa? na kyautawa kaina da rayuwar ƴaƴa na kuwa? zan iya cigaba da zama da haƙƙin wata a kaina while nikuma ina chan ina rayuwa cikin sukumi kuwa? kaii a'a ya kamata in roƙi afuwar dija sannan in bata haƙuri i think iya damar da nake da shi kenan na wanke kaina a wurin ta in banda wannan bana jin zan iya yafewa kaina abin da na mata dan na cutar da ita da wannan tunanin na tsaya chak na zuba mai ido na wasu lokuta

"Ina so zan je gidan su khadijah dan ina buƙatar magana da ita"a gigice ya miƙe

"Cutie har yanzu baki fahimce ni bane?ko bayan wannan bayanin ma kina fushi da ni ne"? Murmushin da ya fi kuka ciwo na yi na ce

"A'ah duk na fahimta kawai ina buƙatar ganawa da ita ne"tsayawa yayi yana mamaki na
"Kenan bukata na bai iso ki ba kike nufi"?

"Bukatar ka ta iso ni amma amincewar bukatar lies on so many factors wanda ban isa in tantance su kai tsaye ba"

Kallo na ya ke yi yana jin mamaki

"Me kike buƙatar bincikawa akai na? sanina ne baki yi ba ko baki gamsu da yardar da ke tsakani na da ke bane?menene baki sani akai na ba da har kika tunanin ba zaki iya amince min ba har sai kin bincika"?

"Hmm sanin ka da sanin tarihin ka ba matsalata ba ce in ni da kai mun san gaskiya wasu na bukatar a ganar da su ainihin abin dan haka ina buƙatar ganawa da dija"kaiwa nan na dau car key ɗina na dau wayata na fara tafiya tare min hanya yayi

"Banu inda zaki tafi Aisha me yasa baki da tausayi ne a duk lokacin da wani kofar farinciki ta bude min burin ki ki rufe kofar forcefully kawai kan ki kika sani babu ruwan ki da feelings ɗin wani i cared about you shi yasa na jure duk wasu abubuwa dan dai kawai in mallake ki a matsayin abokiyar rayuwa amma duk hustles ɗina ba kya gani kan ki kawai kika sani"

Kwayar idon shi na kalla na ga bacin rai amma duk yadda zai ɗau maganar sai dai ya ɗauƙa in ya so ma ya cigaba da min kallon selfish being amma ba zan iya cin amana ba

"Kana iya cewa duk abin da ran ka ke so akai na amma hakan ba zai sage min gwiwa ba dan ni na san abin da muke yi akwai ayar tambaya in kai baka yi la'akari da hakan ba"

Kaiwa nan na kama hanya na buɗe ƙofar na fita ina jiyo shi yana cewa but i said i wanna marry you na yi shiru na cigaba da tafiya a daidai lokacin da na hau kan titi a lokacin na ankara da shima bi na yake yi ina gaba yana baya ƙara speed ɗin motar na yi dan kar ma ya kamo ni haka shima ya ƙara gudun nashi motae kamar masu wasan tsere haka muka rinƙa sharara gudu da motocin mu a kan titi ban ankara ba na hango babbar motar kwashe kaya na dunfaro ni at the same direction da na ke tuƙi a 360 na juya hancin motar Allah ya kiyaye babu abin da ya same ni shima ganin hakan daga nesa ya rinƙa danna min horn amma na zata kokarin hana ni yake yi buɗewar kofar motar na ji na juyo kamar zai make ni ya ce
"Fito"babu musu na fita daga motar girar sama da ta ƙasa a haɗe ya fara masifa

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum