Page 4

838 84 7
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

4⃣

   Idar da sallah na ke da wuya na ga fitowar ta daga inda na ke tsammanin kitchen ne da murmushi ta ce min
"Har kin idar"
Na amsa mata da eh
  Ce min tayi toh taso kici abinci
Na ce mata "a'a nagode ma'am a koshe nake

Murmushi ta yi tace "ki ce dai baki da niyar amsar abubuwan da kike son samu ba kenan ƴata

Shiru na yi saboda ban san yadda aka yi matar nan ke da saukin kai haka ba duba da irin qualities din ta
  "Toh" nagode
"Yauwa koh ke fah""

   Muka mike muka tafi wani wuri a cikin falon da yasha shimfidaden abin zama mai kalar ja sakaye da doughnut pillows ga kuloli da plats hade da abubuwan sha a jere

  Zama nayi tayi serving di na da well cooked tuwon shinkafa miyar ganye(vegetable) wanda ya sha smoke fish 

Koh da muka gama cin abinci sai ta kuma bude wani kular zata zuba min wani abin
A hanzarce nace

"A'a na koshi ma'am ki barshi haka"saboda duk na matsu in ji abin da ya kawo ni

Girgiza min kanta ta yi tace "shikenan dan na lura bakya son cin abinci ko kadan"

Na yi yar karamar dariya na ce ba haka bane kawai dai na koshi ne

   Muka koma kan kujera a falon ta zauna tare da kiran wata dattijuwa mai suna mama habiba
Zuwa tayi ta ce "gani hajiya"
  "Mama fruit salad zaki kawo min""
  Toh hajiya ta koma kitchen din
  Itakuma ta juyo izuwa gare ni tana cemin
"All set"??
Cikin zumudi nace
"Very much set"ina murmushi
Itama shi ta min kafin ta fara

   

   _20/12/2018_
Shine ranar da aka kawota asibitin barnawa misalin karfe 2:47pm a daidai lokacin da tashi daga wun aiki na zan koma gida na turo hancin mota na kenan na hangi wani motar na shigowa sai na tsaya mishi ya shigo ni kuma na fito

Ina isowa gida kiran dr Ladan ya shigo wayata na daga da mamaki saboda ni dai na san nayi clearing komai kafin in fito daga asibitin
  Na dau wayar bayan mun gaisa sai yake ce min akwai wata patient da ya kawo temporary saboda wasu dalilan sa akan kwanaki goma shabiyu zata yi ya dauke ta

Na nemi sanin dalilin yin haka saboda it sounds kamar abin da yayi yayi ne illegally ba tare da ya bi steps din da ake bi ba saboda ya kasance daɗɗaɗen likitan kwakwalwa(psychiatrist)a asibitin har ya kai ana sa ran bashi matsayi mafi girma a asibitin saboda irin hazaka da kwazon shi
Yana iya yin abubuwa kan shi tsaye ba tare da an mishi wani tsatsauran bincike ba saboda yardar da aka mishi

Sai kawai ya ce min Hajiya Rukayya zan miki bayanin one on one gobe yanzu dai na ce su saka ta a bed 5 na bata alluran da ya kamata da wasu care da suka dace

Abin ya daure min kai sosai sai na ce mishi shikenan Allah ya kaimu

Da maganar na kwana na tashi

Koh da na iso asibitin sai na neme shi kafin ya zo har na karasa zuwa ward din ina jiran shi

  Da zuwa na na nemi a bani file din patient da aka kawo jiya nemo shi aka yi aka bani

  Na ajiye a office di na muka je aka yi handing over muka yi duk abin da ya dace na shige office di na na zauna
Zaro glasses dina nayi na saka na bude file din


*Aisha Murad Abdulsalaam*

Sunan da na gani kenan a jikin foldern
Shekarunta ashirin da biyar(25years)
A first class degree graduate on Art and design
Married with history of 2months pregnancy
Lives at Abuja

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now