Page 69-70

916 55 4
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_kuna rai na my dearies_

_maimunah🌹my maimu_
_deeja_
_jiddah_
_miss thomas_
_Mrs daddy_
_Halima bello_
_Farida mpape_
_Fatima garba_
_My maman mubeena_
_Ummu safwan_
_Allah ya ƙara zumunci_

6⃣9⃣➖7⃣0⃣

  Mun yi landing safely a nan na farka inda ya riƙo hannu na aka saka mana kayan mu a cab muka shiga na yi mamakin abin da ya hana shi sakawa a zo a ɗauke mu saidai na yi shiru dan zai iya yiwuwa duk a cikin sirrin da yake ɓoyewa ne a motar ma bacci bacci nake ji dan haka na kuma kwanciya a jikin shi while shi kuma yana ta shafa fuskata yana min sannu tafiyar da ɗan nisa dan haka kafin mu isa inda zamu sauka wata baccin ta kuma ɗauka ta sai shi ne ya fito da ni rungume a jikin sa kaɗan kaɗan na ke buɗe idanuna har na buɗe su tar na ga a kofar gida muke yanayin environment ɗin ya saka ni sakin jiki ban yi tunanin saukowa ba ƙaramar kofar gate ɗin ya buɗe mana muka shiga a babbar falon gidan muka tsai da madakata ya sauke ni haɗe da kwantar da ni ina ta kallon shi har ya cire min doguwar abayar da na saka ya rage daga riga sai wandon da ke ciki ya ɓalle boturan rigar exposing my chest ya cire rigar gabaɗaya cire jeans trouser ɗin ya yayi yana yi yana min tsiya wai jikin yayi yawa dole ma mu fara tafiya gem kafin mu koma murmushi kawai na iya mai bayan ya gama cire min kayan ya ya shiga yi min tausa ina ta lumshe ido na wani baccin ke son ɗauke ni ganin haka ya daina tausar ya ɗauke ni muka wuce zuwa bedroom ina iya cewa a yawan kayan alatu wannan bedroom ɗin ya fi na mu na Abuja sai dai a tsari da scanty room decorators na Abj ya fi.

Na yi tsammanin kwantar da ni zai yi sai yayi bathroom da ni kamar in saka mai kuka haka na rinƙa ji a lokacin da ya sauke min ruwan shower tun daga kai na kafin in ankara shima sai gashi ya yi joining ɗi na a shower ɗin babu alkhairi a tsayuwar mu dan sai da na gwammaci ƙiɗa da karatu babu abin da ya min amma wani irin muguwar rough play da yayi min har yana so ya shafe azaban da na ji a jiya amma na daure ban yi kuka ba karshe dai baccin na mai a shower ɗin dan kamar wacce ta sha wani abu na rinƙa ji ban san yadda ya karasa min wankan ba amma na farka na ganni kwance saman royal bed ɗin ɗakin ni kaɗai sanyin ɗakin a appropriate temperature da salati na farka na yi miƙa na ɗan ji dama daman jiki na dan haka kallon agogo na yi na yi saurin miƙewa na yi hanyar bayi na yi alwala na dawo na tantance gabas na tada iƙama bayan na idar na rinƙa zuba idon ganin shi amma ban gan shi ba dan haka na cigaba da karatun alqur'ani da nake yi a zuciya ta

Kamar bayan mintuna kaɗan na fara jin ƙamshi na daɗa buɗe hanci na sai na ji eh fah da gaske ƙamshin ne rasa ta ina yake fitowa na yi sai na fara bin ɗakin ina neman ta inda ƙamshin ke fitowa har na kai bakin ƙofar ɗakin ssi na ji ƙamshin ya daɗu a hankali na rinƙa saukowa har na iso tsakiyar falon na juya na ga wata ƙofa na tura kofar me zan gani..

My hubby in a complete chef attire hular dogo irin na masu girki da apron ɗaure a jikin shi ya saka wata karamar boot hannun shi sanye cikin abin sauke girki ga shi kitchen ɗin tsaf tsaf da shi kamar ba namiji ke aiki a ciki ba ƙamshin ya daɗu ina iya cewa ban taɓa jin ƙamshin flavour ɗin nan ba sai a ranar dan haka na ƙarasa cikin sanɗa na rungume shi ta baya sai ya sake murmushi ya riƙe hannu na ya ce

"Wify har kin tashi"? ban amsa mai ba sai na daɗa lafewa a bayan shi zai juyo na ce

"A'a cigaba da aikin ka"sai ya murmusa ya cigaba da aikin na shi na ƙi sakin shi in ya juya ina biye da shi kwance a bayan shi in wun oven zai je ina bin shi har ya gama kammalawa ina ta kallon shi komai cikin tsari da ilimi yake yin su ya tsara komai a muhallin shi ya jer su a dinning ɗin kitchen i was eager to taste the dish dan haka na taya shi haɗa kayan a saman dinning ɗin ya ce min

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now