Page 45-46

566 48 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_Kafatanin wannan shafi naku ne *Soyayya mai garɗi fans group* da *Brilliant Writers Association group* na san ya maku kaɗan amma ku yanyana shafin duk kalma ɗaya ku dauka na baku kyauta Allah ya bar zumunci yadda kuke nuna min so da ƙauna da adduo'in da kuke min ko na wa na jini ne sai haka_

4⃣5⃣➖4⃣6⃣

"Uban wa ya baki izinin zama a kujerar offishi na bayan kin rasa wannan damar kimanin mintuna arba'in da shida da suka wuce"a tsawace na karasa maganar not minding presence din Abdulrahman a wurin..

  Wani kallon ikon Allah ya min nima na mayar mai da martanin kallon da ya min tare da dage glass din sama na cunno baki gaba kaɗan

"Ya aka yi ne kake kallo na kamar ka ga sabuwar mutum huh"??

Bai ce min komai ba instead sai ya ce wa dija ta zauna zata zauna kenan na kuma tsawatar mata
"Malama in kika yi gigin zama a kujerar nan ki yi kuka da kanki dan kiran ki nayi ba wai kizo ki zauna min ba yawwa"?

Ban basu damar yin magana ba na yi proceeding

"Mr Abdulsalaam dalilin kiran Ms Alhassaan cikin meeting din mu shine ina so ne in yi clearing mata misconception din da take da shi a kai na da kai kanka dan gani take ko wata abin muke yi bayan mu'amalar aikin mu da kai toh so nake ta gyara tunanin ta ta san cewa ni Aisha Murad na fi karfin yi wa kawata kwacen saurayi sai dai sai dai ni a yi min again bana ɓata lokaci na a kan abin da na san ko zan mutu in dawo ba zai taba zama mallaki na ba na fi karfi kwace sai dai in mutum ya kawo kan shi gare ni da niyar agaza mai akan duhun da yake ciki na takurar wata" kaiwa nan na bar su da tunanin zuci

"Khadijah abin da yasa na yi kiran ki ba komai bane illah so nake ki ganewa idanun ki na fo karfin tijara dan na so magana da fiance din ki shiyasa na kira ki kar ki ga kamar wani abin zamu ƙulla sirri zamu yi a da na so in yi maganar a gaban ki but yadda kika yi reacting sai ya saka ni chanza ra'ayi na dan ba tsoron ki nake ba haka zalika ba ki isa yi min shamaki da abin da nake da ikon yi ba ni da building ɗi na so now that you have seen it with your naked transparent eyes kinaiya tafiya Ms Alhassaan"..

Fuuu kamar zata tashi saman ita in ba dan ya tilasta mata zuwa bada hakuri ba da ban isaa in daga mata murya ba dan a ganin ta ai ta min komai a lokacin da nake cikin tashin hankali ta manta cewa ita wahalar da kanta ta ke yi ba son ta nake yi ba amma ni ban taba wahal da kai na akan ɗa namiji ba hasalima su ke wahala akan soyayya ta ba tare da na sani ba

  Har ta kai kofa zata fita ta ji nuryar shi yana mai dakatar da ita cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba saka ta juyowar yayi haka ta juyo fuskar nan ya daɗa cika fam kamar zai fashe

"Kin yi abin da na aike ki yi"?

"Hero kana fa gani da idon ka yadda ta ke nuna min mulki a offishin ta kawai dan ina aiki a karkashin ta ta manta cewa a matsayin team ta roke ni mu yi aikin amma har ta ke da bakin gasa min magana still hero kana tsammanin ni Khadijah Alhassaan zan buɗe baki na in bawa Aisha Murad haƙuri toh wallahi Allah bata isa ba sai dai ta cinye kan ta dan bakin cikin abin da na mata amma ni ba zata tozarta ni ba dan babu abin da ban sani ba game da ita da rayuwar ta komai a hannu na yake yanzu ta ce har zata dakatar da ni a aiki saboda na nuna kishin ka a fili bayan maza kusan uku ta hana zaman lafiya biyu na nan na faman azabtar da matayen su saboda ita dan ta ki amsar soyayyar su wa ya sani halan kai ta hango take kokarin kwace min kai sai ta fake da cewa aiki aiki tunda ta zama injin aiki bata da hutu in ba wata manufa ce da ita ba ya zata dau zafi akan wannan ƴar ƙanƙanuwar maganar... ban bari ta gama maganar na dakatar da ita

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now