Page 29-30

548 44 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣9⃣➖3⃣0⃣

  _BEGINNING OF THE LOVE STORY_

11:50Am
A daidai lokacin da aka taru a gidan su salma kenan an baza nema na wai na bace jin wannan labari sai da falmata ta sume sama da sau uku dan duk blame ɗin akan ta ta ɗora koh ta kanta yaya kabeer bai bi ba yana chan yana ta nemana dan har lokacin bai gama fita daga raɗaɗin abin da ya faru jiya ba yaya umar kuwa Allah ya wadaran halin ta yayi ya ja hankalin salma dan kar ma ta ɗaga hankalin ta akan maganar falmata ummi da tashin ta kenan daga bacci ta karanta papern da na ajiye mata ta share kwalla ganin rubutun ciki kamar haka

_"Baby sis na san zuwa yanzu kin farka daga baccin da kike yina san kina karanta saƙon nan well ba komai zan faɗa miki ba dama so nake ki kama kan ki a matsayin ki na ƴa mace naji wai jiya hasina ta tona abin da kike ta son yaya Ibrahim ya sani i don't know how you reacted a jiyan but ina gargaɗin ki da ki kama ajin ki ki koyawa yaya Ibrahim son ki kafin ki bari ya gane mutuwar son da kike mai ki riƙe girman ki kin san ke babbar yarinya ce yanzu falmata is far away from yaya Ibrahim zai kasance cikin damuwa da ɗimuwa a matsayi na na ƴar uwar ki shawara da taimakon da zan iya baki shine ki taya yaya Ibrahim jinyar rashin da yayi na masoyiyar sa a lokacin ne kuma zaki dasa mai kaunar ki amma kar ki kuskura ki bari ya gane son da kike mai yayi yawa saboda ki a nan gaba kar ya sami laggon rainaki ko wasa da feelings din ki a nan gaba ni na koma Egypt kuma ba zan dawo ba har sai na kammala karatu na ki ja jikin ki da gidan su hasina ba zan hana ki mu'amala da ita ba amma ki san me zaki na fada mata kin dai ji kuma kin gani da idanun ki irin yadda aka yi mana a wun kamun yaya Aqeeb da yadda aka tozarta mu saboda ki iya takun ki kar ki kuskura ki ƙara zuwa shagalin bikin nan har sai komai ya lafa ki tsaya tare da yaya Ibrahim and be with him i love you baby sis take care of your self darling"_

Ta karanta papern ya fi a ƙirga tana ƙara bada kanta assurance ɗin cewa she can do it

  Yaya umar da ke kokarin reaching family demr din su dr hakeem ya yi nasarar samin shi ya mai kirar gaggawa akan ya yi saurin zuwa dan ko yaya naka ya lalace ai naka naka ne da haka dr ya ce su tsimmaye shi nanda mintuna kaɗan komawa ciki ya yi ya tambaya koh ta farfado  aka ce mai eh amma ta kwanta tun ɗazu bata tashi ba shiru yayi ya tambayi inda salma ta shige dan bayan ya ja ta suna gaba da fita daga mu aka danna mai kira haka ya neme ta ya rasa ya koma gidan shi ɗaya sai daga baya ta dawo itama ta karanta saƙon da na bari mata akan ta kula da falmata tare da kwantarwa yayan ta hankali akan ya yarda da ƙaddara itama ta gafarce ni saboda ba zan sami damar attending bikin ta ba but in na dawo zan zo gidan ta

Daga baya ne yaya Ibrahim da salma suka sanar da mutani cewa ai na koma makaranta ne still yaya Aqeeb bai daddara ba jin na koma makaranta shi so yayi ranar auren shi ya yi committing scene da zai saka dan dole ma a haɗa auren shi da ni bayan an daura da aunty mufeedah sai dai ya makaro bai shiga taitayin shi ba har sai ranar da ya ga an ɗaura auren shi da aunty mufeedah kuma taron ya ƙare ranar kuka ya ci sosai har aka shigo da amaryar sashen iyayen sa amma bai sani ba an kai ta gidan ta da ke cikin Apo gida mai kyau da tsarin kallo tun ana jirar zuwar ango har ɗaya bayan ɗaya aka watse bai zo ba hakan ya daɗa tunzira amarya ta daɗa daura ɗamarar yaƙi da ni dan ta san ni ce silar hana shi zuwa gidan ta kira lambobin shi amma shiru bai je ba tana kuka tana tuge kwaliyar da aka mata tsanata na daɗa shigar ta sosai bai dawo gida ba sai biyu saura na dare a lokacin da ta gama ciki fam yana shogowa falon ta fara zazzage mai kwandon bala'i in ban da kallon ta ba abin da yake yi dan a ranar bai yi gigin shan giyar ba ganin ya rasa ni rasawa ta har abada tana kaiwa ƙarshen aya ya wuce ta ya haura sama wani ɗaki daban ya shige ya ƙulle kan shi maganar duniyar nan ta yi kukan ta yi masifa ta yi karshe rokon sa ta koma yi dan ba ta shirya rasa shi ba a nan ta yi bacci shikuma zaman kurma yayi dan kwakwalwar shi ya dai na aiki haka suka karasa daren cikin wani hali washegari da ya tashi ya shirya cikin suit din sa ya fito ya same ta kwance a bakin ƙofar ya kalle ta dan tausayi ta bashi sai dai ai shima abin a tausaya mai ne masoyiyar sa ya rasa fah daka haka ya tsalake ta ya wuce zuwa office abin shi ko da ta tashi ta ga baya nan kukan ta ɗora akan wanda tayi jiya karshe ta shige ta gyara mai ɗaki ta yi nata dakin haka rayuwar su ya cigaba babu walwala babu magana mai daɗi kuma ko daidai da rana ɗaya bai taba kuskuren shiga ɗakin ta ba koh ta shigo nashi ɗakin to barin mata ɗakin yake yi shi kuka ita kuka duk sun rame..

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now