Page 19-20

587 47 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

1⃣9⃣➖2⃣0⃣

Da asubar fari na farka na kurawa ummi ido ina mata kallon mamakin abin da ya faru a jiya da haka dai na tashe ta na ce ta je ta yi sallah dan ni ina fashin sallah da mamaki sai ta ce min yaya Aisha ai ina hutun ne nima..

In total shock na ce kina fashin sallah fah ummi ta daga min kai ta juya ta cigaba da baccin ta sai nima na kwanta ganin ba abin mamaki bane dan salma ma a shekaru goma ta fara balantana wannan da ke goma shabiyu

Ba mu muka farka ba sai karfe takwas na safe shima saboda hayaniyar su falmata da muka ji ne shigowa dakin suka yi suna jijiga ni wai in tashi mu tafi saloon da wun gyaran jiki karfe biyu za'a fara shagulgulan baccin bai ishe ni ba amma haka na diro daga kan gadon na nufi toilet ina balbale su akan sun datse min bacci na dariya suka min suka zauna zaman jira na suna tataunawa akan irin kayan da zamu saka yau..

Salma ce ta ankara da cewa ba ni kadai ba ce sai ta janyo blanket din ta fara tayar da ummi koh da ta dago ta gansu sai ta yi murmushi ta ce yaya salma har lokacin abin yayi ne?

Dariya ta mata tace haba kid sis ba dai da shi kika yi bacci a rai ba ko irin wannan tambayar kai tsaye babu koh gaisuwa!?

Sai ta rufe idon ta wai ita kunya gaba dayan su suka mata dariya sai ta dago ta ce ina kwana yaya salma ta amsa mata sai ta juya zuwa gun falmata ta ce ina kwana yaya falmata itama amsa mata tayi suna mata tsiyar ta zaku aje wun shagali itama sai ta musu dariya tana tambayar su ina na ke falmata ce ta amsa mata da cewa ina toilet

jim kadan na fito daga toilet din daure da towel a kirji na na saka hular leda a kai na wani irin shu'umin kallo falmata ta min kafin ta ce

"Gaskiya yayan mu ya more irin wannan diri Aisho ina zaki kai shi"

Harara na maka mata na ce falmata ki fita a idanuna in rufe wai ni ya kike alakantani ne da mazan gidan ku haka kawai ina zaune siddam na juya zuwa ga salma da ke mana dariya ta ma ce ke banza kina jin me falmata ke gaya min kuwa saurin tarar numfashi na tayi ta ce ai kun fi kusa indo ku da kuke yan gari ɗaya..

Da haushi na halbi salmar da hular kai na na ce hala bakiyi bacci sosai bane jiya kike magana a ruɗe??tsaki na yi ganin sun mayar da ni abin dariya ita salma duk daukar ta da yaa Aqeeb falmata ke alakantani da kuwa bata da masaniya akan cewa yayan ta kabeer na so na balantana ta san cewa falmata ta gano hakan har tana min tsiya da shi

Kumbura nayi kamar filawar da yasha yis na zauna na ce

"An ma fasa fita da ku din yaya Ibrahim ne zai kai ni kuma karar ku a kunnen yaya Kb" kwafa na yi kwafa na juya fuska na ina harar su kasa kasa

Dariya suka saka min suna cewa haba Aishan mu yi mana afuwa baza mu kara ba kin ji yau fah special day ne kar ki manta ke dai kizo muje kar muyi latti kin ji yi hakuri sweetheart

Banza na musu har sai da nagama jan aji na kafin in amince mu tafi shiryawa na yi cikin doguwar riga na yi rolling da gyale mai dan girma dan ni na tsani kananan gyalulukan nan na zamani muka fito muka ma Abbu sallama da yaya Ibrahim har yake cewa mu bari ya kai mu amma muka ce ya bari sai da suka yi hirar su ta soyayya kadan da falmata kafin mu wuce muna zolayarta ta share mu tana murmushi ta ce yara kun yi batan hanya ana yi banda ku..

Dariya kawai muka mata muna cewa ku dai rashin kunya ce ta muku yawa kawai

Salma karaf ta ce oohh ni salma habib falmata da fah kunyar tsiya ce da ke kamar bazaki iya kallon namiji ba har nake jiye miki ashe dai mune sabbi bamu sani ba ke tuntuni yaya Ib ya yaye miki kunyar

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now