Part 1

4.7K 209 10
                                    

Bismillahirrahmanirraheem
Da farko dai ina maku sallama irin na addinin musulunci assalamu alaikum.
Bayan haka ni sunana Nafisa Aliyu wadda aka fi sani da Pheener 👑 This is my first novel so da Allah ina so ayi min uzuri idan an dan samu mishkila saboda kowa yasan nobody is perfect. Allah ka bani ikon isar da saqon dake qunshe cikin littafin nan.

Cikakken hamshaki kuma sadaukin namiji nake hangowa, kallo daya zakayi mishi ka tabbatar da tsantsar jarumta a tattare dashi domin kuwa kana ganinsa zaka tabbatar da ya amsa sunansa na asalin namijin mazaje kuma gwarzo. Baki ne shi mai cikar kirji da kamala, dogo ne kuma mai ji da qarfi a jika. Fuskarsa tana dauke da madaidaitan idanu masu tafiya da imanin mai kallonsu, da matsakaicin hanci. Bakinsa dan da dai. Tabarakallahu ahsanul khaliqeen. Duk inda namiji yakai wannan yakai. Ba wani bane wannan fache Usmanu wanda aka fi sani da Namijin zaki. Usman matsashi ne dan kimanin shekaru 24 wanda karfinsa da jarumtarsa ke bawa kowa mamaki. Indai kukai gaba da gaba dashi a filin daga to sai dai wani ba kai ba. Ba iya karfi abinsa ya tsaya ba, duk wani salo da dabara na fada yana dashi. Dan gata ne na kin karawa kuma dan sarauta. Maiji da mulki, izza, isa da qasaita. Wanda bai dauki kowa a bakin komi ba. Kasancewar ubansa ke mulkin nahiyarsu yasa yake jin kansa kamar duk duniyar a tafin hannunsa take. Yana iya taka kowa ya kwana lafia. To me yasa ma bazai kwana lafia ba. Idan baka barshi dan karfin mulki ba ai dole ka barshi dan karfin damtse 😝. Wannan kenan.

Birnin maleeta

Birnin maleeta wani yanki ne da yake arewa, Allah ya albarkaci wannan birne da ni'ima da kwanciyar hankali

Oops! Questa immagine non segue le nostre linee guida sui contenuti. Per continuare la pubblicazione, provare a rimuoverlo o caricare un altro.

Birnin maleeta wani yanki ne da yake arewa, Allah ya albarkaci wannan birne da ni'ima da kwanciyar hankali. Basu san wani abu ba wai shi yaqi. Suna zaune ne karkashin sarkin su mai adalchi da matemakansa. Galibin garin ba yare daya sukeyi ba. Yaruka 3 ne a garin amma ginshiqin yaren da akafi yi shine fulatanchi. Don fulani ke kaso 50 na garin. Sai Hausawa da kanurai ke da 22 da 28. Birnin maleeta birni ne na wayayyun mutane wanda karatun boko ya ratsa su.

Suna da fadama da koramai. Suna noma sosai ga sana'ar hannu. Akwai kusoshin gwamnati manya manya a birnin. Ga sarkinsu da matemakasa. Kada kuyi mamaki in na ce muku matemakansa. Su wannan birnin haka al'adarsu take. Sarkin su Fullo ne to mataimakansa da bahaushe ne da babarbare. Saboda zaman lafia da adalci da kuma hadin kai irin na birnin. Akalla akwai kimanin mutane miliyan 4 da dubu dari 6 asalin haifaffun birnin. Da gidajen su 🏘 da masana'antarsu 🏭 da makarantunsu da wajen bautarsu da maaikatarsu. Duk mazauna wannan yanki walau hausawan ko fulanin ko kuma kanurai duk zaka same su da wata irin gogaggiyar fata mai tsananin kyau. Ga matayensu da gashi tabarakallah ga kuma dan uban kyau. To ai dole ma fatarsu tayi kyau ko dan ni'ima da da Allah ya albarkace su da shi. Kama daga yanayin weather in da arzikinsu.

Idan naga yanayin karbuwarsa sai na cigaba.
Yours Pheena 👑

Namijin Zaki 🦁 Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora