part 13

335 50 3
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 13

Haka kuwa ya tashi shima ya chanja nasa kayan sannan ya bar wajen ya nufi masaukinsa. Wunin ranar gaba daya a dagule lissafin sa yake. Surar jikinta ne kawai yake bijiro masa."What are u doing Usman, what the heck is wrong with ya? Me yasa duk kabi ka damu ranka ka daga hankalinka? Me kake shirin yi? C'mon, u r more sensitive than this. Kai ne fa, Usman namijin zaki." Haka zuciyarsa tayi ta kwabar sa amma kwakwalwarsa bata bar tariyo masa surar jikin Meenal ba. Karshe sai yanke shawarar ya je ya nemo Saeedu Turaki yayi. Maybe idan yana tare dashi ya dena wannan banzan tunanin. Bai gama tunanin mafitar nan ba Turakin yayi sallama. "Yauwa dama nemanka nake." Usman din ya fada ba tare da wani dogon tunani ba. "Ni kuma ranka ya dade? Ina fata dai lafia." Shiru Usman din yayi kafin yace."lfia lau, ina so ne ka raka ni cikin garin nan na zaga." Mamaki kwarai abin ya bawa Turaki amma sai ya maze. "Babu damuwa ranka shi dade, yaushe zamu tafi."?  "Yanzu" Namijin zaki ya bashi amsa. Ba wani bata lokaci suka dunguma bayi na biye dasu kafin Usman din yaja birki. Tsayawa suma bayin sukai. Hannu ya daga musu kafin kiftawar ido kowa na wajen ya kama gabansa. Turaki bai gama mamaki ba sai da yaga Murmushi ya subuce wa Usman din. "Lallai da wata a kasa. Ruwa baya tsami banza." Turaki ya raya a ransa.
To a bangaren Meeno kuwa, ido ta bude ta ganta a kan gadonta na dakin da aka sauketa a Pasweek. To tasan dai abokan nata sunzo amayari guda amma ta kasa tuno yau inda suka kaita. Ita dai tasan ba Zabbit inda suka saba zuwa suka je ba. "To ina suka kaini yau?? Kamar fa naga kanin Chiroma a wajen? Amma ai ance yayi tafiya, ni kuwa sai na binciko." Tambayoyin da tayiwa kanta kenan bayan farkawarta. Abinda kuma yafi daure mata kai shine taje bandaku yin alwala kawai sai taganta da wani bakon gajeren wando. "Daga ina shi kuma wannan."? Ta tambayi kanta. Ita abin ma dariya ya bata. Haka taita kyakyacewa har ta gaji dan kanta ta fito.

Ita ko Baana maman Meeno tun tana kukan rabuwa da 'yar tata har ta hakura ta dau dangana. Domin tasan kukan babu inda zai kaita. Ita dai addu'arta a kullum bai wuce Allah ya tsare 'yar tata ba ya kiyaye ta daga sharrin masu sharri.

A masarautar Maleeta kuwa, Fulani ta shiga tsananin damuwa na son ganin fuskar Namijin zaki. Abin har ya kai ta ga ta tambayi wata baiwarta akan taje ta dubo mata shi ko yana ina? Bayan baiwar ta dawo ne take sheda mata cewa anga fitar su da shi da Turaki. "Yaya Turaki sun fita da yarima Usman? To ina zasu je."?
Ta tambayi kanta da tsananin mamaki. "Maybe zagaye gari sauyi" ta bawa kanta amsa. Anan ta kuma bawa wannan maid din umarnin duk sanda taga dawowarsu to ta gaya mata. Ita dai yau tayi alkawarin ganin shi at all cost.


To a bangaren Meeno kuwa wata baiwa ta samu da tasu tazo daya take tambayar ta ko ina taji kanin Chiroma zai je? Murmushi wannan baiwar tayi tace."Yarima Usman kike fada? Namijin zaki kenan, ai ya tafi neman auren diyar sarkin Maleeta ne Fulani Nawwara."
Dammmmmmm! Gabanta yayi mugun faduwar da bata san dalili ba. "Maybe dan naji an ambaci Maleeta ne." Ta raya a ranta. "Allah sarki Ammee nah." Ta goge hawayen tuno da mahaifiyar ta datayi. A gaskia to yau dai abokan nata basu kyauta mata ba. Sukaita Maleeta amma suka kasa karisawa da ita wajen Ammin ta?
Tashi tayi ta nufi hanyar masaukinta. A lokacin magariba ta doso. Timmm! Taji tayi karo da mutum. Dago kai tayi a tsiwace tare da karkace baki zata fara ruwan masifa. Saurin sunkuy da kai tayi ganin Chiroma ne. "Kayi hakuri ranka shi dade ban san kai bane."
"Babu komi Meenal." Ya fada yana mai Murmushi. Murmushin itama tayi sanna tace."yauwa Ranka shi dade yaushe zaka maida ni gidan Auntym tawa? Nifa zaman gidan nan ya ishe ni."
"Maganar da naje na sanarwa Ummi kenan, auntyn taki ma ai a nan masarauta take,mijinta ne sarkin dawakin tsakar gida a fadar nan."
Shiru tayi na wani lokaci sannan tace."tabbas, na taba jin Ammi na tayi makamanciyar maganar nan."
"To yanzu kije wajen Ummi zata hadaki da mai rakaki ayau ba sai gobe ba." Ya fada yana mai wucewa. Ita dinma wucewar tayi ta nufi wajen Ummin. Bayna taje ne Ummin ta sake mata bayani sanna tace ta hada yan kayayyakinta sai jakadiya ta rakata. Sunje sun sami Auntyn tata tana kwasar tuwo a kitchen. Ko da jin sallamar Jakadiya sai ta fito da saurin ta tana maraba. Taga dai da mutum a gefen Jakadiyar amma kasancewar gidan ba isashshen haske ga magariba sai bata gane ta ba. Sai bayan sun zauna a tabarmar data shimfida masu ne Jakadiyar ta kora mata jawabi. A gigice take amsawa kafin tasa torch ta haske fuskar Meenon. "Itace wallahi, wallahi itace Jakadiya. Amma nagode Allah ya saka miki da alheri."
"Ba ni zakiya wa godiya ba, Gimbiya zakiyiwa ko ince Yarima Chiroma domin sgi ya samo miki ita tun a  birnin Zabbit."
Godiya Bilkisa ta sake yiwa Jakadiyar kafin ta wuce ta tafi ta barsu.
"Allah nagode maka." Ta sake furtawa a karo na babu adadi. Kala Meeno  bata ce ba domin ita mugun  haushin Aunty Bilkin take ji.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now