part 19

383 47 2
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 19

*Wannan page din sadaukarwa ne ga 80k.. kwarai Allah ya saka da Alkhairi bisa kokari 80k.*

Sarki ne ya bada umurnin a balle kofar ta karfin tsiya domin yana da yakinin babu lafia. Hakan kuwa ce ta faru, da aka balle kofar main entrance din ko da sarki da Gimbiyar suka shiga, sun tarar da kofar bedroom dinshi a a bude amma an turo ta. Har rige rigen bude ta suke. A kwance suka tarar dashi yayi ruf da ciki. Kafar sa daya tana lilo daga saman gado domin a farko gadon ya kwanta. A guje Umminsa ta karasa tana kiransa."Me yake faruwa ne Usman? Me ya same ka."? Ta karasa maganar tare da dafa shi. Azababben zafin da taji a jikinsa ya sa tayi saurin janye hannunta. Mai martaba ba zafin da jikin Usman din yayi ya bashi mamaki.
Cikin nutsuwa ya fara magana."Me yake damunka Usman? Kana son kashe kanka ne zaka kulle kanka a daki baka da lfia har haka."
"Lafia ta kalau Abbi, kawai banjin dadi ne." Ya fada tare da tashi zaune.
"Wanne irin lafiarka kalau? When will u stop behaving like a child for Goodness sake? Haba mana." Gimbiya ta fada a hasale. Usman ne ya katse ta da cewa."Kiyi hakuri Ummi amma ni ko gashin jikina daya baya min ciwo and i mean it."
Tasan Usman bai taba mata karya ba kuma tasan bazai fara yi mata yau ba. Don haka sai tayi wani tunani. Kai ta jinjina sannan tace da mai Martaba."let me handle him. Kaje zanzo nai maka bayani." Murmushi yayi yace."Mother nd son's stuff." Sannan ya juya ya bar side din guards suka rufa masa baya.
Bayan fitar mai Martaba ne Ummin Usman ta kallesa tace."gaya min damuwarka, wa ya taba ka ko kuma mene ne baka so ake maka? Auren ne matsalar ka ko mene."
Ji yayi kamar ya gaya mata damuwarsa, amma tunawa da yayi idan yayi haka ma bai cika namiji ba. Don haka sai ya karkata zancen d cewa."ni abubuwa sun min yawa, Abbi yace wai grand wedding za ayi. Gashi ni ba son yarinyar nake ba. Kuma Ummi sai kawai tazo ta raina ni. Indai fa na aure ta raina ni zatai."
Dariya yaso bawa Ummin amma tasan haushi zai sake ji idan tayi masa dariyar dan haka sai ta kanne ta dinga lallashinsa har zuwa sanda ya dan ware. Ya tsahi yayi wanka sanna tasa shi yaci abinci. sai waje. Isha da ta tabbatar ya ware sannan ta bar part din shi kuma lokacin kwanciya yayi domin wani irin bacci yake ji.
Tun rananr bai bari wani damuwar ta ya kara tasiri a ransa ba. Domin shi ko tuna ta ma ya hana zuciyarsa yi bare ya tuna kalamanta da suka fi madaci daci a garshi. Hada hadar biki ake ta yi. Ita ko aunty Suwaida tana ta fama da laulayi. Chiroma ma zai zo auren Usman. Yanzu haka Meeno ta koma part din Suwaida da zama. Ummi ce da kanta ta roki Aunty Bilki akan ta barta ta koma can din kafin Chiroma ya dawo.

Shigowa yayi cikin parlour dinsa a gajiye domin yau ya dawo daga Zabbit, yashawo hanya don haka yana shigowa da sallama ya nemi kujera ya baje. Sanye take da dogowar straight gown mai rubber a jikin ta Yellow tasha adon stones golden. Duk ta kwanta a jikin ta ta lafe rigar tana da tsaga a gefe daga iya gwuiwa har kasa. Tayi Kalba manya a gashinta ta zubo da guda hudu gaba ta side din hagu dauran sun zuba har gadon bayanta. Kafarta sanye cikin Loafers baki.
Tana tafe tana yauki ta sauko daga matattakalar benen da me parlorn. Da ido yake binta cikin kallo na so da kauna da kuma kewarta.
"Sannu da zuwa yayana." Ta furta cikin muryarta mai sanyi.
Yawu ya hadiya sanna ya amsa a kasalance yace."yauwa my Meenal. Na same ku lfia."
"Lafia lau." Ta amsa a takaice sannan ta juya ta nufi fridge dan dauko masa abinda zai sanyaya makoshinsa. Bayan ta kawo ta ajiye kan center  table din dake gabansa ne ya kasa hakuri har sai da ya fizgota ya manna ta da jikinta sannan yace." Bakya kewata ko baby."?
Dariya ya bata. "Ya bzan yi kewarka ba yayana."
"Naga ai kamar baki murnan dawowata ba." Chiroman ya sake fada.
"Kaga bari na kawo maka abincinka kaci sai ka huta kayi wanka sannan sai na nuna maka kalar kewanka da nayi." Meeno ta fada da wata murya mai cike da jan hankali tare da kashe masa ido guda daya.
Karara wayarsa ce ta tashe shi. A gigice ya farka sanna ya dau wayar. 'MY WIFE' ya gani a jikin wayar. Dauka yayi tare da sallama. A maimakon yaji muryar Suwaida Meeno ce take magana.
"Yaya Chiroma yaushe zaka zo ne."? Meeno ta fada cike da dauki.
"Haba Meenal nayi sallama baki amsa ba kuma babu gaisuwa yausbe zaki girma? Bai jira ta yi magana ba yasake cewa bawa Suwaida wayar."
Bayan Suwaida ta karba ne sun gaisa ya tambayeta jiki suja cigaba da hirarsu ta mata da miji. Sunyi kamar minti  20 sina waya kafin suyi sallama. Kafin su katse wayar ne Meeno ta karbi wayar don suyi magana.
Mafarkin da yayi ne ya fado masa da jin muryarta. "Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Ya furta tare da katse wayar.
Wannan wane irin mafarki ne? Haka ya wuni babu sukuni a ranar.
Tun daga ranan kullum ya kwanta sai yayi mafarki da Meeno. Tun abun na damunsa har ya fara zame masa jiki. Har ya zamana indai ya farka daga bacci to sai ya kira Suwaida dan yasan bazasu gama waya baiji muryar Meeno ba. Da haka har ranar dawowar sa Pasweek yayi.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now