second to the last page.

655 52 8
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 60 to 70

*Second to the last page*
_Long page_

Kwanaki suna ta shudewa haka ma satittika na ta wucewa babu wuys kaji ance wata ya kama kuma ya mutu, a irin wannan halin aka tsinci kai da an shekara guda kenan. Yanzu kam Meeno ta gama komawa 'yar gidan jiya, saboda alakarta da sarauniyar Aljanun ta zama kamar jini da hanta. Kusan duk sanda take son ganinta tafi kawai takeyi sai Meeno ta bayya na izuwa gareta. Domin ta sanya mata wani zobe a hannunta da duk sanda take son ganinta bata da shamaki.
Yanzu kam gaba daya ta gama brainwashing Meeno. Duk abinda take so shi takeyi mata.
A yau sarauniyar Aljanun ta kusiri niyyar fara daukar fansar cutar da aka mata shekaru 18 da suka wuce.

Kamar ko da yaushe hannunta ta tafa sai ga Meeno ta bayyana a gabanta.
"Ranki ya dade lafia irin wanann kira haka na gaggawa." Meeeo ta furta tana zama kusa da karagar sarauniyar Aljanun.
Hade rai sarauniyar tayi sannan ta gyara zaman ta ta fara magana.
"Na dade ina gaya miki ina son na dauki fansa akan wasu tsirran mutane bisa ga zalunta ta da sukai yau kimanun shekaru 18 a duniyar ku ta bil adama. Kuma bincike ya nuna ke daya ce zaki iya daukar min wannan fansa. Dalili kuwa shine akwai alaka mai tsananin karfi a tsakani na dake."
Meeno ce ta jinjina kau sanan tace.
"Wacce irin fansa ce da ke kanki sarauniyar Aljanu baza ta iya dauka da kanta ba sai ni, Me ce ce wanann alakar da ke tsakaninmu, kuma jna so nasan su waye wadan nan mutane me kuma suka miki."? 

"Duka inada wadan nan amsoshin, kuma zan baki amma sai kin fara aiwatar min da abinda na saka ki tukun." Sarauniyar ta fada tana kara gyara zamanta.
Muskutawa Meenon ta sake yi sannan ta kafe sarauniyar da ido kana tace.
" Ko baza ki amsa min wasu daga cikin tambayoyin nawa ba yanzu ai dole ki amsa min wasu. Me kike so nyai kuma su wa zanyi wa.?"
"Ba wani ayyuka bane masu wahala. Ina so ne kije Pasweek jibi, ki dan kwana 2 yadda kowa bazai zarge ki ba. Bayan kwana 2 zan neme ki sai ba gaya miki ne zaki min."

Shiru Meeno tayi sannan ta amsa da
"Babu damuwa,  ya zanyi na bar kurkukun da nake.?"
Dariya Sarauniyar tayi sannan tace. "Wannan ba damuwa bane na shirya komu yadda ya dace."
Hannu ta sake tafawa take Meeno ta bace ta koma inda taje bauta.
Bayan kwana 2 ne aka yi wasu mashahuran bakin larabawa anan masarautar da su Meeno suke aiki. Wadan nan bakin ne byana sun huta suka ce da sarkin kasar suna so su kewaya masarutar. Babu musu sarki yasa aka kewaya dasu.

Suna cikin tafiya ne suka iso inda su Meenk suke aiki. A ranar aikin tastsar madara suke daga jikin wasu murguza murguzan shanu.
Daya daga cikin bakin larabawan ne ya tsaya domin kallon wannan shanun.
Waziri da ya rako su ne yake tambaya ko shanun sun burgeshi ne?
"Eh sun burge ni kwarai, kuma da so samu ne ayi min kudin mace da namiji ko nawa ne zan biya."
Murna ce ta kama wazirin take yasa akayi musu kudi ya zabga musu uban kudi ya ninka kudinsu yakai sau 20. Babu musu bakon balarabe ya dauko kudin ya biya sannan ya kara da cewa.
"Ina so a hadani da bayi guda 2 domin su dinga min irin wannan tastar madarar kasan ba lalle bane 'yan kasarmu a sami wacce zata iya wanann tatsar."
Anan waziri ya bashi damar zabar bayin guda 2. Ilai kuwa sai ya nuna Meeno da Zainab.  Aiko sai waziri ya sake zabga masa kudi wai su wadan nan bayin masu tsada ne don haka na daban ne su.  Babu musu wannan balaraben ya biya aka hado su da su Meeno.
Ko da sarkin kasar yaga irin makudan kudin da waziri yazo dasu ya kuma bashi labarin yadda akai shima take murna ta kamashi ya shiga yiwa waziri kyautar zinare domin wanann kudin babu su ko a lalitar kasar.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now