Part 2

1.9K 99 2
                                    

Har yanzu dai ina cikin birnin ina shawagi inda idona yayi arba da wata dattijuwar mace ta fito daga wani matsakaicin gida na masu rufin asiri. Lullube take da lafayya tun daga samanta har kas. Giftani da tayi naji wani daddadan kamshi ya bigi hanci a take na gane wannam mace duk yadda akai babarbariya ce. Sauri sauri gudu gudu haka naga tana tafiya. Da ganin yadda take wannan sauri na tabbatar da akwai abu mai mahimmanci a tattare da ita. Take nima na nade kafar wano na nabi matar nan a guje dan dauko muku rahoto. Saura naji wani yace qamshinta me ya fizge ni na bita😏
  Ban ankara ba naga wannan mata mai azababben qamshi ta fada wani hamshaqin gida. Da ganin gidan na sarauta ne. Masu tsaron kofa suka so su hanani aiki na haka na haura ta katanga, inda nayi sa'a mukai kicibis da ita nai ajiyar zuciya nabi bayanta. Gaban wani babban kofa naga ta tsaya tayi yare ma wani mutum. Mutumin yashiga wannan kofa jim kadan ya fito yazo ya yara mata sai naga tashiga kofar itama take ko na bita dan na bawa ido na abincinsa. Falo ne na alfarma da yasha ado da kayan qawa, gefe guda ga wata hamshaqiyar kujera a bisanta kuwa wanni dattijo ne mai kyan launi yana dauke da fashin goshi da kuma shunkure irin na barebari. Bayan gaisuwa da dan shiru da ya biyo baya, sai naji matar nan ta fara bayani kamar haka
Ranka ya dade daman akan maganar Meeno ce, yau din ma ba gida ta kwana ba. Kuma wallahi ranka ya dade sabon mukulli muka saka muka rufe gidan nan, kuma wallahi bamuyi masa boyom wasa ba. Kuma ko da asuba da muka tashi wallahi ranka ya dade meeno ba ta kofa ta fice ba. Saboda yadda muka rufe gidan da kwado haka muka tadda shi.
Mutumin nan ya nisa sanan yace kun tabbata sanda kuka rufe gida da meeno kuka rufe??
Tace kwarai kuwa ranka ya dade. Yace mata ni ina mamaki?? Ta ina to ta fita?? Kunsan dai tsayin katangar gidajen garin nan mai haureta sai wani ikon na Allah. Bare Meeno yarinya yar shekara 16.
Tace ni duk ba wannan ba yanzu ace hausawa basuyi ba, fulani ma basuyi ba sai a cikinmu??? Yallabai wannan ba qaramin abin kunya bane...
Bata karasa fada ba ya dakatar da ita, wannan karon fuskarsa ba annuri yace kinga Baana, ban gane me kike nufi ba? Me kike nufi Meeno tayi?? To ina so ki sani mummunan zato dai haramun ne, ke da kika haifeta Baana ina ke ina yi mata wannan fatam🙄
Ina so kisa a ranki koma me Meeno takeyi kaddarar ta ce haka kuma bawa bYa tsallake kaddararsa. Kuma fadin da kike fullo basuyi ba hausa basuyi ba bana so,mu anan haka ai duk kanmu a hade yake. Saboda haka ina so ki tashi kije ki tsammaci dawowarta kizo ki sanar min.
Ta amsa da to ta tashi ta tafi.
Wannan kenan.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now