Last page

837 52 1
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

*_The End_* 🔚🔚🔚🔚🔚

Kwance tashi asarar mai rai. Yau kusan kimanin watan Usman 2 kenan yana kwance. Kuma a yau ne ake sa ran zuwan wani gagarumin mai maganj wanda yake bada magungunan ko wacce irin cuta da iznin Allah. Kamar yadda aka tsara komi haka ya tafi dai dai. Bayan isowar me maganin ne yake tambayar abinda ya faru ana aka sheda masa komai. Baiyi kasa a gwuiwa ba ya dauko wata gorar magani ya bada yace a samu mutum mafi soyuwa a gareshi wanda aka san yafi sanshi akan kowa mafi kusa da zuciyar sa abashi ya shafa masa. Sannan kuma kada a bari ruwan maganin nan ya diga a kasa ko yaya ne. Idan aka bi wannan sharadin in sha Allahu kafin minti 30 zai farfado.

Babu tantama sarki Khaleel yasa aka kirawo Fulani Nawwara domin a tunanin mai tunani matar mutum tafi kowa kusa dashi. Bata yi wani tunani ba ta karbi gorar maganin ta matsa kusa dashi domin ta fara shafa masa.
A garin tuttulo maganin ne a hannuna ta ashe da yawa ta tuttulo cikin zafin nama Meeno tasa hannunta kasan hannun Fulanin ta tare wanda yake kokarin zubowa. Ajiyar zuciya kowa ya saki sannan Fulani ta shafa masa kamar yadda mai magani ya umarta. Wanda ya zubo a hannun Meeno kuwa, tuni ta shafe masa shi a kafarsa saboda mai maganin yace kada a zubar da shi..
Minti 30 tayi shuru Usman bai motsa ba. Awa daya shiru awa 2 shiru tun ana sa ran aga ya motsa har aka fidda rai. 
Shi ko mutumin nan mai magani yayi tsalle ya dire yace ba ayi amfani da magani dai dai ba. Domin shi ya yadda da kansa yasan indai yabada magani aka bi yadda ya dace to tabbasa z a samu nasara. Haka kowa ya tashi ya tafi jiki a sanyaye mai maganin yace a bashi nan da awa 2 zai yi nazari yaga ta ina aka samu matsala.
Kowa ya fice daga dakin har da mai maganin. Kasancewar Meeno ce a baya kamar ance ta juyo. Sai taga kafarsa guda tana motsawa. Kuma wannan kafar itace wacce ya shafawa maganin.
Da farko ta dauka idonta Gizo yake mata amma sai ta tabbatar da Yes ba gizo bane motsi kafar take. Da ta juya taga babu kowa kowa ya fice kawai sai ta yanke shawara ba tare da tayi tunanin komi ba.

Dawowa tayi ta sake zubo ruwan maganin a hannunta tabi ko ina na jikin sa ta shafe masa. Sannan ta nemi waje ta zauna. Kafin minti 30 taga ya soma fizge fizge. A guje ta fita daga dakin dan nemo mai maganin.
Tare da mai maganin suka dawo.

Ita ko Fulani tana can abin duniya ya mata yawa. Gaba daya fa ita zaman gidanga ya ishe ta. Ga miji a kwance babu lafia. Gashi Chiroma ne ya zama sarki sabanin yadda Mahaifiyar ta tayi mata alkawari. Gashi sha'awa tayi mata yawa dan ma tana yawan kallon fina finan batsa sanan tana biyawa kanta bukata. Amma duk da haka ji take kamar taci kanta saboda jaraba.
Gaskia ita ta yanke shawarar bazata iya zama a haka ba. Wannan ai masifa ce. Gida kawai zata tafi ba tare da ta yiwa kowa sallama ba. Shawarar data yanke kenan sanan ta zuba kayanta kala 2 a jaka ta dauki car keys.

Ya dade akansa kafin ya samu ya dora masa maganin da ya saka shi bacci. Rusunawa mai maganin yayi sanan ya fara magana.
"Allah ya taimake ki wannan maganin bacci zai saka shi, nan da awa 6 zai farka idan ya farka na tabbatar da iznin Allah garau zai farka sai dan abinda ba a rasa ba. Allah ya bashi lafai."  Da Ameen Meeno ta amsa sannan ta sallami mai maganin. Wayarta ta ciro ta kira Chirom(sarki).
"Hello Yayana, kazo fa ya Usman ya tashi."
A matukar firgice sarkin ya mike tsaye saboda direct fada  ya nufa daga asibitin. Da sauri ya fito daga fadar sanna ya nufi hanyar asibitin masarautar. Babu musu fadawa suka take masa baya.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now