Part 3

1.6K 91 0
                                    

Dawowar Baana gidan bai fi da daqiqa biyar ba kuwa sai ga Meeno tayi sallama. Ta shigo ta nemi wajen abinta tayi zamanta kai baka ce ita aka gama cigiya ba. Mahaifiyar ta kalle ta tace Meeno daga ina?? Ina so ki gaya min ina kikaje?? Ta ina kika bi?? Yaushe kuma kika fita? Idan katangar dake tsakar gidan ta amsa mata to Meeno ta tanka mata. Bata gushe ba tana tambayar ta ita ko bata tambayarta har sai da ta kai ga Baana ta dora hannu a kai ta fasa ihu tana cewa ni Baana  naga takaina. Allah kanaji kana gani ya Allah, a tarbiyyar yarinyar nan ban rage komai ba. Kai ka jarabceni ya Allah ka kawo min dauki.
Meeno najin haka ta tashi ta kalla mahaifiyarta tace Ammi kina bani mamaki wallahi. Yanzu meye akai na kuka haka zaki tara mana jama'a. I just want u to trust me babu abinda nake ba dai dai ba. Hasali ma abinda nake will surely help us nan gaba. How can a mother just can't trust her own child. Gaskia ya kamata ki canja. Tsanin mamaki da bakinciki suka hana Baana magana. Ta tsaya tana wa diyar tata kallon mamaki da razani. Meeno bata gushe ba tana magana tana cewa Eh Ammi.. Kinsan kin bani tarbiyya cikakke, na kuma sami ilmin addini ingatacce, na san abinda kike gujewa shi yasa kike tashin hankalinki dan bana kwana a gida. Ina so ki kwantar da hankali. Duk abinda kike zato bashi bane. Dazu naji kinje kina gayawa Shugaba cewa yauma ban kwana gida ba. Har yake miki nasiha akan kada ki zarge. Banda abin Ammina ai yadda na fita ne zai fara baki mamaki. Baki mamakin yadda ake nake fita batare da bude kyaure ba, ba kuma tare da haure katanga ba?? Daga nan ya dace ki gane cewa ba yawon banza nake tafia ba. Ya kamata kisan akwai babban alamari a tattare dani. Ko da Meeno tazo nan a zance ta sai mahaifiyarta ta jaa ajiyar zuciya tace da ita. Ameenatou ba wai ina zarginki bane. A matsayinki na yar dana haifa kuma ke din mace mai karanci shekaru, dole na shiga zullumi idan hakan na faruwa dake. Tace amma babu komi ko menene wannan babban alamarin Allah ya warware shi. Ta amsa da Amin. Sannan ta wuce dakinta.

Salamu alaikum! Salamu alaikum!!
Wa alaikumusalaam. Maraba da Bilkisu mai gadon zinare. Kece yau a gidan namu?? Wallahi kuwa yau nice cewar Bilkisu mai gadon zinare. Bismillah mu shiga daamga ciki mana. Bayan sun shiga sun zazzauna a matsakaicin parlorn sun gaisa sunyi hirar yaushe gamo ne Mai gado take cewa da Baana ni kuwa ya Ameenatu?? Shekara guda kenan rabona da ita. Ko tana makaranta ne naji banji motsin ta ba. Anan ne Baana take gaya mata ai ta aika Meeno ne makota karbo mata wasu kaya. Mai gado kanwa ce ga margayi mahifin Meeno. Bata ida rufe baki ba kuwa Meeno tayi sallama ta shigo tazo gefen Amminta ta zauna. Ta gaida Mai gado sannan taje gayawa Ammin tata sakon. Daga nan kuma ta tashi ta koma dakinta. Bayan tafiyarta ne Baana ta soma gaya wa Mai gado matsalolin da taje fuskanta da Meeno. Mai gado tayi salati ta hau salallami tana cewa na shiga uku ni Bilkisa, yau mai zan ji na gani hakan😳 yanzu tsakani da Allah Baana kin kyauta kenan?? Yarinya tana cikin wannan halin amma ki gaza sanarwa da dangin mahaifinta?? Yanzu tun yaushe take cikin wannan halin? Baana tayi murmushin takaici tace wata na 4 kenan bata taba yin cikakken kwana 4 ba tana kwana gidan. Kuma ai na sanar da Shugaba(mataimakin sarkin garin kenan mai wakiltar Kanurai) Mai gado tace hana Baana sanarwa da shugaba ai ba shine mafi aala ba. Baana tace kar ki manta shugaban nan fa yaya ne a wajena ba wai wakiltar mu kawai yake ba. Mai gado tace haka ne. Yanzu gaskia zan kira su Baffa musan abinyi. Bazai yiwu ba ace yarmu tana cikin wannan mummunan halin ba mu ja bakunanmu muyi shiru. Bazai yiwu ba. Idan hankalin Baana yayi dubu ya tashi saboda tasan karshen zancen. Tasan karshen abun ace za a raba ta da yarta guda daya tilo. Karshen zancen suce ta gaza tarbiyyarta. Shi yasa tun farkon maganar bata so gaya musu ba. Itakam bata san yadda zatai ba. Mai gado ce ta katse ta daga wannan dogon tunanin da take tace mata ko ba haka ba. Bari ma na kirawo Baffa na tudu na sanar masa. Batai wata wata ba ta cire wayarta ta kira Baffa natudu inda ta sheda masa halin da ake ciki. A nan take yace da Maigado ta kwana anan idan yaso gobe da sasaafe suyo harama su tawo gidansa dan yanzu yamma tayi kuma suna da yar tazara da gidan Baffan dare zaiyi musu kan su karasa. Mai gado ta amsa da to sannan ta katse wayar.
Wannan kenan.


Pasweek palace

Pasweek palace

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


Fadar pasweek babbar fada ce dake can gabas da birnin maleeta, tsakininsu akwai kimanin tafiya ta kilometer 2,347. Gari ne mai cike da mutane kala kala. Mafi akasarin mazauna wannan yanki musulmai ne. Garin Pasweek gari ne mai dauke da miloyoyin mutane masu bambamcin ra'ayi da aqida. Babban abinda jama'ar wannan yanki sukai fice dashi shine kasuwanci da kuma yaqi. Mafiya mazaunan yankin nan mayaqa ne. Mazajensu duk kusan sadaukai ne kuma yan kusuwa. Kamar yadda ilimi ya zama wajibi wa mutanenmu na nan haka horon yaqi ya zama wajibi wa duk wani da ya kwana ya tashi a garin. A wannan gari suna da jajirtacce kuma gagarumin sadaukin sarki. Sarki Rasheed sarki ne sarkin sarakuna mai ji da Mulki, sarauta da kuma uwa uba qarfi. Sadauki duk inda yakai sarki Rasheedu ya take shi. Yana da 'ya' ya guda 4, biyu maza biyu mata. Akwai Ibraheemu wanda aka fi sani da khaleel, yayi aure yana da mata 1 da yara 2 sai Firdausee itama tana aure sai Usman wanda aka fi sani da Namijin zaki 🦁 wanda yake kan ganiyarsa kamar yadda nayi muku bayani a baya. Namijin zaki 🦁 shahar a kyau, sadaukantaka da isa da mulki. Sai kuma yar auta Fatima Zuhra. Ita ma irin halinsu daya da Usman na ji da kai da taka kowa.
Wannan kenan.

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now