part 30

388 112 2
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 29

Zama Fulani tayi anan ta sake yin wani nazari na kamar minti 30 sannan ta tashi tayi kwafa ta shige daya daga cikin bedrooms dinta. Tunda ta shiga ba ita ta fito ba har sai bayan Maghreb.
A bangaren Namijin zaki kuwa shima da ya fice sabgogin gabansa ya tafi haka ita ma Meeno gidansu ta koma ta tarar da Kamwar mahaifinta Aunty Bilki tana tsintar wake. Kujera taja sannan itama ta zauna ta saka hannunta cikin farantin waken tana taya ta.
Sunayi Aunty Bilki tana sako musu hira jifa jifa, hankalin Meeeno gaba daya ba wajen yaje ba saboda haka da ummmm da uhmm uhmmm take bata amsa. Itama Auntynta ta ta lura da haka sai kuwa da bude baki tace."wai mene ne yae dumunki ne Ameena? Gaba daya kin chanja kwana 2, kisani ke din fa amana ce a hannuna." Meeeno ce ta dan kalle ta sannan tace."babu komi."
Kwafa Aunty Bilkin tayi a ranta. Amma a fili sai ta tausasa murya sannan tace."Haba Ameena, ina a matsayin kanwar mahaifinki idan baki gayan matsalar kibba wa zaki gayawa?? Duk nan wa kike dashi da ya dara ni? Ki daure ki gayan. Ko kuma kinga bari ma ba sai kin gayan ba amma dan Allah ki dena dumawa."
Ganin yadda ta damu ne yasa Meeno ta dan saki ranta. Murmushi tayi sannan tace."To in sha Allahu Aunty."
"Yauwa Meenon Baba." Aunty Bilki ta fada tana shafa kan Meenon.
"nifa Meenal sunana Aunty." Meeno ta fada tana hade rai. Haba Aunty Bilki ta kama sannan tace."iyeeee! To Naji Meenal." Dariya duk suka fashe dashi. Meeno ce tayi musu abincin sannan suka zuba suka ci. Ranan a nan ta kwana.
Washe gari kuwa babu inda ta fita taje. Tayi alkawarin dena shiga harkar masu mulkin nan saboda ita bazata juri wulakanci. Har Aunty Suwaida ma ta dena zuwa gidan ta.
Ilai kuwa sai Auntyn ta take tambayar ta."wai ni Meenal bazaki fito kije ko ina ba ne."?
"Aunty ni fa na dena zuwa ko ina fa. Su masu mulkin nan 'yan wulakanci ne fa." Ta fada tana gatsine fuska.
"To ai ko baki isa ba, ko wajen aikin ki ai kya je, ko kin manta Gimbiya ta dauke ki aiki a wajen Fulani Zahra." Aunty Bilki ta fada tana zama a kusa da kafar Meenon.
"Ni fa gaskia ba aiki ta dauke ni ba, kawai jininmu ne ya hadu da Yaa Zahra, kuma ai naga ko ficika bata taba bani na aikatau ba." Cewar Meeno.
Karaf Auntyn tata ta amshw da."Yooo da zaki ce ko sisi bata taba baki ba ai naga watan baiyi ba ka? Kuma bari ma kiji ta aiko min da kudade masu yawan gaske."
Kafin ta rufe bakinta taji Salamae wata baiwa. Bayan sun amsa ne baiwar ta sheda musu Aunty Suwaida ce ta aiko. Caraf Meeno tace." Je kice mata bana jin dadi ne."
Kafin ta karasa fadin me zata ce aunty Bilki ta katse ta da cewa." ai taji dadin jikin ma, je kice mata gata nan zuwa."
Bayan tafiyar baiwar da kyar ta samu ta lallabe ta ta tashi ta tafi.
Taje gidan yaya Chiroman acan ta samu Zahra taje neman ta. Bayan sun gaggaisa ne Aunty Suwaida ta tambayeta wai lafia bata zo ba kuma yau ma ba dan ta aika ba bazata zo ba kenan?
Tabe fuska tayi sannan tace."wallahi Aunty banyi niyyar shiga cikin ku ba kuma har abada na yake hukunci. Ni bazan juri wulakanci ba ne."
Murmushi Suwaida tayi sannan tace."daman nasan za a rina ai. Domin na san halin Fulani Nawwara  ke ma kuma nasan hali. Allah dai ya kade fitina Ameen."
Ita de Zahra bata ce komi ba haka suka dan taba hira sanann Zahra ta sake tambayar Meenal."Wai mi Meenal ya tafiyarmu Zabbit ne."?
Murna ce ta kama Meeno sanann tace."Yaa Zahra ni fa na tambayi Aunty kuma ta barni ke kawai nake jira."
Itama Zahra murna ce ta kamata sanann tace."Aiko bari Yaya Chiroma ya dawo sai muji yaushe zai koma in yasa sai ku bishi ko? Kinsan na kusa komawa Makaranta."
Da haka suka ci gaba da hirar har akai Maghreb. Sallama Meeno tayi musu akan zata je gidan su anan zata kwana. Zahra ta so hanata amma bata son ta takura ta haka ta bar ta taje.

To ita ko Fulani yau ma wani tuggun ta kullawa Zaki, haka ta sake samun dama suka sake Gaurayuwa a filin daga soyayya. Kwarai kuwa yau taji dadin da bata taba ji ba a rayuwarta. Bayan sun gama ne kuma sai ta fashe da kuka.
Shi a tunaninsa shagwaba ce amma yadda ta ci gaba da kukan kamar Allah ya aiko ta ne yasa shi dan tashi zaune. Lallashinta ya fara yi kafin ya tambayeta mene damuwarta?
Narkewa ta sake yi a jikinsa sannan tayi kasa da murya cikin sexy voice tace." yaya Usman bansan me nayi maka ba ka tsaneni." Mutumin da yake cikin giyar Zumar da Fulani ta lasa masa sai ya kada baki yace." Ba wai na tsaneki bane Nawwara. Ta ya zan tsane ki bayan tari. So da kaunar da kike min."
(Kunji fa Zaki kamar bai tsane tan ba)
Sake marairaicewa tayi sannan tace"Tunda Allah yasa na fara ganinka naji duk duniya kayi min, naji ina kaunar ka fiye da komi a rayuwata, zuciyaa ta tayi nisa a sonka, ni banga laifin zuciyar da ko yaushe muradinta bai wuce kasancewa da abin kaunarta ba." Ta karashe zancen da matsanancin kuka.
Kwarai yaji tausayin ta. Dan haka yayi kasa da murya ya hau lallashin abarsa tare da shafa sumar kanta.
"Yanzu me kike so nayi miki kisan ba wai na tsane ki bane Fulani."? Usman ya fada cikin wata irin murya domin yanzu salon ya fara chanjawa.
"So nake kawai ka yarda muyi rayuwa irin ta Ma'aurata, ka barnj na shayar da kai ruwan soyayyar da nake maka mara misaltuwa. Ka barni na gija daular soyayyata a cikin ranka, bance lallai sai ka so ni ba amma dan Allah kada ka tsaneni. Idan baka tsaneni ba nayi maka alkawarin shigar da kai duniyar da baka taba shiga iribta ba ta soyayya." Ta karashe zancen da rada masa a kunne tare da dan kama fatar kunnan ta dan ciza a hankalii.
"Aaaarrrrrhhhh" ya dan saki kara tare da cewa."Nayi miki alkawari Fulani, zamu zauna muyi rayuwa irinta mata da miji, amma ki sani ni raini ne ban so a rayuwa, muddin kikai tunanin raina ni zan tsane ki fiye da komi."
Murna ce ta cika zuciyar Nawwara. Kamar ta tashi ta taka rawar murna haka take ji. Kankameshi tayi ta lalubo lips dinshi tare da fara tsotsa kamar ta samu lollipop. Haka su ka ci gaba da harkoku har zuwa sanda daddaden bacci yayi gaba dasu.

*A cigaba da voting a wattpad..*
*'Yan whatsapp kuma a cigaba da comment. Abinda yasa ma bayi typing ba kwana biyu naga babu wasu zafafan Comments ne.*

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now