part 16

352 40 0
                                    

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
    *NAMIJIN ZAKI*
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

   By
_Nafisa Aliyu_
    *(mrs Naseer)*

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
'''🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
______________________________________

Page 16

*_Assalamu alaikum wa Rahmatullah! Da fatan yan uwa duk mun tashi lfia. Ina sonnayi using wannan dama domin na mika sakon godiya ga masoya masu bin wannan littafi musamman a wattpad, Allah ya bar kauna ya kuma ci gaba da bani damar da zan ci gaba da sibirbido muku wannan labari. Ina so kuma nayi tuni dan Allah a cigaba da voting da comment. Yan whatsapp ma ina godiya sai dai su basa comments. Za kuma ku iya bi na a wattpad @mrs_naseer nagode._*

To yau ma kamar kullum Meeno ta tashi tayi sallar asuba, tana zaune tana azhkar dinta, domin yanzu bata wasa da shi tunda Aunty Suwaida ta koya mata, bayan ta idar ne kuma ta tashi domin taya Auntyn ta Mai gado yan aikacen aikacen gida. Bayan sun gama ne sun karya da shayi da bread da kosai ne Meeno take cewa da mai gado."Aunty Bilki zanje gidan Aunty Suwaida, tace naje zanyi mata tsifa." Washe hakora mai Gado tayi sannan tace, saura yau ma ta baki wani abu ki ki karba wallahi Ameena na kusa na fara hanaki zuwa ko ina a cikin masarautar nan muddin za a dinga yi miki alheri kina kin karba. Ai ance ma shedan shi ke mai da alheri." Murmushi Meenon tayi sannan tace."banda abu irin na Aunty bilki, ki bari ke idan aka miki alherin sai ki amsa, amman wannan tunda ni Meenal aka yiwa to bazan amsa ba. Domin Ammi na ta sha gaya min _ka guji abin hannun mutane sai mutane su so ka._ dan haka ni kinga tafiya ta."
Ta wuce ta tafi ta barta tana ta babatu.
Bayan zuwan ta bangaren Chiroma ne ta tarar da Aunty Suwaida ba lfia, tana ta faman amai ga wani mugun zazzabi da yake son rufe ta. Da gudu ta fito ta nufi shashen Ummi ta gaya mata. Bayan an kirawo likita yazo ya duba ta ne ya tabbarar da Suwaidan tana da juna 2 na tsawon wata 2. Zo kuga murna a wajen mai Martaba domin shi uban gayyar ba ya nan ya Koma Zabbit domin cigaba da project din da ya fara. Ita ma Suwaidan tayi murna haka ma Meeno, domin ji take tamkar Suwaidan 'yar uwarta ce, saboda yadda ita na Suwaidan ta rike ta tamkar 'yar uwa. Mafi akasarin lokaci ita Ummi ma mamakin yadda Suwaida ta saku jiku da Meeno take, saboda Suwaida ma 'yar sarki ce jikar sarki, wani lokacin tana da Izza, amma gashi ta sake da karamar yarinya haka.
To da yamma ne bayan Meeno ta gama yiwa Suwaida gyaran daku ta zauna take mata tausa saboda jikin nata duk babu dadi. Magana Meeno ta fara kamar haka."Ranki ya dade nace ni kuwa kin sanar da mai girma Chiroma."?
Dariya Suwaidan tayi tace."oh ni Suwaida, Meenal har ta fi ni dokin wannan ciki, to ban sanar masa ba, saboda kinsan Chiroma karamin aikin sa ne ya baro paskweek yace zai zo, kuma kinsan bai gama abinda yake ba. Amma tunda nan da sati 2 zai zo, idan yazo ai yaji labari." Hade rai Meeno tayi tace."A gaskia aunty wannan ba dai dai bane. Ya kamata ki gaya masa."  Dariya Suwaidan ta sake yi tace."aiko sai dai ke ki gaya masa domin ni kunya nake ji." suasake saka dariya duk su biyun. Basuyi minti 20 da gama maganar ba kuwa sai ga Chiroma ya kira waya. Aiko Meeno tayi caraf ta daga wayar ta kara a kunne ta fara magana."Ranka ya dade albishirinka.!"?
"Goro fari tass Meenal." Chiroman ya amsa.
Ita ko babu abinda ya dameta ta kada baki tace."dama My princess ce bata da lafia "
Shiru yayi domin shi abin ya bashi mamaki. Ya za tace masa albishir da rashin lafiyar matarsa. Bai gama tunanin ba ta katse shi."shine nazo na same ta tana ta amai, naje na gayawa Ummi, aka kira Dr shine fa yace Auntyn ciki ne da ita na 2months.." 
Bai san ma wace irin murna zai yi ba. Yayi murna yayi godiyar Allah sannan ya kada baki yace."Meenal fada min duk abinda kike so tukwuicin wannan albishir da kika min mai dadi sauraro."
Dariya tayi mai sauti sanna tace."yallabai ba yau zan tambaye ka ba."
Shi ma dariya yayi da shirmen nata yace."to ni kuma na miku alkawarin dmyi miki ko mene duk sanda kika tambaya."
"Promise."? Ta sake tambayarsa.
Yace mata."Yea i promise u Meenal. Kuma zan tabbatar miki da Chiroma baya saba alkawari." Dariya tayi sannan ta hada shi da matarsa ta basu waje domin su samu damar soyewa.
To matafiya fa sun dauko hanya don har sun kusa isa Pasweek. Kuma a wannan karon ran maza a bace yake, amma baka isa ka gane ba saboda yanayin sa na kullum kusan hakan yake. To sun dawo misalin karfe 9 na dare, kuma kamar ko yaushe kafafu sun fara daukewa  a cikin masarautar. Namijin zaki direct part dinsa ya nufa domin ya huta gajiya. Sai muce Allah ya tashe mu lfia.

Pheener(mrs_naseer)

08060154424

Namijin Zaki 🦁 Where stories live. Discover now